Bincika › Jigogi › Al’adun makoki
Rayuwar yau da kullum
Al’adun makoki a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (55), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Kece tufafi sa’ad da aka ji mummunan labariFar 37:29, Far 37:34, Far 44:13, 2Sam 1:11, 2Sam 13:31, Ayu 1:20, 2Sar 2:12
Ayoyin
Far 37:29Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa.
Far 37:34Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa.
Far 44:13Ganin wannan sai suka kyakkece rigunansu. Sa’an nan suka jibga wa jakunansu kaya, suka koma birni.
2Sam 1:11Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka yayyage rigunarsu.
2Sam 13:31Sai sarki ya tashi, ya yage tufafinsa, ya kuma kwanta a ƙasa; dukan bayinsa kuwa suka tsaya da rigunansu yagaggu.
Ayu 1:20Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada
2Sar 2:12Da Elisha ya ga haka sai ya yi ihu yana cewa, “Babana! Babana! Kekunan yaƙin da mahayan dawakan Isra’ila!” Elisha kuwa bai sāke ganinsa ba. Sai ya kama tufafinsa ya yayyage.
- Tsummokin makoki a kewaye da kwankwasoFar 37:34, 1Sar 21:27, Esta 4:1
Ayoyin
Far 37:34Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa.
1Sar 21:27Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai.
Esta 4:1Sa’ad da Mordekai ya sami labari game da dukan abin da aka yi, sai ya yayyage rigunansa, ya sanya tsummokin makoki, ya zuba toka a kā, ya kuma shiga ciki birni yana kuka mai zafi da ƙarfi.
- Ƙura ko toka a kaiYosh 7:6, 2Sam 13:19, 2Sam 15:32, Ayu 2:12
Ayoyin
Yosh 7:6Sai Yoshuwa ya yaga tufafinsa ya fāɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, yana can har yamma. Dattawan Isra’ila ma suka yi haka, suka zuba toka a kawunansu.
2Sam 13:19Sai Tamar ta zuba toka a kanta, ta kuma yayyage doguwar riga mai kayan adon da take sanye da shi. Ta sa hannunta a kai, ta tafi tana kuka da ƙarfi.
2Sam 15:32Da Dawuda ya isa ƙwanƙoli, inda mutane sun saba yi wa Allah sujada, Hushai, mutumin Arkitawa kuwa yana can don yă tarye shi, taguwarsa a yage, ga kuma ƙura a kansa.
Ayu 2:12Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu,
- Kwanciya cikin tsummokin makoki da tokaEsta 4:3, Yun 3:6
Ayoyin
Esta 4:3Aka yi makoki sosai da azumi, da kuka mai zafi a cikin Yahudawa a kowane lardin da aka kai doka da kuma umarnin sarki. Mutane da yawa suka kwanta a cikin tsummokin makoki da kuma toka.
Yun 3:6Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.
- Kwanciya a ƙasa2Sam 12:16, 2Sam 13:31
Ayoyin
2Sam 12:16Dawuda ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi, ya kuma shiga gidansa ya kwana kwance a ƙasa.
2Sam 13:31Sai sarki ya tashi, ya yage tufafinsa, ya kuma kwanta a ƙasa; dukan bayinsa kuwa suka tsaya da rigunansu yagaggu.
- Rufe kai da tafiya ba takalma2Sam 15:30
Ayoyin
2Sam 15:30Amma Dawuda ya ci gaba yana hawan Dutsen Zaitun, yana kuka yayinda yake tafiya; kansa a rufe, kuma babu takalma a ƙafafunsa. Dukan mutanen da suke tare da shi suka rufe kawunansu suna ta kuka yayinda suke haurawa.
- Rufe fuska2Sam 19:4, Esta 6:12
- Tuge gashi daga kai da gemuEzr 9:3
Ayoyin
Ezr 9:3Sa’ad da na ji wannan, sai na yaga rigata da alkyabbata, na tsittsige gashin kaina da na gemuna, na zauna, na rasa abin da yake mini daɗi.
- Aske kaiAyu 1:20, Ezk 27:31
- Cire kayan adoFit 33:4–6
Ayoyin
Fit 33:4–6Da mutane suka ji wannan mugun magana, sai suka fara makoki. Ba kuma wanda ya sa kayan ado. Gama Ubangiji ya riga ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurinkai. In na yi tafiya da ku ko na ɗan lokaci, mai yiwuwa in hallaka ku. Yanzu sai ku tuɓe kayan adonku, zan kuwa yanke shawara a kan abin da zan yi da ku.’ ” Saboda haka Isra’ilawa suka tuttuɓe kayan adonsu a Dutsen Horeb.
