Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Rawa

Rayuwar yau da kullum

Rawa a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (21), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Miriyam da mata sun yi rawa da ganguna bayan ƙetare tekuFit 15:20
    Ayoyin
    Fit 15:20Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.
  • Musa ya ga ɗan maraƙin da rawarFit 32:19
    Ayoyin
    Fit 32:19Da Musa ya kusato sansanin, sai ya ga ɗan maraƙin da kuma mutane suna rawa. Sai fushinsa ya yi ƙuna, ya kuwa jefar da allunan da suke hannuwansa, allunan kuwa suka farfashe a gindin dutsen.
  • ’Yar Yefta ta fito ta tarye shi tana rawaMah 11:34
    Ayoyin
    Mah 11:34Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya.
  • ’Yan matan Shilo suna rawa a bikin shekara-shekaraMah 21:19–21
    Ayoyin
    Mah 21:19–21Sai suka tuna, akwai bikin Ubangiji da sukan yi shekara-shekara a Shilo ya yi kusa. Shilo yana arewancin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.” Saboda haka suka cewa mutanen Benyamin, “Ku je ku ɓuya a gonakin inabi ku lura. Sa’ad da ’yan matan Shilo suka fito waje don su yi rawa, ku fito a guje daga gonakin inabi, kowannenku yă kama wa kansa mata daga cikin ’yan matan Shilo, ku tafi ƙasar Benyamin.
  • Mata suna rawa suna waƙa: “Shawulu ya kashe dubbai”1Sam 18:6–7, 1Sam 21:11
    Ayoyin
    1Sam 18:6–7Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa. Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”
    1Sam 21:11Amma bayin Akish suka ce masa, “Wannan ba shi ne Dawuda sarkin ƙasar ba? Ashe, ba shi ne aka yi ta yin waƙoƙi a kansa, ana raye-raye, ana cewa, “Shawulu ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai?”
  • Dawuda ya yi rawa da dukan ƙarfinsa a gaban akwatin alkawari2Sam 6:14–16
    Ayoyin
    2Sam 6:14–16Dawuda, sanye da efod lilin, ya yi ta rawa a gaban Ubangiji da dukan ƙarfinsa, yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni. Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal ’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.
  • Mikal ta ga Sarki Dawuda yana rawa ta raina shi1Tar 15:29
    Ayoyin
    1Tar 15:29Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal ’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.
  • Yara suna tsalle da ganga da moloAyu 21:11–12
    Ayoyin
    Ayu 21:11–12Suna aika ’ya’yansu kamar garke; ’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle. Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya; suna jin daɗin busar sarewa.
  • “Ka mai da kukata ta zama rawa”Zab 30:11
    Ayoyin
    Zab 30:11Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,
  • Ku yabe shi da ganga da rawaZab 149:3, Zab 150:4
    Ayoyin
    Zab 149:3Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.
    Zab 150:4yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
  • Akwai lokacin makoki da lokacin rawaM Had 3:4
    Ayoyin
    M Had 3:4Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa.
  • “rawar Mahanayim”WW 6:13
    Ayoyin
    WW 6:13Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya; ki dawo, ki dawo, don mu dube ki! Don me kuke duban Bashulammiya sai ka ce rawar Mahanayim?
  • ’Yan mata suna farin ciki da rawa, samari da tsofaffi maIrm 31:4, Irm 31:13
    Ayoyin
    Irm 31:4Zan sāke gina ki za ki kuwa sāke ginuwa, ya Budurwar Isra’ila. Za ki kuma ɗauki ganganki ki fita don ki yi rawa da masu farin ciki.
    Irm 31:13’Yan mata za su yi rawa su kuma yi murna, haka ma samari da tsofaffi. Zan mai da makokinsu farin ciki; zan ta’azantar da su in kuma sa su yi farin ciki a maimakon baƙin ciki.
  • “Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki”Mako 5:15
    Ayoyin
    Mako 5:15Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki.
  • Yara a kasuwa: “Mun yi muku busa, ba ku kuwa yi rawa ba”Mat 11:17
    Ayoyin
    Mat 11:17“ ‘Mun yi muku busa, ba ku kuwa yi rawa ba, mun rera waƙar makoki, ba ku kuwa yi makoki ba.’
  • Kiɗa da rawa domin ɗan da ya dawoLuk 15:25
    Ayoyin
    Luk 15:25“Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa.
  • ’Yar Hiridiyas ta yi rawa a liyafar ranar haihuwar HiridusMat 14:6–7, Mar 6:22
    Ayoyin
    Mat 14:6–7A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai, har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa.
    Mar 6:22Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa. Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.”

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.