Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Abota

Rayuwar yau da kullum

Abota a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (45), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe; an haifi ɗan’uwa domin lokacin wahalaK Mag 17:17
    Ayoyin
    K Mag 17:17Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
  • Akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwaK Mag 18:24
    Ayoyin
    K Mag 18:24Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
  • Raunukan da aboki ya yi maka na aminci neK Mag 27:6
    Ayoyin
    K Mag 27:6Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
  • Gara maƙwabci na kusa da ɗan’uwa mai nisaK Mag 27:10
    Ayoyin
    K Mag 27:10Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
  • Kamar yadda ƙarfe yake wasa ƙarfe, haka mutum yake wasa waniK Mag 27:17
    Ayoyin
    K Mag 27:17Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.
  • Kada ka cika zuwa gidan maƙwabcinka, don kada ya gaji da kaiK Mag 25:17
    Ayoyin
    K Mag 25:17Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka yawan ganinka zai sa ya ƙi ka.
  • Albarka da babbar murya da sassafe ana ɗaukarta kamar la’anaK Mag 27:14
    Ayoyin
    K Mag 27:14In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe, za a ɗauka shi a matsayin la’ana.
  • Kada ka yi abota da mai saurin fushiK Mag 22:24–25
    Ayoyin
    K Mag 22:24–25Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi, in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.
  • Arziki yakan jawo abokai da yawa; matalauci kuwa akan rabu da shiK Mag 19:4, K Mag 19:6
    Ayoyin
    K Mag 19:4Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi.
    K Mag 19:6Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.
  • Maimaita laifi yakan raba abokaiK Mag 17:9
    Ayoyin
    K Mag 17:9Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
  • Biyu sun fi ɗaya; igiya mai kashi uku ba ta saurin tsinkewaM Had 4:9–12
    Ayoyin
    M Had 4:9–12Biyu sun fi ɗaya, gama suna samun riba mai kyau na aikinsu. In ɗaya ya fāɗi, abokinsa zai taimake shi yă tashi. Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi! In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna. Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai? Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya, mutum biyu za su iya kāre kansu. Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.
  • Aboki na kusa da suka ci abinci tare ya juya wa mai zabura bayaZab 41:9, Zab 55:12–14
    Ayoyin
    Zab 41:9Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.
    Zab 55:12–14Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi. Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa, wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah.
  • Ayuba yana kuka cewa abokansa sun juya masa bayaAyu 6:14–15, Ayu 16:20, Ayu 19:19
    Ayoyin
    Ayu 6:14–15“Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki. Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani,
    Ayu 16:20Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne yayinda nake kuka ga Allah;
    Ayu 19:19Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.
  • A kāriyar Bulus ta farko, kowa ya bar shi2Tim 4:16
    Ayoyin
    2Tim 4:16A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.
  • Yesu: babu ƙaunar da ta fi mutum ya ba da ransa saboda abokansaYoh 15:13–15
    Ayoyin
    Yoh 15:13–15Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana.

Misalai

  • Abram ya ceci ɗan’uwansa Lot da horarrun mutane 318Far 14:14–16
    Ayoyin
    Far 14:14–16Da Abram ya ji cewa an kama danginsa, sai ya tara horarrun mutane 318, da aka haifa a gidansa, ya bi sawun sarakunan da suka tafi da Lot, har Dan. Da dad dare, Abram ya rarraba mutanensa don su fāɗa wa sarakunan nan, ya ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewa da Damaskus. Ya washe su da kuma dukan kayayyakinsu, ya kuma dawo da Lot danginsa da mallakarsa, tare da mata da sauran mutane.
  • Rut ba za ta bar Na’omi ba: “Inda za ki, zan tafi”Rut 1:16–17
    Ayoyin
    Rut 1:16–17Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.”
  • Sama’ila ya yi baƙin ciki saboda Shawulu1Sam 15:35, 1Sam 16:1
    Ayoyin
    1Sam 15:35Daga wannan rana Sama’ila bai ƙara saduwa da sarki Shawulu ba, har rasuwar Sama’ila, amma ya yi baƙin ciki sosai a kan Shawulu. Ubangiji kuwa ya damu da ya sa Shawulu ya zama Sarkin Isra’ila ba.