- Ba shafa mai, da tufafin makoki2Sam 14:2, Dan 10:3
Ayoyin
2Sam 14:2Saboda haka Yowab ya aiki wani zuwa Tekowa, ya sa a zo da wata mace mai hikima. Ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki. Ki sa rigar makoki, kada kuwa ki shafa mai. Ki yi kamar macen da ta yi kwanaki da yawa, tana makokin matattu.
Dan 10:3Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.
- Masu makoki suna yawo a titunaM Had 12:5
Ayoyin
M Had 12:5sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu da kuma hatsarori a tituna; sa’ad da itacen almon ya toho, fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar, sha’awace-sha’awace sun kafe. Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa ya bar masu makoki suna ta yi.
- Akan kira gwanayen mata masu kuka su yi makokiIrm 9:17–18
Ayoyin
Irm 9:17–18Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku lura yanzu! Ku kira mata masu makoki su zo ku aika wa gwanaye a cikinsu su zo. Bari su zo da sauri su yi kuka a kanmu sai idanunmu sun cika da hawaye giranmu kuma su jiƙe sharkaf.
- Masu busan sarewa da taro mai hayaniya a gidan yarinyar da ta mutuMat 9:23
Ayoyin
Mat 9:23Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya,
- Abokai sukan zo su ta’azantar da iyaliYoh 11:19, Yoh 11:31
A cikin Doka
- Ba yanka jiki ko aske goshi saboda matattuFir 19:28, M Sh 14:1
- Taɓa gawa yakan sa mutum ya zama marar tsarki kwana bakwaiƘid 19:11, Ƙid 19:16
- Firistoci za su iya ƙazantar da kansu saboda iyali na kusa kaɗaiFir 21:1–3
Ayoyin
Fir 21:1–3Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da firistoci, ’ya’yan Haruna maza, ka ce musu, ‘Kada firist yă ƙazantar da kansa saboda wani cikin mutanensa da suka mutu, sai dai na danginsa na kusa, kamar mahaifiyarsa ko mahaifinsa, ɗansa ko ’yarsa, ɗan’uwansa, ko ’yar’uwarsa da ba tă riga ta yi aure ba, wadda take dogara gare shi, da yake ba ta da miji, saboda ita zai iya ƙazantar da kansa.
- Kada babban firist ya kece tufafinsa ko ya kusaci gawaFir 21:10–11
Ayoyin
Fir 21:10–11“ ‘Babban firist, wanda yake ɗaya cikin ’yan’uwansa wanda aka shafe da mai a kansa, wanda kuma aka naɗa don yă sa rigunan firistoci, kada yă bar gashin kansa buzu-buzu, ko ya kyakketa rigunansa. Ba zai shiga inda akwai gawa ba. Kada yă ƙazantar da kansa, ko ma ta mahaifinsa ce ko ta mahaifiyarsa.
- Kada Haruna da ’ya’yansa maza su yi makokin Nadab da AbihuFir 10:6
Ayoyin
Fir 10:6Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta.
- Ba a ci kome na zakka sa’ad da ake makoki baM Sh 26:14
Ayoyin
M Sh 26:14Ban ci wani daga cikin tsattsarkan rabo yayinda nake makoki, ko in cire wani rabo mai tsarki yayinda nake marar tsarki, ko in miƙa wani sashensa ga matattu ba. Na yi biyayya ga Ubangiji Allahna, na aikata kome da ka umarce ni.
Misalai
- Ibrahim ya yi makoki ya yi kuka saboda SaratuFar 23:2
Ayoyin
Far 23:2Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.
- Yaƙub ya ƙi a ta’azantar da shi saboda YusufFar 37:34–35
Ayoyin
Far 37:34–35Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa. Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.
- Masar ta yi makokin Yaƙub kwana saba’in; Yusuf ya yi makoki kwana bakwai a AtadFar 50:3, Far 50:10–11
Ayoyin
Far 50:3Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi makoki dominsa kwana saba’in.
Far 50:10–11Sa’ad da suka kai masussukar Atad, kusa da Urdun, sai suka yi kuka da ƙarfi da kuma mai zafi, a can Yusuf ya yi makoki kwana bakwai saboda mahaifinsa. Sa’ad da Kan’aniyawa waɗanda suke zama a can suka ga makokin a masussukan Atad, sai suka ce, “Masarawa suna bikin makoki na musamman.” Shi ya sa ake kira wannan wurin da yake kusa da Urdun, Abel-Mizrayim.
