Rayuwar yau da kullum
Barci a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (34), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Maganganu
- Yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙaunaZab 127:2
Ayoyin
Zab 127:2Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
- “Zan kwanta in kuma yi barci lafiya”Zab 4:8, Zab 3:5
- Sa’ad da ka kwanta, barcinka zai yi daɗiK Mag 3:24
Ayoyin
K Mag 3:24sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
- Barcin ma’aikaci yana da daɗi; yalwar attajiri ba ta bar shi ya yi barci baM Had 5:12
Ayoyin
M Had 5:12Barcin ma’aikaci daɗi gare shi, ko yă ci kaɗan ko da yawa, amma yalwar mai arziki ba ta barinsa yă iya yin barci.
- Kada ka so barci, don kada ka talauceK Mag 20:13
Ayoyin
K Mag 20:13Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
- “Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa”K Mag 6:9–10, K Mag 24:33
Ayoyin
K Mag 6:9–10Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku? Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
K Mag 24:33Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
- Ragwanci kan jawo zurfin barciK Mag 19:15
Ayoyin
K Mag 19:15Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.
- Mai tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barciZab 121:4
Ayoyin
Zab 121:4tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.
- Iliya ya yi wa annabawan Ba’al ba’a: wataƙila yana barci1Sar 18:27
Ayoyin
1Sar 18:27Da tsakar rana, Iliya ya fara yin musu ba’a. Ya ce, “Ku yi ihu da ƙarfi, tabbatacce shi allah ne! Mai yiwuwa yana cikin zurfin tunani, ko dai aiki ya yi masa yawa, ko ya yi tafiya. Mai yiwuwa yana barci ne, dole a tashe shi.”
- Wa’adi: ba barci sai an sami mazauni domin UbangijiZab 132:3–5
Ayoyin
Zab 132:3–5“Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba, ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna, sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”
Misalai
- Adamu ya yi barci mai nauyiFar 2:21
Ayoyin
Far 2:21Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama.
- Abram ya yi barci mai nauyi yayinda rana take faɗuwaFar 15:12
Ayoyin
Far 15:12Yayinda rana tana fāɗuwa, sai Abram ya yi barci mai zurfi, sai wani duhu mai kauri mai kuma bantsoro ya rufe shi.
- Yaƙub ya yi barci da dutse a ƙarƙashin kansaFar 28:11
Ayoyin
Far 28:11Sa’ad da ya kai wani wuri, sai ya dakata domin yă kwana, gama rana ta riga ta fāɗi. Ya ɗauki dutse daga cikin duwatsun wurin, ya sa shi ya zama matashin kansa, sa’an nan ya kwanta don yă yi barci.
- Yaƙub: sanyi da dare, barci kuma ya ƙaurace wa idanunaFar 31:40
Ayoyin
Far 31:40Yanayin da na kasance ke nan, da rana na sha zafin rana da dare kuma na sha sanyi, ga rashin barci.
- Yayel ta kashe Sisera yayinda yake barci saboda gajiyaMah 4:21
Ayoyin
Mah 4:21Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu.
- Delila ta sa Samson ya yi barci a cinyartaMah 16:19
Ayoyin
Mah 16:19Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.
- Bowaz ya kwanta kusa da tarin hatsi; da tsakar dare ya sami RutRut 3:7–8
Ayoyin
Rut 3:7–8Sa’ad da Bowaz ya gama ci da sha yana kuma cikin farin ciki, sai ya tafi ya kwanta a ƙarshen tarin hatsi. Rut kuwa ta sulalle ta je ta buɗe ƙafafunsa ta kwanta. Da tsakar dare sai wani abu ya firgitar da mutumin, ya kuwa juya sai ya tarar da mace kwance a ƙafafunsa.
- Dawuda ya ɗauki māshi da tulun ruwa daga wurin Shawulu da yake barci1Sam 26:7, 1Sam 26:12
Ayoyin
1Sam 26:7Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.
1Sam 26:12Saboda haka Dawuda ya ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da Shawulu suka tafi. Ba wanda ya gan su, ba wanda ya san abin da ya faru, ba kuwa wanda ya farka, dukansu suna barci gama Ubangiji ya sa barci mai nauyi ya ɗauke su.
- An kashe Ish-Boshet a lokacin hutunsa na tsakar rana2Sam 4:5
Ayoyin
2Sam 4:5To, Rekab da Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana.
- Iliya ya yi barci a ƙarƙashin itacen tsintsiya1Sar 19:5
Ayoyin
1Sar 19:5Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci. Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.”
- Zerzes da ya rasa barci ya sa aka karanta masa littafin tarihiEsta 6:1
Ayoyin
Esta 6:1A daren nan, sarki bai iya barci ba, saboda haka ya ba da umarni a kawo, a kuma karanta masa littafin tarihi na shekara-shekara, da rubutaccen labarin mulkinsa.
- Mafarkan Nebukadnezzar: barci ya ƙaurace masaDan 2:1
Ayoyin
Dan 2:1A shekara ta biyu ta mulkinsa, Nebukadnezzar ya yi mafarkai; hankalinsa ya tashi har ya kāsa barci.
- Dariyus bai iya barci ba yayinda Daniyel yake tare da zakokiDan 6:18
Ayoyin
Dan 6:18Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.
- Yunana ya yi barci a cikin jirgi lokacin hadariYun 1:5
Ayoyin
Yun 1:5Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa.
- Yesu yana barci a kan katifa a bayan jirgi lokacin hadariMat 8:24, Mar 4:38, Luk 8:23
Ayoyin
Mat 8:24Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.
Mar 4:38Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?”
Luk 8:23Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.
- Almajirai sun yi barci a GetsemaneMat 26:40–43, Luk 22:45
Ayoyin
Mat 26:40–43Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba? Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.” Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.” Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci.
Luk 22:45Da ya tashi daga addu’a, ya koma inda almajiransa suke, sai ya iske su suna barci, daga gajiyar baƙin ciki.
- Bitrus yana barci a kurkuku tsakanin sojoji biyuAyy M 12:6
Ayoyin
Ayy M 12:6A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa.
- Yitikus ya yi gyangyaɗi yayinda Bulus yake magana, ya fāɗi daga tagaAyy M 20:9
Ayoyin
Ayy M 20:9Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Sa’ad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.