Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Bukukuwa da liyafa

Rayuwar yau da kullum

Bukukuwa da liyafa a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (44), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Al’adu

  • An zaunar da ’yan’uwan Yusuf bisa ga shekarunsu, daga ɗan fari zuwa ƙaramiFar 43:33
    Ayoyin
    Far 43:33Aka zaunar da ’yan’uwan Yusuf a gabansa bisa ga shekarunsu, daga ɗan fari zuwa auta. ’Yan’uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki.
  • Rabon Benyamin ya ninka na sauran sau biyarFar 43:34
    Ayoyin
    Far 43:34Daga teburin da yake a gaban Yusuf aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Benyamin ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.
  • Sama’ila ya zaunar da Shawulu a wurin girma cikin baƙi talatin1Sam 9:22–24
    Ayoyin
    1Sam 9:22–24Sa’an nan Sama’ila ya shiga da Shawulu da baransa ya zaunar da su a gaban waɗanda aka gayyata, mutanen sun kai wajen mutum talatin. Sama’ila ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman da na ba ka, wannan da na ce ka ajiye dabam.” Sai mai dahuwan ya ɗauko cinya da abin da yake bisanta ya kawo ya ajiye a gaban Shawulu. Sama’ila ya ce, “Ga abin da aka ajiye dominka. Ka ci, gama an keɓe shi dominka saboda wannan hidima daga lokacin da na ce, ‘Na gayyaci baƙi.’ ” Shawulu kuwa ya ci tare da Sama’ila a ranan nan.
  • Kada ka zauna a wurin girma a bikin aureLuk 14:8–10
    Ayoyin
    Luk 14:8–10“In wani ya gayyace ka bikin aure, kada ka zaɓi wurin zama mai bangirma, don wataƙila akwai wani da ya fi ka girma, da aka gayyata. In kuwa haka ne, wanda ya gayyace duk biyunku, zai zo ya ce maka, ‘Ka ba wa mutumin nan wurin zamanka.’ Ka ga, an ƙasƙantar da kai, kuma dole ka ɗauki wuri mafi ƙasƙanci. Amma in an gayyace ka, ɗauki wuri mafi ƙasƙanci, don in wanda ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Ka hawo nan aboki a wuri mafi girma.’ Wannan zai ɗaukaka ka a gaban dukan ’yan’uwanka baƙi.
  • Baƙi sukan kishingiɗa a kan dogayen kujeruAmos 6:4, Yoh 13:23–25
    Ayoyin
    Amos 6:4Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa kuna mimmiƙe a kan kujerunku. Kuna cin naman ƙibabbun raguna da na ƙosassun ’yan maruƙa.
    Yoh 13:23–25Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi. Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?” Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?”
  • Masu cin abinci sukan tsoma hannu a kwano gudaMat 26:23
    Ayoyin
    Mat 26:23Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.
  • Shugaban biki yakan ɗanɗana ruwan inabiYoh 2:8–10
    Ayoyin
    Yoh 2:8–10Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.” Suka yi haka. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”
  • Molo da garaya, ganguna da sarewa, da ruwan inabi a bukukuwaIsh 5:12, Amos 6:5
    Ayoyin
    Ish 5:12Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
    Amos 6:5Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.
  • Kiɗa da rawa a bikin ɗan da ya dawoLuk 15:23–25
    Ayoyin
    Luk 15:23–25Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali. Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali. “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa.
  • Samson ya yi kacici-kacici a bikin aurensa na kwana bakwaiMah 14:10–12
    Ayoyin
    Mah 14:10–12To, mahaifinsa ya gangara don yă ga yarinyar. Samson kuwa ya shirya wata liyafa a can, yadda yake bisa ga al’adar angwaye. Sa’ad da ya bayyana, sai aka haɗa shi abokai talatin. Sai Samson ya ce, “Bari in yi muku kacici-kacici, in kun ba ni amsa cikin kwana bakwai na wannan biki, zan ba ku riguna lilin talatin da kuma tufafi talatin.
  • Sarauniya Bashti ta yi wa mata liyafa ta dabamEsta 1:9
    Ayoyin
    Esta 1:9Sarauniya Bashti ita ma ta yi liyafa saboda mata a fadar Sarki Zerzes.
  • Akan shirya abinci don jin daɗiM Had 10:19
    Ayoyin
    M Had 10:19Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma kuɗi ne amsar kome.
  • Baƙin da aka gayyata suna kawo hanzari (misali)Luk 14:16–20
    Ayoyin
    Luk 14:16–20Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa. Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’ “Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’ “Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’ “Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’
  • Ku aika da rabo ga waɗanda ba su shirya kome baNeh 8:10–12
    Ayoyin
    Neh 8:10–12Nehemiya ya ce, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku.” Lawiyawa suka rarrashi mutane duka suna cewa, “Ku natsu, gama wannan rana ce mai tsarki. Kada ku yi baƙin ciki.” Sa’an nan dukan mutane suka koma gidajensu suka ci, suka sha, suka aika wa wanda ba shi da abinci, gama yanzu sun fahimci kalmomin da aka karanta musu.
  • ’Ya’yan Ayuba maza sukan yi biki bi da bi suna gayyatar ’yan’uwansu mataAyu 1:4–5
    Ayoyin
    Ayu 1:4–5’Ya’yansa maza sukan yi biki a gidajensu, wannan yă yi yă ba wancan, sai su kira ’yan’uwansu mata ukun su ci, su sha tare. Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.