    1Sam 16:1Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Har yaushe za ka yi ta makoki saboda Shawulu? Na riga na ƙi shi da zaman sarkin Isra’ila. Ka cika ƙahonka da mai, zan aike ka zuwa wurin Yesse na Betlehem. Na zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza yă zama sarki.”
  • Yonatan yana ƙaunar Dawuda kamar kansa, ya kuma ba shi rigarsa1Sam 18:1–4
    Ayoyin
    1Sam 18:1–4Bayan da Dawuda ya gama magana da Shawulu, sai Yonatan ɗan Shawulu ya ji zuciyarsa tana son Dawuda sosai. Yonatan kuwa yana ƙaunar Dawuda kamar ransa. Tun daga wannan rana Shawulu ya zaunar da Dawuda tare da shi, bai bar shi ya koma gidan mahaifinsa ba. Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa. Yonatan ya tuɓe doguwar taguwarsa da ya sa, ya ba wa Dawuda, tare da sulkensa, har ma da māshi da kibiyarsa, da kuma bel nasa.
  • Dawuda da Yonatan sun yi wa juna sumba, suka yi kuka, suka rabu da rantsuwa1Sam 20:41–42, 1Sam 23:16–18
    Ayoyin
    1Sam 20:41–42Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsu, ya rusuna har sau uku. Sa’an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, Dawuda kuwa ya yi kuka sosai. Yonatan ya ce wa Dawuda, “Sauka lafiya, mun riga mun yi rantsuwar abokantaka da juna a cikin sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji ne shaida tsakanina da kai, tsakanin zuriyarka da zuriyata har abada.’ ” Sai Dawuda ya tafi, Yonatan kuwa ya koma gari.
    1Sam 23:16–18Yonatan ɗan Shawulu kuwa ya tafi wurin Dawuda a Horesh, ya ƙarfafa shi yă dogara ga Allah. Ya ce, “Kada ka ji tsoro, mahaifina Shawulu ba zai taɓa sa hannu a kanka ba. Za ka zama sarki a Isra’ila, ni kuma in zama na biyu gare ka. Kai, ko mahaifina Shawulu ma ya san da haka.” Su biyunsu kuwa suka ɗaura yarjejjeniya a gaban Ubangiji. Sai Yonatan ya koma gida amma Dawuda ya zauna Horesh.
  • Makokin Dawuda: “Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce”2Sam 1:26
    Ayoyin
    2Sam 1:26Na yi baƙin ciki saboda kai, Yonatan ɗan’uwana; ƙaunatacce kake a gare ni. Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce, abar al’ajabi fiye da ta mace.
  • Saboda Yonatan, Mefiboshet yakan ci abinci a teburin Dawuda kullum2Sam 9:1, 2Sam 9:7
    Ayoyin
    2Sam 9:1Wata rana Dawuda ya yi tambaya ya ce, “Akwai wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu wanda zan nuna masa alheri saboda Yonatan?”
    2Sam 9:7Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.”
  • Dawuda ga firist Abiyatar: “Ka zauna tare da ni … Ka zauna lafiya tare da ni”1Sam 22:23
    Ayoyin
    1Sam 22:23Ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro mutumin da yake neman ranka, yana nema raina ma. Ka zauna lafiya tare da ni.”
  • Hiram sarkin Taya ya daɗe yana abokin Dawuda1Sar 5:1
    Ayoyin
    1Sar 5:1Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa.