- Isra’ila sun yi makoki kwana talatin saboda Haruna, talatin kuma saboda MusaƘid 20:28–29, M Sh 34:8
Ayoyin
Ƙid 20:28–29Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen, sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin.
M Sh 34:8Isra’ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab kwana talatin, sai da lokacin kuka, da na makoki suka ƙare.
- Babbar kuka a Masar: babu gidan da ba wanda ya mutuFit 12:30
Ayoyin
Fit 12:30Fir’auna da dukan fadawansa da kuma dukan Masarawa, suka tashi a cikin daren da kuka mai zafi, aka kuma ji kukan a ko’ina a cikin ƙasar Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.
- Dawuda da mutanensa sun yi kuka har ba sauran ƙarfi1Sam 30:4
Ayoyin
1Sam 30:4sai Dawuda da mutanensa suka yi kuka, suka yi ta kuka har sai da ƙarfinsu ya ƙare.
- Makokin Dawuda saboda Shawulu da Yonatan: “jarumawa sun fāɗi!”2Sam 1:17–19
Ayoyin
2Sam 1:17–19Dawuda ya rera wannan makoki saboda Shawulu da ɗansa Yonatan. Ya umarta a koya wa mutanen Yahuda wannan waƙa mai suna Makokin Baka (tana a rubuce a Littafin Yashar), “Ya Isra’ila, an kashe darajarki a kan tuddanki. Ga shi, jarumawa sun fāɗi!
- Makokin Dawuda saboda Abner2Sam 3:33–34
Ayoyin
2Sam 3:33–34Sarki ya kuma yi wannan waƙar makoki domin Abner ya ce, “Daidai ne Abner yă mutu, kamar yadda marasa bin doka suke mutuwa? Hannuwanka ba a daure suke ba, ƙafafunka ba a tabaibaye suke ba. Ka mutu kamar waɗanda suke mutuwa a hannun mugaye.” Sai dukan mutane suka sāke fashe da kuka saboda shi.
- “Ya ɗana Absalom! Ya Absalom ɗana, ɗana!”2Sam 18:33, 2Sam 19:4
Ayoyin
2Sam 18:33Sai gaban sarki ya faɗi. Ya haura zuwa ɗakin da yake kan katangar hanyar shiga ya yi kuka. Yayinda yake tafiya ya ce, “Ya ɗana Absalom! Ɗana, ɗana Absalom! Da ma a ce ni ne na mutu maimakonka. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”
2Sam 19:4Sarki ya rufe fuskarsa ya yi kuka da ƙarfi yana cewa, “Ya ɗana Absalom! Ya Absalom ɗana, ɗana!”
- Batsheba ta yi makokin Uriya2Sam 11:26–27
Ayoyin
2Sam 11:26–27Da matar Uriya ta ji cewa mijinta ya mutu, sai ta yi makoki saboda shi. Bayan kwanakin makoki suka ƙare, Dawuda ya sa aka kawo ta gidansa, ta kuwa zama matarsa, ta kuma haifa masa ɗa. Sai dai abin da Dawuda ya yi bai gamshi Ubangiji ba.
- Mawaƙa maza da mata sun rera waƙoƙin makoki saboda Yosiya2Tar 35:24–25
Ayoyin
2Tar 35:24–25Saboda haka suka ɗauke shi a keken yaƙin, suka fitar da shi, suka sa shi a wata keken yaƙin da yake da shi, suka kawo shi Urushalima, inda ya mutu. Aka binne shi a makabartar kakanninsa, sai dukan Yahuda da Urushalima suka yi makoki dominsa. Annabin Irmiya ya tsara waƙoƙin makoki domin Yosiya, wanda har wa yau mawaƙa maza da mata suke rera game da Yosiya. Suka sa waɗannan su zama al’ada a Isra’ila, suna kuma a rubuce cikin Littafin Makoki.
- Mordekai ya yi kuka cikin tsummokin makoki; an hana tsummokin makoki a ƙofar sarkiEsta 4:1–2
Ayoyin
Esta 4:1–2Sa’ad da Mordekai ya sami labari game da dukan abin da aka yi, sai ya yayyage rigunansa, ya sanya tsummokin makoki, ya zuba toka a kā, ya kuma shiga ciki birni yana kuka mai zafi da ƙarfi. Amma ya kai bakin ƙofar sarki ne kawai, gama ba a yarda wani sanye da tsummokin makoki yă shiga cikin birni ba.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.