Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Ragwanci

Rayuwar yau da kullum

Ragwanci a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (26), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Maganganu a Karin Magana

  • Ka tafi wurin kyashi, kai rago: yakan tara abinci da raniK Mag 6:6–8
    Ayoyin
    K Mag 6:6–8Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima! Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki, duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
  • Ɗan barci, sai talauci ya zo kamar ɗan fashiK Mag 6:9–11
    Ayoyin
    K Mag 6:9–11Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku? Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi.
  • Gonar rago: ƙaya, sarƙaƙiya da katangar dutse da ta rusheK Mag 24:30–34
    Ayoyin
    K Mag 24:30–34Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci; ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe. Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.
  • Hannuwa marasa aiki sukan talauta mutumK Mag 10:4
    Ayoyin
    K Mag 10:4Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.
  • Wanda yake barci lokacin girbi ɗa ne mai kunyatarwaK Mag 10:5
    Ayoyin
    K Mag 10:5Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.
  • Kamar ruwan tsami ga haƙora, hayaƙi kuma ga idanuK Mag 10:26
    Ayoyin
    K Mag 10:26Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.
  • Ragwanci yakan ƙare a aikin ganduK Mag 12:24
    Ayoyin
    K Mag 12:24Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
  • Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farautaK Mag 12:27
    Ayoyin
    K Mag 12:27Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci.
  • Rago yana marmari amma ba shi da komeK Mag 13:4, K Mag 21:25
    Ayoyin
    K Mag 13:4Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.
    K Mag 21:25Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.
  • Hanyar rago kamar shingen ƙaya ceK Mag 15:19
    Ayoyin
    K Mag 15:19An tare hanyar rago da ƙayayyuwa, amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce.
  • Mai ragwanci a aikinsa ɗan’uwan mai hallakarwa neK Mag 18:9
    Ayoyin
    K Mag 18:9Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
  • Yakan sa hannunsa a kwano amma ba ya iya kai shi bakinsaK Mag 19:24, K Mag 26:15
    Ayoyin
    K Mag 19:24Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa!
    K Mag 26:15Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.
  • Ba ya noma a lokaci, sai ya rasa kome lokacin girbiK Mag 20:4
    Ayoyin
    K Mag 20:4Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
  • “Akwai zaki a waje!”K Mag 22:13, K Mag 26:13
    Ayoyin
    K Mag 22:13Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”
    K Mag 26:13Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”
  • Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago a gadonsaK Mag 26:14
    Ayoyin
    K Mag 26:14Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago yake jujjuya a gadonsa.
  • Ya fi mutane bakwai masu amsa da hikima hikima a ganinsaK Mag 26:16
    Ayoyin
    K Mag 26:16Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.

A wasu wurare

  • Saboda ragwanci tsaiko yakan lotsa, ɗaki kuma yakan yi yoyoM Had 10:18
    Ayoyin
    M Had 10:18In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa, in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.
  • Wawa yakan naɗe hannuwansaM Had 4:5
    Ayoyin
    M Had 4:5Wawa yakan kame hannuwansa yă kuma lalatar da kansa.
  • Bawan da ya binne talentinsa an kira shi mai ƙyuyaMat 25:26
    Ayoyin
    Mat 25:26“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba?
  • Kada ƙwazonku ya raguRom 12:11
    Ayoyin
    Rom 12:11Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji.
  • “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci”2Tes 3:10–12
    Ayoyin
    2Tes 3:10–12Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.” Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.
  • Gwauraye ’yan mata sukan koyi zaman banza, suna yawo gida-gida1Tim 5:13
    Ayoyin
    1Tim 5:13Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.
  • Kada ku zama masu sanyin jikiIbr 6:12
    Ayoyin
    Ibr 6:12Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.