Bincika › Jigogi › Bukukuwan aure da aure
Rayuwar yau da kullum
Bukukuwan aure da aure a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (53), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Al’adu
- Iyaye ne sukan nema wa ’ya’yansu maza mataFar 21:21, Far 24:3–4, Far 28:1–2, Irm 29:6
Ayoyin
Far 21:21Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar.
Far 24:3–4Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba. Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.”
Far 28:1–2Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana. Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin ’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka.
Irm 29:6Ku yi aure ku kuma haifi ’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa ’ya’yanku maza, ku kuma ba da ’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi ’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.
- Samson ya roƙi iyayensa su auro masa mace BafilistiyaMah 14:2
Ayoyin
Mah 14:2Da ya komo, sai ya gaya wa mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, “Na ga wata mace a Timna; ku auro mini ita ta zama matata.”
- An tambayi Rebeka: “Za ki tafi tare da mutumin nan?”Far 24:57–58
Ayoyin
Far 24:57–58Sa’an nan suka ce, “Bari mu kira yarinyar mu tambaye ta game da zancen.” Saboda haka suka kira Rebeka suka ce mata, “Za ki tafi tare da mutumin nan?” Sai ta ce, “Zan tafi.”
- Rebeka ta rufe kanta da mayafinta sa’ad da ta sadu da IshakuFar 24:65
Ayoyin
Far 24:65ta ce wa bawan, “Wane ne mutumin can a fili, da yake zuwa yă tarye mu?” Bawan ya ce, “Maigidana ne.” Saboda haka ta ɗauki mayafinta to rufe kanta.
- Kayan ado da tufafi domin amarya, kyautai domin iyalintaFar 24:53
Ayoyin
Far 24:53Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada.
- Ana biyan sadaki ga mahaifin amaryaFar 34:12, Fit 22:16–17
Ayoyin
Far 34:12Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.”
Fit 22:16–17“Idan mutum ya ruɗe budurwa, wadda ba wanda yake nemanta, ya kuma kwanta da ita, dole yă biya kuɗin aurenta, za tă kuma zama matarsa. In mahaifinta ya ƙi yă ba da ita ga mutumin, dole mutumin yă biya dukiya daidai da abin da akan biya domin budurwai.
- Laban: ba al’adarmu ba ce a aurar da ƙarama kafin babbaFar 29:26
Ayoyin
Far 29:26Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da ’ya ƙarama aure kafin ’yar fari.
- Mako guda na bikin aureFar 29:22, Far 29:27–28
Ayoyin
Far 29:22Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki.
Far 29:27–28Ka gama makon amaryanci na ’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.” Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa.
- Ango ya yi biki na kwana bakwai tare da abokai talatinMah 14:10–12
Ayoyin
Mah 14:10–12To, mahaifinsa ya gangara don yă ga yarinyar. Samson kuwa ya shirya wata liyafa a can, yadda yake bisa ga al’adar angwaye. Sa’ad da ya bayyana, sai aka haɗa shi abokai talatin. Sai Samson ya ce, “Bari in yi muku kacici-kacici, in kun ba ni amsa cikin kwana bakwai na wannan biki, zan ba ku riguna lilin talatin da kuma tufafi talatin.
- Kayan adon amarya da ɗamarar aurentaIrm 2:32, Ish 61:10
Ayoyin
Irm 2:32Budurwa za tă manta da kayan adonta amarya ta manta da kayan adon aurenta? Duk da haka mutanena sun manta da ni, kwanaki ba iyaka.
Ish 61:10Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji; raina yana farin ciki a cikin Allahna. Gama ya suturce ni da rigunan ceto ya yi mini ado da rigar adalci, yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
- Gimbiya cikin riga mai adon zinariya tare da ƙawayentaZab 45:13–14
Ayoyin
Zab 45:13–14Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun; an saƙa rigarta da zaren zinariya. Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka.
- Rawanin Solomon daga mahaifiyarsa a ranar aurensaWW 3:11
Ayoyin
WW 3:11Fito, ku ’yan matan Sihiyona, ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani, rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa, a ranar aurensa, a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki.
- Muryoyin amarya da ango sun cika titunaIrm 7:34
Ayoyin
Irm 7:34Zan kawo ƙarshen muryar murna da farin ciki da muryar amarya da ango a garuruwan Yahuda da kuma a titunan Urushalima, gama ƙasar za tă zama kufai.
- ’Yan mata goma da fitilu sun fita don su taryi ango (misali)Mat 25:1–6
Ayoyin
Mat 25:1–6“A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba. Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu. Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su. “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’
- Ana sa rai baƙi su sa tufafin aure (misali)Mat 22:11–12
Ayoyin
Mat 22:11–12“Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren. Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.
- Dattawa a ƙofar birni sun zama shaidun aureRut 4:9–11
Ayoyin
Rut 4:9–11Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon. Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!” Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.