Lokatai

  • Fir’auna ya yi biki a ranar haihuwarsaFar 40:20
    Ayoyin
    Far 40:20To, a rana ta uku ne, ranar tunawa da haihuwar Fir’auna, ya kuwa yi biki wa dukan hafsoshinsa. Ya fid da shugaban masu shayarwa da kuma shugaban masu tuya a gaban hafsoshinsa.
  • Liyafar ranar haihuwar Hiridus domin manyan mutanen GaliliMar 6:21
    Ayoyin
    Mar 6:21A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili.
  • Babban bikin Ibrahim a ranar da aka yaye IshakuFar 21:8
    Ayoyin
    Far 21:8Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki.
  • Ishaku da Abimelek sun tabbatar da alkawari da bikiFar 26:28–30
    Ayoyin
    Far 26:28–30Suka amsa, “Mun ga a zahiri cewa Ubangiji yana tare da kai; saboda haka muka ce, ‘Dole rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai.’ Bari mu yi yarjejjeniya da kai cewa ba za ka cuce mu ba, kamar yadda ba mu fitine ka ba, amma muka yi maka kirki, muka kuma sallame ka cikin salama. Yanzu kuwa kai albarkatacce ne na Ubangiji.” Sai Ishaku ya shirya musu liyafa, suka ci suka kuma sha.
  • Yaƙub da danginsa sun ci abinci a kan dutseFar 31:54
    Ayoyin
    Far 31:54Ya miƙa hadaya a can a ƙasar tudu, ya kuma gayyaci danginsa zuwa wurin cin abinci. Bayan suka ci, sai suka kwana a can.
  • Dawuda ya yi wa Abner da mutane ashirin biki2Sam 3:20
    Ayoyin
    2Sam 3:20Sa’ad da Abner wanda yake tare da mutane ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda ya shirya masa liyafa tare da mutanensa.
  • Bikin Adoniya domin waɗanda yake sa rai za su naɗa shi sarki1Sar 1:25
    Ayoyin
    1Sar 1:25Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’
  • Kwana uku na ci da sha a Hebron don naɗa Dawuda sarki1Tar 12:38–40
    Ayoyin
    1Tar 12:38–40Dukan waɗannan mayaƙa ne waɗanda suka ba da kansu da yardar rai su yi hidima. Suka zo Hebron da cikakken niyya don su naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila. Duka sauran Isra’ilawa su ma suka goyi baya a naɗa Dawuda sarki. Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi. Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.
  • Solomon ya yi wa dukan bayinsa biki bayan mafarkinsa1Sar 3:15
    Ayoyin
    1Sar 3:15Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne. Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki.
  • Zerzes ya nuna dukiyarsa kwana 180, sa’an nan ya yi biki kwana bakwaiEsta 1:3–8
    Ayoyin
    Esta 1:3–8A shekara ta uku ta mulkinsa, ya yi wa dukan hakimansa da ma’aikatansa liyafa. Shugabannin mayaƙan Farisa, da Mediya, da yerimai; da kuma hakimai na lardunan suka kasance. Kwanaki 180 cif, ya nuna yawan dukiyar masarautarsa, da ɗaukakarta da kuma darajar girmansa. Sa’ad da waɗannan kwanaki suka wuce, sai sarki ya yi liyafa a cikin lambun da aka shinge na fadar sarki wadda ta ɗauki kwana bakwai wa dukan mutane daga ƙarami har zuwa babba, waɗanda suke zama a masarautar Shusha. Lambun yana da fararen labulen da aka rataye da shunayya na lallausan lilin, da aka ɗaura da igiyoyin fararen lilin, da yadin jan garura, haɗe da zoban azurfa a kan ginshiƙin farin ƙasa. A nan, akwai kujeru na zinariya da na azurfa a kan daɓe mai ado da aka yi da duwatsu masu daraja, da farin ƙasa, da fararen duwatsun wuya, da waɗansu duwatsu masu tsada. Aka rarraba ruwan inabi cikin kwaf na zinariya, kowanne kuwa dabam yake da ɗayan. Ruwan inabin kuwa yana da yawa, bisa ga wadatar sarki. Bisa ga umarnin sarki, aka bar kowane baƙo yă sha yadda ya ga dama, gama sarki ya umarci dukan bayin da suke rarraba ruwan inabin su ba wa kowa abin da yake so.
  • A liyafar Esta: “Yanzu, mece ce bukatarki?”Esta 5:6
    Ayoyin
    Esta 5:6Yayinda suke shan ruwan inabi, sarki ya sāke ce wa Esta, “Yanzu, mece ce bukatarki? Za a biya miki shi. Kuma mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”
  • Biki saboda dokar sarki da kuma a kwanakin FurimEsta 8:17, Esta 9:17–19
    Ayoyin
    Esta 8:17A kowane lardi da kowace birni, ko’ina da dokar sarki ta kai, aka yi farin ciki a cikin Yahudawa, cike da bukukkuwa. Yawan mutane da waɗansu ƙasashe suka zama Yahudawa, don tsoron Yahudawa ya kama su.
    Esta 9:17–19Wannan ya faru a ran goma sha uku na watan Adar. A rana ta goma sha huɗu kuwa suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da kuma ta farin ciki. Amma Yahudawan da suke a Shusha suka taru a rana ta goma sha uku da ta sha huɗu, sa’an nan a rana ta goma sha biyar suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da ta farin ciki. Shi ya sa Yahudawan ƙauyuka, waɗanda suke zama a karkara, suke kiyaye rana ta goma sha huɗu ta watan Adar a matsayin ranar farin ciki da ta biki, ranar ba da kyautai ga juna.
  • Babban bikin Belshazar domin manyan mutanensaDan 5:1–3
    Ayoyin
    Dan 5:1–3Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su. Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su.
  • Bikin Nabal irin na sarki1Sam 25:36
    Ayoyin
    1Sam 25:36Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye.
  • Mutane sun zauna su ci su sha a gaban ɗan maraƙinFit 32:6
    Ayoyin
    Fit 32:6Saboda haka kashegari, mutane suka tashi da sassafe suka miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Bayan haka suka zauna suka ci, suka sha, suka kuma tashi suka yi rawa.

