Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Rashin lafiya da likitoci

Rayuwar yau da kullum

Rashin lafiya da likitoci a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (41), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Likitoci

  • Likitocin Yusuf sun shafe jikin Yaƙub da maganin adana gawaFar 50:2
    Ayoyin
    Far 50:2Sa’an nan Yusuf ya umarci masu maganin da suke yin masa hidima, su shafe mahaifinsa Isra’ila da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe shi da maganin hana ruɓa.
  • Asa, da ciwo a ƙafafunsa, ya nemi likitoci2Tar 16:12, 1Sar 15:23
    Ayoyin
    2Tar 16:12A shekara ta talatin da tara ta mulkinsa, Asa ya kamu da wata cuta a ƙafarsa. Ko da yake cutar ta yi tsanani, duk d haka ma a cikin ciwonsa bai nemi taimako daga Ubangiji ba, sai dai daga likitoci.
    1Sar 15:23Game da sauran ayyukan mulkin Asa, dukan nasarorinsa, dukan abin da ya yi, da kuma biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. A tsufansa, sai ƙafafunsa suka kamu da cuta.
  • Wata mace da take zubar jini shekara goma sha biyu ta kashe dukan abin da take da shi ga likitociMar 5:25–26, Luk 8:43
    Ayoyin
    Mar 5:25–26A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni.
    Luk 8:43A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita.
  • “ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya”Mat 9:12
    Ayoyin
    Mat 9:12Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
  • Karin magana: “Likita, warkar da kanka!”Luk 4:23
    Ayoyin
    Luk 4:23Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”
  • Luka, “ƙaunataccen likitan nan”Kol 4:14
    Ayoyin
    Kol 4:14Luka ƙaunataccen likitan nan, da kuma Demas suna gaishe ku.
  • “Ba magani ne a Gileyad? Ba likita ne a can?”Irm 8:22
    Ayoyin
    Irm 8:22Ba magani ne a Gileyad? Ba likita ne a can? To, me ya sa ba warkarwa wa raunin mutanena?

Magunguna

  • Kwaɓin ɓaure domin marurun Hezekiya2Sar 20:7, Ish 38:21
    Ayoyin
    2Sar 20:7Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke.
    Ish 38:21Ishaya ya riga ya ce, “Ku shirya curin da aka yi da ’ya’yan ɓaure ku kuma shafa a marurun, zai kuwa warke.”
  • Mutumin Samariya ya ɗaure raunuka, yana zuba mai da ruwan inabiLuk 10:34
    Ayoyin
    Luk 10:34Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.
  • Ruwan inabi kaɗan domin ciki da yawan rashin lafiya1Tim 5:23
    Ayoyin
    1Tim 5:23Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.
  • Akan shafa wa marasa lafiya maiMar 6:13, Yaƙ 5:14
    Ayoyin
    Mar 6:13Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.
    Yaƙ 5:14Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji.
  • Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyauK Mag 17:22
    Ayoyin
    K Mag 17:22Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.

