Rayuwar yau da kullum
Fitilu a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (28), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
A cikin tabanakul da haikali
- Wurin ajiye fitila na ƙerarriyar zinariya, rassa shida da kwafuna kamar furannin almondFit 25:31–36
Ayoyin
Fit 25:31–36“Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi. Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen. Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan. A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni. Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka. Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya.
- Fitilu bakwai, da lagwanin zinariya da farantaiFit 25:37–38, Fit 37:23
Ayoyin
Fit 25:37–38“Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta. Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya.
Fit 37:23Da zinariya zalla suka yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa.
- An yi shi da talenti guda na zinariya zallaFit 25:39, Fit 37:24
- Man zaitun tsantsa da aka matse yakan sa fitilu su ciFit 27:20, Fir 24:2
- Haruna yakan lura da fitilu tun daga yamma har safeFit 27:21, Fir 24:3–4
Ayoyin
Fit 27:21A cikin Tentin Sujada, a waje da labulen da yake a gaban Akwatin Alkawari, Haruna da ’ya’yansa za su sa fitilu su yi ta ci a gaban Ubangiji, daga yamma har safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a cikin Isra’ila har tsararraki masu zuwa.
Fir 24:3–4Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa. Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji.
- Akan ƙone turare sa’ad da ake lura da fitilu, safe da magaribaFit 30:7–8
Ayoyin
Fit 30:7–8“Haruna zai ƙone turare a bisa bagaden kowace safiya, sa’ad da yake shirya fitilu. Dole Haruna yă ƙone turare sa’ad da ya ƙuna fitilu da yamma, ta haka za a riƙa ƙona turare a gaban Ubangiji, daga tsara zuwa tsara.
- An kafa fitilun don su haskaka wurin da yake gaban wurin ajiye fitilaƘid 8:2–3
Ayoyin
Ƙid 8:2–3“Yi magana da Haruna, ka ce masa, ‘Sa’ad da za ka shisshirya fitilun nan bakwai, ka shirya su yadda za su fuskanci gaba domin haskensu yă haskaka ta gaba.’ ” Haka kuwa Haruna ya yi; ya shisshirya fitilun yadda za su fuskanci gaba a kan wurin ajiye fitilan, kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
- Wurin ajiye fitila yana fuskantar tebur, a gefen kuduFit 40:24–25
Ayoyin
Fit 40:24–25Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
- A lokacin tafiya akan rufe shi da zane mai ruwan shuɗiƘid 4:9
Ayoyin
Ƙid 4:9“Za su ɗauki zane mai ruwan shuɗi su rufe wurin ajiye fitilan da yake don fitilu, tare da fitilunsa, lagwaninsa da farantansa, da dukan tulunansa don man amfaninsu.
- Sama’ila ya kwanta kafin fitilar Allah ta mutu1Sam 3:3
Ayoyin
1Sam 3:3Fitilar Allah kuwa tana ci, ba tă mutu ba tukuna, Sama’ila kuma na kwance a haikali na Ubangiji inda akwai akwatin Allah.
- Solomon ya yi wuraren ajiye fitila goma na zinariya, biyar a kowane gefe1Sar 7:49, 2Tar 4:7
Ayoyin
1Sar 7:49ya yi alkukai na zinariya zalla (Biyar a dama, biyar kuma a hagu, a gaban wuri mai tsarki na can cikin); ya yi zāne-zānen furannin zinariya da fitilu da kuma arautaki;
2Tar 4:7Ya yi wurin ajiye fitila goma na zinariya bisa ga tsari dominsu ya kuma sa su a haikali, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa.
- Akan kunna fitilun wurin ajiye fitila na zinariya kowace yamma2Tar 13:11
Ayoyin
2Tar 13:11Kowace safiya da kowace yamma sukan miƙa hadayun ƙonawa da turare mai ƙanshi ga Ubangiji. Sukan shirya burodi a tsarkaken tebur mai tsabta, sukan kuma ƙuna fitilu a alkukai kowace yamma. Muna kiyaye ƙa’idodin Ubangiji Allahnmu. Amma ku kun yashe shi.
- Hezekiya: kakanninmu sun rufe shirayin haikali suka kashe fitilu2Tar 29:6–7
Ayoyin
2Tar 29:6–7Kakanninku ba su yi aminci ba; suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnmu, suka kuma yashe shi. Suka juya fuskokinsu daga mazaunin Ubangiji suka kuma juya masa baya. Suka kulle ƙofofin shirayi, suka kuma kashe fitilu. Ba su ƙone turare ko su miƙa hadayun ƙonawa a wuri mai tsarki ga Allah na Isra’ila ba.
- Babiloniyawa sun kwashe wuraren ajiye fitilaIrm 52:19
Ayoyin
Irm 52:19Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.
A gida
- Mutane sukan sa fitila a kan wurin ajiye fitila, ba a ƙarƙashin kwando ko gado baMat 5:15, Mar 4:21, Luk 8:16, Luk 11:33
Ayoyin
Mat 5:15Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.
Mar 4:21Sai ya ce musu, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da murfi ko kuma ku sa ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan sa ta a kan wurin ajiye fitila ba?
Luk 8:16“Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske.
Luk 11:33“Babu wanda yakan ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta, ko ya rufe ta da murfi ba. A maimako, yakan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, don masu shiga su ga haske.
- Wata mace ta kunna fitila ta share gida saboda kuɗin da ya ɓaceLuk 15:8
Ayoyin
Luk 15:8“Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba?
- Fitilar mace mai ƙwazo ba ta mutuwa da dareK Mag 31:18
Ayoyin
K Mag 31:18Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
- Rubutu ya bayyana a bangon fāda kusa da wurin ajiye fitilaDan 5:5
Ayoyin
Dan 5:5Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu.
- Fitilu da yawa a ɗakin bene a ToruwasAyy M 20:8
Ayoyin
Ayy M 20:8Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru.
- ’Yan mata goma da fitilu; biyar ba su kawo ƙarin mai ba (misali)Mat 25:1–8
Ayoyin
Mat 25:1–8“A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba. Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu. Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su. “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’ “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu. Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.