  • Hushai abokin Dawuda ya kasance da aminci a lokacin tawayen Absalom2Sam 15:32–37, 2Sam 16:16–17
    Ayoyin
    2Sam 15:32–37Da Dawuda ya isa ƙwanƙoli, inda mutane sun saba yi wa Allah sujada, Hushai, mutumin Arkitawa kuwa yana can don yă tarye shi, taguwarsa a yage, ga kuma ƙura a kansa. Sai Dawuda ya ce masa, “In ka tafi tare da ni, za ka zama mini kaya. Amma in ka koma birni, ka gaya wa Absalom, ‘Zan zama bawanka, ya sarki; dā ni bawan mahaifinka ne, amma yanzu zan zama bawanka,’ ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel. Ba Zadok da Abiyatar firistocin nan suna nan tare da kai ba? Ka gaya musu duk abin da ka ji a fadan sarki. ’Ya’yansu biyu maza, Ahimawaz ɗan Zadok, da kuma Yonatan ɗan Abiyatar, suna can tare da su. Ka aike su wurina da duk abin da ka ji.” Saboda haka Hushai abokin Dawuda ya isa Urushalima yayinda Absalom yake shigowa birnin.
    2Sam 16:16–17Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!” Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake nuna wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”
  • Ittai mutumin Gat ya ƙi ya bar Dawuda da yake gudu2Sam 15:19–21
    Ayoyin
    2Sam 15:19–21Sarki ya ce wa Ittai mutumin Gat, “Don me za ka zo tare da mu? Ka koma ka zauna tare da Sarki Absalom. Kai baƙo ne, ɗan gudun hijira daga garinka. Jiya-jiya ka zo. Yau kuma in sa ka yi ta yawo tare da mu, ga shi ban ma san inda za ni ba? Koma, ka tafi da ’yan’uwanka. Bari alheri da amincin Ubangiji su kasance tare da kai.” Amma Ittai ya ce wa sarki, “Muddin Ubangiji yana a raye kuma muddin ranka yă daɗe yana a raye, duk inda ranka yă daɗe sarki zai kasance, ko a yi rai ko a mutu, a can bawanka zai kasance.”
  • Sarki Ahaziya ya ziyarci Sarki Yoram da aka yi wa rauni2Sar 8:28–29
    Ayoyin
    2Sar 8:28–29Ahaziya ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab don su yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Arameyawa suka yi wa Yoram rauni; saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni.
  • Abokan Ayuba uku sun zauna tare da shi kwana bakwai shiruAyu 2:11–13
    Ayoyin
    Ayu 2:11–13Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi. Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu, sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.
  • Daniyel ya roƙi sarki ya ɗaukaka abokansa ukuDan 2:17–18, Dan 2:49
    Ayoyin
    Dan 2:17–18Sa’an nan Daniyel ya komo gida ya kuma sanar wa abokansa Hananiya, Mishayel da Azariya, batun nan duka. Ya roƙe su su roƙi jinƙan Allah na sama domin wannan mafarki, saboda kada a kashe shi da abokansa tare da sauran masu hikima na Babilon.
    Dan 2:49Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki.
  • Yesu yana ƙaunar Marta, ’yar’uwarta da LazarusLuk 10:38–39, Yoh 11:5, Yoh 11:11
    Ayoyin
    Luk 10:38–39Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa.
    Yoh 11:5Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus.
    Yoh 11:11Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
  • Ɗan ’yar’uwar Bulus ya gargaɗe shi game da maƙarƙashiyaAyy M 23:16
    Ayoyin
    Ayy M 23:16Amma da ɗan ’yar’uwar Bulus ya ji wannan makirci, sai ya tafi cikin barikin soja ya gaya wa Bulus.
  • Firiskila da Akwila sun sa rayukansu cikin haɗari saboda BulusRom 16:3–4
    Ayoyin
    Rom 16:3–4Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu. Sun yi kasai da ransu saboda ni. Ba ni kaɗai nake musu godiya ba amma har ma da dukan ikkilisiyoyin Al’ummai.
  • Bulus game da Timoti: “Ba ni da wani kamar sa”Fil 2:19–22
    Ayoyin
    Fil 2:19–22Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku. Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku. Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.
  • Afaforiditus, ɗan’uwan Bulus, abokin aikinsa da abokin famarsaFil 2:25
    Ayoyin
    Fil 2:25Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.