Rayuwar yau da kullum
Tsufa a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (42), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Maganganu
- Ka tashi a gaban tsofaffi; ka girmama masu furfuraFir 19:32
Ayoyin
Fir 19:32“ ‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.
- Ana samun hikima a wurin tsofaffiAyu 12:12
Ayoyin
Ayu 12:12Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba? Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?
- Furfura rawani ne mai darajaK Mag 16:31, K Mag 20:29
Ayoyin
K Mag 16:31Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.
K Mag 20:29Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu, furfura ita ce darajar tsofaffi.
- Jikoki su ne rawanin tsofaffiK Mag 17:6
Ayoyin
K Mag 17:6Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
- Shekaru saba’in, ko tamanin in muna da ƙarfiZab 90:10
Ayoyin
Zab 90:10Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare.
- “Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa”Zab 71:9, Zab 71:18
- Sa’ad da suka tsufa za su ci gaba da ba da ’ya’yaZab 92:14
Ayoyin
Zab 92:14Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,
- “Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa”Zab 37:25
Ayoyin
Zab 37:25Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.
- “Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi”Ish 46:4
Ayoyin
Ish 46:4Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku. Na yi ku zan kuma riƙe ku; zan lura da ku in kuma kuɓutar da ku.
- An kwatanta tsufa: kwanakin da ba za ka ji daɗinsu baM Had 12:1–5
Ayoyin
M Had 12:1–5Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin lokacin wahala ta zo shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu,” kafin rana da haske wata da taurari su daina haske, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa; sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki, majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi, sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa, idanun da suke duba ta taga suka duhunta; sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga tituna ƙarar niƙa kuma ya tsagaita; sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane, ba a kuwa jin waƙoƙinsu, sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu da kuma hatsarori a tituna; sa’ad da itacen almon ya toho, fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar, sha’awace-sha’awace sun kafe. Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa ya bar masu makoki suna ta yi.
- Tsofaffi maza da mata za su zauna a titunan Urushalima, da sanda a hannuZak 8:4
Ayoyin
Zak 8:4Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Tsofaffi maza da mata za su sāke zauna a titunan Urushalima, kowanne da sanda a hannu saboda tsufa.
- Sa’ad da ka tsufa, wani zai sa maka tufafiYoh 21:18
Ayoyin
Yoh 21:18Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”
- Tsofaffi maza da tsofaffi mata a cikin ikkilisiyaTit 2:2–3
Ayoyin
Tit 2:2–3Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri. Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari.
Misalai
- An yi wa Ibrahim alkawarin tsufa mai kyau, ya kuma mutu tsoho da gamsuwaFar 15:15, Far 25:8
- Saratu tsohuwa ta yi dariya da alkawarin ɗaFar 18:11–12, Far 21:7
Ayoyin
Far 18:11–12Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa. Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, “Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?”
Far 21:7Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”
- Ishaku, tsoho kuma idanunsa sun kusa makancewa, ya kira IsuwaFar 27:1–2
Ayoyin
Far 27:1–2Sa’ad da Ishaku ya tsufa idanunsa suka raunana har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa ya ce masa, “Ɗana.” Isuwa kuwa ya amsa, ya ce “Ga ni.” Ishaku ya ce, “Yanzu na tsufa kuma ban san ranar mutuwata ba.
- Yaƙub a gaban Fir’auna (shekara 130): “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne”Far 47:9
Ayoyin
Far 47:9Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.”
- Yaƙub tsoho ba ya iya ganin ’ya’yan Yusuf sosaiFar 48:10
Ayoyin
Far 48:10Yanzu fa idanun Isra’ila sun fara rasa ƙarfi saboda tsufa, har ba ya iya gani sosai. Saboda haka Yusuf ya kawo ’ya’yansa maza kusa da shi, sai mahaifinsa ya sumbace su ya rungume su.
- Musa yana da shekara 120: idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa bai ragu baM Sh 34:7
Ayoyin
M Sh 34:7Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba.
- Kaleb yana da shekara tamanin da biyar: “Ina nan da ƙarfina”Yosh 14:10–11
Ayoyin
Yosh 14:10–11“Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar! Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā.
- Yoshuwa tsoho ya kira dukan Isra’ilaYosh 13:1, Yosh 23:1–2
Ayoyin
Yosh 13:1Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba.
Yosh 23:1–2An daɗe bayan da Ubangiji ya ba Isra’ilawa hutu daga dukan abokan gāban da suke kewaye da su. Yoshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa, sai ya aika a kira Isra’ilawa duka, dattawansu, shugabanninsu, alƙalansu, da manyan ma’aikatansu, ya ce musu, “Na tsufa, shekaruna kuwa sun yi yawa,
- Eli, mai shekara tasa’in da takwas kuma mai nauyi, ya fāɗi daga kujerarsa1Sam 4:15, 1Sam 4:18
Ayoyin
1Sam 4:15wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani.