Misalai

  • Yaƙub ya kamu da rashin lafiya; Yusuf ya kawo ’ya’yansa maza biyuFar 48:1
    Ayoyin
    Far 48:1Bayan wani lokaci aka faɗa wa Yusuf, “Mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ’ya’yansa maza biyu, Manasse da Efraim suka tafi tare da shi.
  • Maigidan wani bawa Bamasare ya bar shi sa’ad da ya kamu da rashin lafiya1Sam 30:13
    Ayoyin
    1Sam 30:13Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Wane ne ubangidanka, kuma daga ina ka fito?” Ya ce, “Ni mutumin Masar ne, bawan wani mutumin Amalek. Maigidana ya ƙyale ni sa’ad da na yi rashin lafiya kwanaki ukun da suka wuce.
  • Ɗan Yerobowam ya kamu da rashin lafiya; mahaifiyarsa ta ɓad da kama ta je wurin annabi1Sar 14:1–3
    Ayoyin
    1Sar 14:1–3A lokacin Abiya, ɗan Yerobowam ya kamu da ciwo, sai Yerobowam ya ce wa matarsa, “Ki tafi, ki ɓad da kama, don kada a gane ke a matsayin matar Yerobowam. Ki je Shilo. Annabi Ahiya yana a can, wannan wanda ya ce mini zan zama sarki a bisa wannan mutane. Ki ɗauki dunƙulen burodi goma tare da ke, da waina, da tulun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.”
  • Ɗan gwauruwar Zarefat ya kamu da rashin lafiya1Sar 17:17
    Ayoyin
    1Sar 17:17Ana nan sai ɗan matan, wato, gwauruwan nan ya fara ciwo. Ciwon ya ƙara muni, daga ƙarshe sai ya daina numfashi.
  • Yaron matar Shunam a gona: “Kaina yana mini ciwo! Kaina yana mini ciwo!”2Sar 4:18–20
    Ayoyin
    2Sar 4:18–20Yaron ya yi girma, wata rana sai ya tafi wurin mahaifinsa, wanda yake tare da masu girbi. Ba zato sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo! Kaina yana mini ciwo! Kaina yana mini ciwo!” Sai mahaifinsa ya ce wa bawansa, “Kai shi wurin mahaifiyarsa.” Bayan bawan ya ɗaga shi ya kai wurin mahaifiyarsa, sai yaron ya zauna a cinyarta har tsakar rana, sa’an nan ya mutu.
  • Ahaziya ya ji rauni sa’ad da ya fāɗi ta cikin asabari2Sar 1:2
    Ayoyin
    2Sar 1:2Ahaziya fa ya fāɗo daga tagar ɗakin samansa a Samariya ya ji rauni. Saboda haka ya aiki masinjoji, yana cewa, “Ku je ku tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron, ku ga ko zan warke daga wannan rauni.”
  • Ben-Hadad na Aram ya tambayi Elisha ko zai warke2Sar 8:7–8
    Ayoyin
    2Sar 8:7–8Sai Elisha ya tafi Damaskus, Ben-Hadad mutumin Aram kuwa yana ciwo. Sa’ad da aka faɗa wa sarki, “Mutumin Allah ya hauro tun daga can zuwa nan,” sai ya ce wa Hazayel, “Ɗauki wannan tare da kai ka tafi ka taryi mutumin Allah. Ka nemi nufin Ubangiji ta wurinsa; ka tambaye shi, ‘Zan warke daga ciwon nan?’ ”
  • Elisha ya kamu da ciwon da ya mutu da shi2Sar 13:14
    Ayoyin
    2Sar 13:14To, Elisha ya kamu da ciwon da ya kashe shi. Yowash sarkin Isra’ila ya gangara don yă gan shi, ya kuma yi kuka dominsa. Ya yi kuka yana cewa, “Babana! Babana, keken yaƙin Isra’ila da mahayan dawakanta!”
  • Hezekiya ya yi rashin lafiya har ya kusa mutuwa, sa’an nan ya warkeIsh 38:1, 2Sar 20:7
    Ayoyin
    Ish 38:1A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.”
    2Sar 20:7Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke.
  • Ayuba, cike da marurai, yana sosa jikinsa da kaskon tukunyaAyu 2:7–8
    Ayoyin
    Ayu 2:7–8Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa. Sai Ayuba ya ɗauki kaskon tukunya yana ta sosa ƙurajen da shi, yayinda yake zaune cikin toka.
  • Daniyel ya kwanta da rashin lafiya kwanaki bayan wani wahayiDan 8:27
    Ayoyin
    Dan 8:27Ni, Daniyel, na gaji matuƙa na kuma yi rashin lafiya na kwanaki masu yawa. Sa’an nan sai na tashi na ci gaba da hidimar sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ya fi ƙarfin fahimtata.
  • Surukar Bitrus tana kwance da zazzaɓi mai zafiMat 8:14, Luk 4:38
    Ayoyin
    Mat 8:14Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi.
    Luk 4:38Yesu ya fita daga majami’ar, ya tafi gidan Siman. Surukar Siman kuwa tana fama da zazzaɓi mai tsanani, sai suka roƙi Yesu yă taimake ta.
  • Ɗan wani ma’aikacin fāda yana kwance da rashin lafiya a KafarnahumYoh 4:46–47
    Ayoyin
    Yoh 4:46–47Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.
  • Wani yaro mai farfaɗiya yakan fāɗi cikin wuta ko ruwaMat 17:15
    Ayoyin
    Mat 17:15Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa.
  • Marasa lafiya da yawa suna kwance a tafkin Betesda; wani mutum shekara talatin da takwasYoh 5:2–3, Yoh 5:5
    Ayoyin
    Yoh 5:2–3To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar. A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu.
    Yoh 5:5Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas.
  • Wani mutum gurgu tun haihuwa ana kai shi ƙofar haikali kowace ranaAyy M 3:2
    Ayoyin
    Ayy M 3:2To, sai ga wani da aka haifa gurgu ana ɗauke da shi zuwa ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, inda akan ajiye kowace rana, don yă yi bara daga masu shigowa cikin filayen haikali.
  • Lazarus na Betani yana rashin lafiya; ’yan’uwansa mata sun aika wa Yesu labariYoh 11:1–3
    Ayoyin
    Yoh 11:1–3To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta. Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.”
  • Dokas ta kamu da rashin lafiya ta mutuAyy M 9:37
    Ayoyin
    Ayy M 9:37A lokacin nan ta yi rashin lafiya ta mutu, aka kuma yi wa gawarta wanka aka ajiye a wani ɗaki a gidan sama.
  • Mahaifin Fubiliyus yana fama da zazzaɓi da atuniAyy M 28:8
    Ayoyin
    Ayy M 28:8Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi.
  • Afaforiditus ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwaFil 2:25–27
    Ayoyin
    Fil 2:25–27Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna. Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya. Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.
  • Bulus ya fara wa’azi a Galatiya saboda rashin lafiyaGal 4:13–14
    Ayoyin
    Gal 4:13–14Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko. Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.
  • Bulus ya bar Turofimus da rashin lafiya a Miletus2Tim 4:20
    Ayoyin
    2Tim 4:20Erastus ya dakata a Korint, na kuma bar Turofimus cikin rashin lafiya a Miletus.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.