Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Buguwa

Rayuwar yau da kullum

Buguwa a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (30), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Maganganu

  • Ruwan inabi mai ba’a ne, barasa mai hayaniya ceK Mag 20:1
    Ayoyin
    K Mag 20:1Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne; duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.
  • Wa yake da jajayen idanu? Waɗanda suke daɗewa wajen ruwan inabiK Mag 23:29–35
    Ayoyin
    K Mag 23:29–35Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu? Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi. Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro! A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa. Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa. Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa. Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?”
  • Mashayi da mai zari za su talauceK Mag 23:20–21
    Ayoyin
    K Mag 23:20–21Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci, gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.
  • Bai dace sarakuna su sha ruwan inabi baK Mag 31:4–7
    Ayoyin
    K Mag 31:4–7“Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa, don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu. A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala; bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.
  • Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe suna neman barasaIsh 5:11–12
    Ayoyin
    Ish 5:11–12Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe don su nufi wurin shaye-shaye, waɗanda suke raba dare har sai sun bugu da ruwan inabi. Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
  • “jarumawa a shan ruwan inabi da gwanaye a haɗin abubuwan sha”Ish 5:22
    Ayoyin
    Ish 5:22Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi da gwanaye a haɗin abubuwan sha,
  • Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda barasaIsh 28:7–8
    Ayoyin
    Ish 28:7–8Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi suke jiri don sun sha barasa Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa sun kuma yi tatur da ruwan inabi; suna jiri saboda sun sha barasa, suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi, suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara. Duk amai ya rufe teburori kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.
  • “Gobe ma zai zama kamar yau, ko ma fiye da haka”Ish 56:12
    Ayoyin
    Ish 56:12Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi! Bari mu cika cikinmu da barasa! Gobe ma zai zama kamar yau, ko ma fiye da haka.”
  • Ruwan inabi yakan kawar da fahimtaHos 4:11
    Ayoyin
    Hos 4:11ga karuwanci, ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi, waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.
  • Shan ruwan inabi da kwanoniAmos 6:6
    Ayoyin
    Amos 6:6Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi kuna kuma shafa mai mafi kyau, amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.
  • Kaiton wanda yake sa maƙwabtansa su buguHab 2:15
    Ayoyin
    Hab 2:15“Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha, yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu, don dai yă ga tsiraicinsu.
  • Masu buguwa sukan bugu da dare1Tes 5:7
    Ayoyin
    1Tes 5:7Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.
  • Kada ku bugu da ruwan inabiAfi 5:18, Rom 13:13, Luk 21:34
    Ayoyin
    Afi 5:18Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.
    Rom 13:13Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba.
    Luk 21:34“Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.

A cikin Doka

  • Iyaye suna iya kai ƙarar ɗa gaban dattawa: “Mai zari ne, kuma mashayi”M Sh 21:20
    Ayoyin
    M Sh 21:20Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.”
  • Firistoci ba sa shan ruwan inabi sa’ad da suke shiga Tentin SujadaFir 10:9
    Ayoyin
    Fir 10:9“Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.
  • Banazare yakan guji ruwan inabi da barasaƘid 6:3
    Ayoyin
    Ƙid 6:3dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.

Misalai

  • Nuhu ya shuka gonar inabi ya kuma buguFar 9:20–21
    Ayoyin
    Far 9:20–21Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi. Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa.
  • ’Ya’yan Lot mata sun sa mahaifinsu ya buguFar 19:32–33
    Ayoyin
    Far 19:32–33Bari mu sa mahaifinmu yă sha ruwan inabi, sa’an nan sai mu kwana da shi, don kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” A wannan dare, suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, ’yar farin ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba.
  • Nabal, a bugu sosai a bikinsa, bai ji kome ba sai da safe1Sam 25:36–37
    Ayoyin
    1Sam 25:36–37Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye. Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse.
  • Dawuda ya sa Uriya ya bugu, amma Uriya bai tafi gida ba2Sam 11:13
    Ayoyin
    2Sam 11:13Dawuda ya gayyace shi, ya kuwa ci ya sha tare da shi, Dawuda ya sa ya bugu tilis. Amma da yamma Uriya ya koma ya kwanta a tabarmarsa cikin bayin maigidan sarki; bai je gida ba.
  • Absalom ya jira sai zuciyar Amnon ta yi daɗi da ruwan inabi2Sam 13:28
    Ayoyin
    2Sam 13:28Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.”
  • Zimri ya kashe Sarki Ela yayinda yake buguwa1Sar 16:9–10
    Ayoyin
    1Sar 16:9–10Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza. Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.
  • Ben-Hadad da sarakuna 32 suna sha a tentunansu da tsakar rana1Sar 20:16
    Ayoyin
    1Sar 20:16Suka fita da tsakar rana yayinda Ben-Hadad tare da sarakuna 32 masu goyon bayansa suke cikin tentunansu suna sha, suna buguwa.
  • Zerzes, da zuciyarsa ta yi daɗi da ruwan inabi, ya kira Sarauniya BashtiEsta 1:10–11
    Ayoyin
    Esta 1:10–11A rana ta bakwai, sa’ad da Sarki Zerzes, ya yi tilis da ruwan inabi, sai ya umarci bābānni bakwai waɗanda suke yin masa hidima, wato, Mehuman, Bizta, Harbona, Bigta, Abagta, Zetar da Karkas, su kawo Sarauniya Bashti a gabansa, sanye da rawanin sarautarta, don ta nuna kyanta wa mutane da kuma hakimai, gama ita kyakkyawa ce ƙwarai.
  • Belshazar ya sha daga kwanonin haikalin UrushalimaDan 5:1–4
    Ayoyin
    Dan 5:1–4Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su. Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.

Waɗanda aka zaci sun bugu

  • Eli ya zaci Hannatu, da take addu’a a zuci, ta bugu1Sam 1:13–15
    Ayoyin
    1Sam 1:13–15Hannatu tana addu’a a zuci, ba a jin muryarta, sai leɓunanta ne kawai suna motsi. Eli kuwa ya yi tsammani ta bugu ne. Sai ya ce mata, “Har yaushe za ki ci gaba da maye? Ki daina shan ruwan inabi.” Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne.
  • An kira Yesu “mai haɗama da kuma mashayi”Mat 11:19
    Ayoyin
    Mat 11:19Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”
  • A Fentekos: “Sun yi tatil da ruwan inabi ne”Ayy M 2:13–15
    Ayoyin
    Ayy M 2:13–15Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.” Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.