Bincika › Jigogi › Ciniki da ’yan kasuwa
Rayuwar yau da kullum
Ciniki da ’yan kasuwa a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (37), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Ibrahim ya auna azurfa “bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi”Far 23:16
Ayoyin
Far 23:16Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin.
- Ayarin mutanen Ishmayel suna ɗauke da kayan yaji, man shafawa da mur zuwa MasarFar 37:25
Ayoyin
Far 37:25Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.
- An sayar da Yusuf ga ’yan kasuwa a shekel ashirin na azurfaFar 37:28, Far 37:36
Ayoyin
Far 37:28Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.
Far 37:36Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna.
- Hiram ya aika da al’ul da fir; Solomon ya biya da alkama da man zaitun1Sar 5:8–11, 2Tar 2:15
Ayoyin
1Sar 5:8–11Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir. Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.” A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata. Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara.
2Tar 2:15“Yanzu fa, bari ranka yă daɗe, yă aiko wa bayinsa alkama da sha’ir da kuma man zaitun da ruwan inabin da ka alkawarta,
- Jiragen ruwan Solomon sun kawo talenti 420 na zinariya daga Ofir1Sar 9:26–28
Ayoyin
1Sar 9:26–28Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku. Hiram kuwa ya aiki mutanensa, masu tuƙan jirgin ruwa waɗanda suka san teku, don su yi hidima a jerin jiragen ruwa tare da mutanen Solomon. Suka tafi Ofir suka kuma dawo da talenti 420 na zinariya, wanda suka ba wa Sarki Solomon.
- Solomon yakan karɓi kuɗin shiga daga ’yan kasuwa da masu ciniki1Sar 10:15, 2Tar 9:14
Ayoyin
1Sar 10:15Ban da haraji daga ’yan kasuwa, da fatake, da kuma daga dukan sarakunan Arabiya, da gwamnonin ƙasar.
2Tar 9:14ban da harajin da fatakai da ’yan kasuwa suke biya. Haka kuma dukan sarakunan Arabiya da gwamnonin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa wa Solomon.
- Na’omi ta sayar da ƙasar da take ta ElimelekRut 4:3
Ayoyin
Rut 4:3Sa’an nan ya ce wa dangin nan mai fansa, “Na’omi, wadda ta dawo daga Mowab, tana so ta sayar da filin da yake na ɗan’uwanmu Elimelek.
- Maƙeran zinariya da ’yan kasuwa sun gyara wani sashe na katangar UrushalimaNeh 3:32
Ayoyin
Neh 3:32Maƙeran zinariya da ’yan kasuwa suka gyara wani sashi tsakanin ɗakin da yake bisa kusurwa da Ƙofar Tumaki.
- Mutanen Taya sukan sayar da kifi a Urushalima a ranar AsabbaciNeh 13:16
Ayoyin
Neh 13:16Mutane daga Taya waɗanda suke zama a Urushalima suna shigar da kifi da kaya iri-iri na ’yan kasuwa suna kuma sayar da su a Urushalima a ranar Asabbaci wa mutanen Yahuda.
- Nehemiya ya rufe ƙofofi; ’yan kasuwa sun kwana a bayan birniNeh 13:19–20
Ayoyin
Neh 13:19–20Sa’ad da inuwar yamma ya fāɗo a ƙofofin Urushalima kafin Asabbaci, na umarta a rufe ƙofofi kuma kada a buɗe sai Asabbaci ya wuce. Na kafa waɗansu mutanena a ƙofofin don kada a shigo da wani kaya a ranar Asabbaci. Sau ɗaya ko biyu, ’yan kasuwa da masu sayar da kowane irin kaya suka kwana waje da Urushalima.
- Mace mai ƙwazo takan sayi gona ta kuma sayar da tufafin lilinK Mag 31:16, K Mag 31:24
Ayoyin
K Mag 31:16Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
K Mag 31:24Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.
- Jirgin ruwan Bulus ya sauke kayansa a TayaAyy M 21:2–3
Ayoyin
Ayy M 21:2–3Sai muka sami wani jirgin ruwa da zai ƙetare zuwa Funisiya, sai muka shiga muka kama tafiya. Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya. Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa.
- Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura daga TiyatiraAyy M 16:14
Ayoyin
Ayy M 16:14Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus.
- Masu canjin kuɗi da masu sayar da kurciyoyi a filin haikaliYoh 2:14
Ayoyin
Yoh 2:14A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi.
- Wani ɗan kasuwa ya sayar da dukan abin da yake da shi saboda lu’u-lu’u guda mai daraja (misali)Mat 13:45–46
Ayoyin
Mat 13:45–46“Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau. Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.
- An ba bayi kuɗi don su yi ciniki da shi (misali)Luk 19:13, Mat 25:16
- “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni … mu yi kasuwanci”Yaƙ 4:13
Ayoyin
Yaƙ 4:13Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.”
Ciniki da Taya (Ezekiyel 27)
- Tarshish: azurfa, ƙarfe, kuza da dalmaEzk 27:12
Ayoyin
Ezk 27:12“ ‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma.
- Yaban, Tubal da Meshek: bayi da kayan tagullaEzk 27:13
Ayoyin
Ezk 27:13“ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.
- Bet Togarma: dawakai, dawakan yaƙi da alfadaraiEzk 27:14
Ayoyin
Ezk 27:14“ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai.
- Dedan: barguna na sirdi; bakin teku: hauren giwa da katakon kanyaEzk 27:15, Ezk 27:20
- Aram: zumurrudu, shunayya, kayan ado, lilin mai taushi, murjani da yakutuEzk 27:16
Ayoyin
Ezk 27:16“ ‘Mutanen Aram sun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.
- Yahuda da Isra’ila: alkama, zuma, mai da man shafawaEzk 27:17
Ayoyin
Ezk 27:17“ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.
- Damaskus: ruwan inabin Helbon da uluEzk 27:18
Ayoyin
Ezk 27:18“ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar.
- Arabiya da Kedar: ’yan raguna, raguna da awakiEzk 27:21
Ayoyin
Ezk 27:21“ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki.
- Sheba da Ra’ama: kayan yaji, duwatsu masu daraja da zinariyaEzk 27:22
Ayoyin
Ezk 27:22“ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.
A cikin Doka
- Ma’aunai, nauyaye da mudu na gaskiyaFir 19:35–36, M Sh 25:13–15
Ayoyin
Fir 19:35–36“ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
M Sh 25:13–15Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
- Kada mai saye da mai sayarwa su cuci junaFir 25:14
Ayoyin
Fir 25:14“ ‘In ka sayar da gona wa wani daga mutanen ƙasarka, ko ka saya wata gona daga gare shi, kada ku cuci juna.
Maganganu
- “Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” in ji mai saya, sa’an nan ya yi taƙama sa’ad da ya tafiK Mag 20:14
Ayoyin
K Mag 20:14“Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki.
- ’Yan kasuwa da suke jira Asabbaci ta wuce don su sayar da hatsiAmos 8:5
Ayoyin
Amos 8:5Kuna cewa, “Yaushe Sabon Wata zai wuce don mu sayar da hatsi, Asabbaci ta wuce, don mu sayar da alkama?” Mu yi awo da ma’aunin zalunci mu ƙara kuɗin kaya mu kuma cutar da mai saya,
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.