- Ana kiran Yusuf mijin Maryamu tun suna cikin alkawarin aure kawaiMat 1:18–19, Luk 1:27
Ayoyin
Mat 1:18–19Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki. Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye.
Luk 1:27gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu.
A cikin Doka
- Sabon ango ba zai tafi yaƙi ba har shekara ɗayaM Sh 24:5
Ayoyin
M Sh 24:5In mutum bai daɗe da aure ba, kada a sa yă je yaƙi, ko yă yi wani aiki. Gama zai huta shekara guda a gida, yă faranta wa matar da ya aura rai.
- Ɗan’uwa yakan auri gwauruwar ɗan’uwansa da ya mutu babu ɗaM Sh 25:5–10, Far 38:8, Mar 12:19
Ayoyin
M Sh 25:5–10In ’yan’uwa suna zama tare, in ɗayansu ya mutu babu ɗa, kada gwauruwar tă yi aure waje da iyalin. Ɗan’uwan mijinta zai ɗauke ta, yă aure ta, yă kuma cika abin da yă kamaci ɗan’uwan miji yă yi. Ɗan farin da ta haifa zai ɗauki sunan ɗan’uwan da ya rasu saboda kada sunansa yă ɓace daga Isra’ila. Amma fa, in mutum ba ya so yă auri matar ɗan’uwansa, sai tă tafi wurin dattawa a ƙofar gari tă ce, “Ɗan’uwan mijina ya ƙi yă wanzar da sunan ɗan’uwansa a Isra’ila. Ya ƙi yă cika abin da ya kamaci ɗan’uwan miji yă yi gare ni.” Sai dattawan garinsa su kira shi, su kuma yi masa magana. In ya nace yana cewa, “Ba na so in aure ta,” sai gwauruwan nan, matar ɗan’uwansa tă haura wurinsa a gaban dattawa, tă tuɓe takalminsa guda, ta tofa masa miyau a fuska, tă ce, “Haka za a yi ga mutumin da zai ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.” Za a kira zuriyarsa a Isra’ila Iyalin da aka tuɓe masa takalmi.
Far 38:8Sa’an nan Yahuda ya ce wa Onan, “Ka kwana da matar ɗan’uwanka ka cika wajibinka gare ta a matsayin ɗan’uwan miji, don ka samar wa ɗan’uwanka ’ya’ya.”
Mar 12:19Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.
- Dole ’ya’yan Zelofehad mata su yi aure cikin kabilar mahaifinsuƘid 36:6–8
Ayoyin
Ƙid 36:6–8Ga abin da Ubangiji ya umarta saboda ’ya’ya matan nan na Zelofehad. Za su iya auri duk wanda suka ga dama, muddin sun yi aure a cikin kabilar kakanninsu. Ba gādon Isra’ilan da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowane mutumin Isra’ila zai riƙe gādonsa na kabilar da ya gāda daga kakanninsa. Kowace ’ya wadda ta ci gādon ƙasa, a kowace kabilar Isra’ilawa, dole tă auri wani cikin kabilar kakanninta, saboda kowane mutumin Isra’ila yă mallaki gādon kakanninsa.
- Firistoci ba za su auri macen da mijinta ya sake ta baFir 21:7, Fir 21:13–14
Ayoyin
Fir 21:7“ ‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu.
Fir 21:13–14“ ‘Dole macen da zai aura ta kasance budurwa. Ba zai auri matan da mijinta ya mutu, ko macen da mijinta ya rabu da ita, ko macen da ta ɓata kanta ta wurin karuwanci ba, sai dai yă auri budurwa daga cikin mutanensa,
- Mace da aka kama a yaƙi takan yi makokin iyayenta wata guda tukunaM Sh 21:10–13
Ayoyin
M Sh 21:10–13Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, sai Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannuwanku kuka kuma kama su a matsayin bayi, in ka ga wata kyakkyawar mace wadda ta ɗauki hankalinka a cikin bayin, za ka iya aure ta tă zama matarka. Ka kawo ta gidanka ka sa tă aske kanta, tă yanka kumbanta tă kuma tuɓe tufafin da ta sa sa’ad da aka kama ta. Bayan ta zauna a gidanka ta kuma yi makokin mahaifinta da mahaifiyarta wata ɗaya cif, sai ka shiga wurinta ka zama mijinta, za tă kuwa zama matarka.
- An gaya wa Isra’ilawa kada su yi auratayya da al’umman Kan’anaM Sh 7:3
Ayoyin
M Sh 7:3Kada ku yi auratayya da su. Kada ku ba da ’ya’yanku mata wa ’ya’yansu maza, ko ku ɗauko ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza.
Misalai
- Ibrahim ya auri Saratu, ’yar’uwarsa ta wajen ubaFar 11:29, Far 20:12
- Ishaku ya ƙaunaci Rebeka, aka kuma ta’azantar da shi bayan mutuwar mahaifiyarsaFar 24:67
Ayoyin
Far 24:67Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.
