Bincika › Jigogi › Faɗa da gardama
Rayuwar yau da kullum
Faɗa da gardama a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (32), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Misalai
- Makiyayan Abram da na Lot sun yi faɗa, sai su biyu suka rabuFar 13:7–9
Ayoyin
Far 13:7–9Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne. Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne. Ba ga dukan ƙasar tana gabanka ba? Bari mu rabu. In ka yi hagu sai ni in yi dama. In ka yi dama, sai ni in yi hagu.”
- Ibrahim ya kai ƙarar rijiyar da bayin Abimelek suka ƙwaceFar 21:25
Ayoyin
Far 21:25Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace.
- Musa ya iske Ibraniyawa biyu suna faɗaFit 2:13, Ayy M 7:26
Ayoyin
Fit 2:13Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?”
Ayy M 7:26Kashegari, Musa ya sadu da Isra’ilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku ’yan’uwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’
- Musa ba ya iya ɗaukar dukan gardamar mutane shi kaɗaiM Sh 1:12
Ayoyin
M Sh 1:12Amma yaya zan ɗauka dukan damuwoyinku da nawayarku da kuma faɗace-faɗacenku duka ni kaɗai?
- Efraim sun yi wa Yefta barazana; “Shibbolet” a mashigan UrdunMah 12:1–6
Ayoyin
Mah 12:1–6Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.” Yefta ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya sosai da Ammonawa, ko da yake na kira ku, amma ba ku cece ni daga hannuwansu ba. Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?” Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.” Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,” sai su ce, “To, ka ce, ‘Shibbolet.’ ” In ya ce, “Sibbolet,” saboda ba sa iya faɗin kalmar daidai, sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Aka kashe mutanen Efraim dubu arba’in da biyu a ta haka.
- Labarin matar Tekowa: ’ya’ya maza biyu sun yi faɗa a gona2Sam 14:6
Ayoyin
2Sam 14:6Baiwarka tana da ’ya’ya maza biyu. Suka yi faɗa da juna a fili, kuma ba wanda yake can don yă raba su. Ɗayan ya bugi ɗayan, ya kashe shi.
- Almajirai suna gardama a kan wane ne mafi girma a cikinsuMar 9:33–34, Luk 22:24
Ayoyin
Mar 9:33–34Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?” Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?
Luk 22:24Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.
- Gardama mai zafi a Antiyok game da kaciyaAyy M 15:1–2
Ayoyin
Ayy M 15:1–2Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.” Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.
- Bulus da Barnabas sun rabu saboda MarkusAyy M 15:37–39
Ayoyin
Ayy M 15:37–39Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su, amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba. Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus,
- Farisiyawa da Sadukiyawa sun yi gardama game da tashin matattuAyy M 23:7–10
Ayoyin
Ayy M 23:7–10Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu. (Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.) Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?” Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja.
- Bulus ya tsayayya wa Kefas fuska da fuska a AntiyokGal 2:11
Ayoyin
Gal 2:11Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake.
- Korintiyawa: “Ni ina bin Bulus,” “Ni ina bin Afollos”1Kor 1:11–12
Ayoyin
1Kor 1:11–12’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku. Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”
- Masu bi suna kai juna ƙara a kotu1Kor 6:6–7
Ayoyin
1Kor 6:6–7Me zai sa ɗan’uwa yă kai ƙarar ɗan’uwa, a gaban marasa bi? Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku?
- Bulus ya roƙi Yuwodiya da Sintike su yi zaman lafiya da junaFil 4:2
Ayoyin
Fil 4:2Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.
A cikin Doka
- Wanda aka ji wa rauni a faɗa akan biya shi saboda aikin da ya rasa da warkarsaFit 21:18–19
Ayoyin
Fit 21:18–19“Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya, idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda ne, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓata masa, yă kuma lura da shi, har yă warke sarai.
- Akan kai gardama tsakanin mutane kotu a yanke hukunciM Sh 25:1
Ayoyin
M Sh 25:1Idan mūsu ya tashi tsakanin mutum biyu har abin ya kai su kotu, alƙalai kuwa suka yanke hukunci a kan batun, suka kuɓutar da marar laifi sa’an nan suka hukunta mai laifi,
Maganganu a Karin Magana
- Ƙiyayya takan tā da husuma; ƙauna takan rufe laifuffukaK Mag 10:12
Ayoyin
K Mag 10:12Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.
- Mai saurin fushi yakan tā da faɗaK Mag 15:18, K Mag 29:22
Ayoyin
K Mag 15:18Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.
K Mag 29:22Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa, mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa.
- Gara ɗan busasshen abinci cikin salama da biki tare da faɗaK Mag 17:1
Ayoyin
K Mag 17:1Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.
- Fara faɗa kamar sakin ruwan rigyawa neK Mag 17:14
Ayoyin
K Mag 17:14Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.
- Abin girma ne a kawo ƙarshen gardama; kowane wawa zai yi faɗaK Mag 20:3
Ayoyin
K Mag 20:3Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.
- Ka kori mai ba’a, faɗa kuwa zai ƙareK Mag 22:10
Ayoyin
K Mag 22:10Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare.
- Tsoma baki a faɗan wani kamar kama kare a kunnuwa neK Mag 26:17
Ayoyin
K Mag 26:17Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.
- Mace mai faɗa kamar ɗigar ruwa ce ba fasawa a ranar ruwan samaK Mag 27:15, K Mag 25:24
Ayoyin
K Mag 27:15Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;
K Mag 25:24Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
A wasu wurare
- Ka yi sulhu da abokin gābanka da sauri tun kuna kan hanyar zuwa kotuMat 5:25
Ayoyin
Mat 5:25“Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.
- In da hali, ku zauna lafiya da kowaRom 12:18
Ayoyin
Rom 12:18Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.
- Muhawarar wauta takan haifar da faɗa2Tim 2:23–24
Ayoyin
2Tim 2:23–24Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma.
- “Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku?”Yaƙ 4:1
Ayoyin
Yaƙ 4:1Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne?
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.