A teburin abinci

  • A bikin Sabon Wata wurin Dawuda ba kowa1Sam 20:5, 1Sam 20:24–25
    Ayoyin
    1Sam 20:5Dawuda ya ce, “Gobe fa shi ne Bikin Sabon Wata, ya kamata in ci tare da sarki amma bari in tafi fili in ɓuya har jibi da yamma.
    1Sam 20:24–25Dawuda ya tafi ya ɓuya a fili. Sa’ad da ranar Bikin Sabon Wata ta zo, sarki ya zauna don yă ci. Ya zauna a kujeransa inda ya saba zama kusa da bango yana fuskantar Yonatan, Abner kuma ya zauna kusa da sarki. Amma kujeran Dawuda ba kowa.
  • Mefiboshet da ’ya’yan Barzillai maza suna ci a teburin sarki2Sam 9:10, 1Sar 2:7
    Ayoyin
    2Sam 9:10Kai da ’ya’yanka maza da bayinka za ku riƙa yin masa noma, ku kuma kawo hatsin, don jikan maigidanka yă sami abinci. Mefiboshet kuma, jikan maigidanka, zai riƙa ci a teburina.” (Ziba kuwa yana da ’ya’ya maza goma sha biyar da kuma bayi ashirin.)
    1Sar 2:7“Amma ka yi alheri ga ’ya’yan Barzillai mutumin Gileyad, ka sa su kasance a cikin waɗanda suke ci a teburinka. Sun goyi bayana sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka Absalom.
  • Annabawa 850 suna ci a teburin Yezebel1Sar 18:19
    Ayoyin
    1Sar 18:19Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.”
  • Lot ya shirya biki ya toya burodi marar yistiFar 19:3
    Ayoyin
    Far 19:3Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka tafi tare da shi, suka kuma shiga gidansa. Ya shirya musu abinci, ya gasa burodi marasa yisti, suka ci.
  • Lawi ya yi wa Yesu babbar liyafaLuk 5:29
    Ayoyin
    Luk 5:29Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su.
  • Farisiyawa sun gayyaci Yesu ya ci abinci tare da suLuk 7:36, Luk 14:1
    Ayoyin
    Luk 7:36To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur.
    Luk 14:1Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau.
  • An zuba turare a kan Yesu a wani liyafa a BetaniMar 14:3, Yoh 12:2–3
    Ayoyin
    Mar 14:3Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.
    Yoh 12:2–3A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi. Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.