- Yaƙub ya yi aiki shekara bakwai saboda Rahila; suka zama kamar ’yan kwanakiFar 29:18–20
Ayoyin
Far 29:18–20Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar ’yarka Rahila.” Laban ya ce, “Ya fi kyau in ba ka ita, da in ba wani mutum dabam. Zauna tare da ni.” Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar ’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata.
- An fara ba Yaƙub Liyatu, sa’an nan RahilaFar 29:21–28
Ayoyin
Far 29:21–28Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.” Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki. Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki ’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita. Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa ’yarsa tă zama mai hidimarta. Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?” Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da ’ya ƙarama aure kafin ’yar fari. Ka gama makon amaryanci na ’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.” Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa.
- Kaleb ya ba da ’yarsa Aksa ga mutumin da ya ci Kiriyat SeferMah 1:12–13
Ayoyin
Mah 1:12–13Sai Kaleb ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat Sefer ya kuma ci ta da yaƙi, zan ba shi ’yata Aksa yă aura.” Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb ya ci birnin, saboda haka Kaleb ya ba shi ’yarsa Aksa ya aura.
- Shawulu ya yi alkawarin ba da ’yarsa ga mutumin da ya kashe Goliyat1Sam 17:25, 1Sam 18:17
Ayoyin
1Sam 17:25Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.”
1Sam 18:17Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”
- Shawulu ya nemi loɓar Filistiyawa ɗari; Dawuda ya kawo ɗari biyu1Sam 18:25–27, 2Sam 3:14
Ayoyin
1Sam 18:25–27Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa. Da ma’aikatan suka gaya wa Dawuda waɗannan abubuwa, sai ya yi murna don zai zama surukin sarki. Amma kafin lokacin yă cika, Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da ’yarsa Mikal aure ga Dawuda.
2Sam 3:14Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”
- Bowaz ya ɗauki Rut matarsa a gaban shaiduRut 4:5, Rut 4:10
Ayoyin
Rut 4:5Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.”
Rut 4:10Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!”
- Mutanen Benyamin sun kama mata daga cikin masu rawa na ShiloMah 21:21–23
Ayoyin
Mah 21:21–23ku lura. Sa’ad da ’yan matan Shilo suka fito waje don su yi rawa, ku fito a guje daga gonakin inabi, kowannenku yă kama wa kansa mata daga cikin ’yan matan Shilo, ku tafi ƙasar Benyamin. Sa’ad da iyayensu maza ko ’yan’uwansu suka kawo mana ƙara, za mu ce musu, ‘Ku yi mana alheri ku bar su, domin ba mu samo musu mata ba lokacin yaƙi, ku kuma marasa laifi ne, tun da yake ba ku ba da ’ya’yan matanku gare su ba.’ ” Haka mutanen Benyamin suka yi. Yayinda ’yan matan suke rawa, kowane mutum ya kama ɗaya ya yi gaba da ita ta zama matarsa. Sa’an nan suka komo ƙasar gādonsu suka sāke giggina garuruwan suka kuwa zauna a cikinsu.
- Zerzes ya naɗa Esta sarauniya ya kuma yi bikin EstaEsta 2:17–18
Ayoyin
Esta 2:17–18To, sarki ya so Esta fiye da duk sauran matan, ta kuma sami tagomashinsa da kuma yardarsa fiye da duk sauran budurwai. Saboda haka ya sa rawanin sarauta a kanta, ya kuma mai da ita sarauniya a maimakon Bashti. Sarki kuwa ya yi ƙasaitacciyar liyafa, liyafar Esta, wa dukan hakimansa da shugabannin masarautarsa. Ya yi shelar hutu ko’ina a larduna, ya kuma raba kyautai a yalwace irin na sarauta.
- Hosiya ya sayi wata mace da shekel goma sha biyar na azurfa da sha’irHos 3:2
Ayoyin
Hos 3:2Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir.
- Yesu da almajiransa a wani bikin aure a KanaYoh 2:1–10
Ayoyin
Yoh 2:1–10A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can, aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.” Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.” Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin. Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal. Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.” Suka yi haka. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”
- Manzanni sukan tafi da matansu cikin tafiye-tafiyensu1Kor 9:5
Ayoyin
1Kor 9:5Ba mu da ’yancin tafiya tare da matar da muka aura mai bi kamar sauran manzanni da ’yan’uwan Ubangiji da kuma Kefas suke yi?
Maganganu a Karin Magana
- Wanda ya sami mata ya sami abu mai kyauK Mag 18:22
Ayoyin
K Mag 18:22Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
- Gara zama a kusurwar rufin gida da zama a gida da mace mai faɗaK Mag 21:9, K Mag 21:19
Ayoyin
K Mag 21:9Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
K Mag 21:19Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.