1Sam 4:18Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.
- Sama’ila ya tsufa ya naɗa ’ya’yansa maza alƙalai1Sam 8:1, 1Sam 8:5
- Barzillai, mai shekara tamanin, ya ƙi zuwa fāda tare da Dawuda2Sam 19:32–37
Ayoyin
2Sam 19:32–37To, Barzillai fa tsoho ne, mai shekara tamanin. Ya tanada wa sarki a lokaci da yake Mahanayim, gama shi attajiri ne. Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka ƙetaro tare da ni ka zauna tare da ni a Urushalima, zan kuwa tanada maka.” Amma Barzillai ya ce wa sarki, “Shekara nawa ya rage mini har da zan tafi Urushalima da sarki? Yanzu ina da shekara tamanin. Zan iya bambanta abu mai daɗi da marar daɗi kuma ne? Bawanka zai iya jin ɗanɗano abin da yake ci, ko yake sha ne? Har yanzu zan iya jin muryoyin mawaƙan maza da mata? Don me bawanka zai zama ƙari kaya ga ranka yă daɗe? Bawanka zai ƙetare Urdun tare da sarki, yă ɗan yi maka rakiya kaɗan. Me ya sa ranka yă daɗe zai ba ni irin wannan lada. Ka bar bawanka yă koma, don in mutu a garina, kusa da kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ga bawanka Kimham. Bari yă ƙetare tare da ranka yă daɗe, sarki. Ka yi abin da ka ga dama da shi.”
- Sarki Dawuda tsoho ba ya jin ɗumi ko da bargo1Sar 1:1–4
Ayoyin
1Sar 1:1–4Sa’ad da Sarki Dawuda ya tsufa ya kuma ƙara shekaru, ba ya iya jin ɗumi ko an rufe shi da abin rufuwa. Saboda haka bayinsa suka ce masa, “Bari mu nemi wata budurwa wadda za tă yi wa ranka yă daɗe, sarki hidima, tă kuma kula da shi. Za tă dinga kwanta kusa da ranka yă daɗe, yă ji ɗumi.” Suka nemi kyakkyawar yarinya cikin fāɗin Isra’ila, sai suka sami Abishag, mutuniyar Shunam, suka kawo ta wa sarki. Yarinyar kuwa kyakkyawa ce ƙwarai; ta kuwa lura da sarki, ta kuma yi masa hidima, amma sarki bai yi jima’i da ita ba.
- Rehobowam ya ƙi shawarar dattawa1Sar 12:6–8
Ayoyin
1Sar 12:6–8Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawa waɗanda suka yi wa mahaifinsa Solomon, hidima a kwanakinsa. Ya ce, “Wace shawara ce za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?” Suka amsa, “In a yau za ka zama bawan waɗannan mutane, ka kuma yi musu hidima, ka ba su amsa mai kyau, kullum za su kasance bayinka.” Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawarar matasa waɗanda suka yi girma tare, waɗanda kuma suke masa hidima.
- Annabi Ahiya, idanunsa sun dushe saboda tsufa1Sar 14:4
Ayoyin
1Sar 14:4Saboda haka matar Yerobowam ta yi abin da ya faɗa, ta kuma tafi gidan Ahiya a Shilo. Yanzu dai Ahiya ba ya gani; idanunsa sun tafi saboda tsufa.
- Yehohiyada ya mutu yana da shekara 130, tsoho cike da shekaru2Tar 24:15
Ayoyin
2Tar 24:15Yanzu Yehohiyada ya tsufa kuma cike da shekaru, ya kuwa mutu yana da shekara ɗari da talatin.
- Elihu ya jira kafin ya yi magana domin sauran sun girme shiAyu 32:6–7
Ayoyin
Ayu 32:6–7Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma kun girme ni; shi ya sa na ji tsoro na kāsa gaya muku abin da na sani. Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana; ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’
- Ayuba ya rayu ya ga tsara huɗuAyu 42:16–17
Ayoyin
Ayu 42:16–17Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu. Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.
- Jikan Na’omi zai tallafa mata a tsufantaRut 4:15
Ayoyin
Rut 4:15Zai sabunta rayuwarki yă adana ki a tsufanki. Gama surukarki wadda take ƙaunarki wadda kuma take mafi kyau gare ki fiye da ’ya’ya maza bakwai, ta haife shi.”
- Zakariya da Elizabet, dukansu sun tsufa ƙwaraiLuk 1:7, Luk 1:18
- Anna, gwauruwa mai shekara tamanin da huɗuLuk 2:36–37
Ayoyin
Luk 2:36–37Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure, ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.
- Bulus: “ni Bulus tsoho”Flm 1:9
Ayoyin
Flm 1:9duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.