Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Haraji

Rayuwar yau da kullum

Haraji a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (35), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Kowanne da aka ƙidaya a ƙidayar jama’a yakan biya rabin shekelFit 30:11–16, Fit 38:26
    Ayoyin
    Fit 30:11–16Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su. Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji. Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji. Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku. Ku karɓi kuɗin kafara daga hannun Isra’ilawa, ku yi amfani da shi domin hidimar Tentin Sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar rayukansu.”
    Fit 38:26Duk mutumin da ya shiga ƙirge daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, ya ba da rabin shekel. Mazan da suka shiga ƙirge sun kai mutum 603,550.
  • Kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara domin gidan AllahNeh 10:32
    Ayoyin
    Neh 10:32“Mun ɗauka hakkin bin umarnai na ba da kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara don hidimar gidan Allahnmu.
  • Yusuf: kashi ɗaya bisa biyar na girbin Masar na Fir’auna neFar 41:34, Far 47:24
    Ayoyin
    Far 41:34Bari Fir’auna yă naɗa komishinoni a kan ƙasar don su karɓi kashi ɗaya bisa biyar na girbin Masar a lokacin shekaru bakwai na yalwar abinci.
    Far 47:24Amma sa’ad da hatsi suka nuna, za ku ba da kashi ɗaya bisa biyar ga Fir’auna. Sauran kashi huɗu bisa biyar kuma ku riƙe a matsayin iri don gonaki da kuma abinci wa kanku da gidajenku da kuma ’ya’yanku.”
  • Ƙasar firistocin Masar ne kaɗai ba ta Fir’auna baFar 47:26
    Ayoyin
    Far 47:26Ta haka Yusuf ya kafa wannan ya zama doka game da ƙasa a Masar, har yă zuwa yau cewa kashi ɗaya bisa biyar na amfani gona ya zama na Fir’auna. Gonakin firistoci ne kaɗai ba su zama na Fir’auna ba.
  • Wani sarkin Farisa ya ɗauke wa firistoci da masu hidimar haikali harajiEzr 7:24
    Ayoyin
    Ezr 7:24Ku kuma san cewa, ba ku da ikon sa firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofin haikali, da masu aiki a gidan Allah, ko waɗansu masu aiki a haikali su biya haraji, ko kuɗin shiga.
  • Iyalin wanda ya kashe Goliyat za a ɗauke musu haraji1Sam 17:25
    Ayoyin
    1Sam 17:25Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.”
  • Hutun haraji saboda liyafar EstaEsta 2:18
    Ayoyin
    Esta 2:18Sarki kuwa ya yi ƙasaitacciyar liyafa, liyafar Esta, wa dukan hakimansa da shugabannin masarautarsa. Ya yi shelar hutu ko’ina a larduna, ya kuma raba kyautai a yalwace irin na sarauta.
  • Zerzes ya sa haraji har zuwa tsibirai mafi nisaEsta 10:1
    Ayoyin
    Esta 10:1Sarki Zerzes ya sa a biya haraji a ko’ina a cikin daular, har zuwa ƙasashe masu nesa na bakin teku.

Sarakuna da haraji

  • Hakimai goma sha biyu na Solomon kowa yakan ciyar da fāda wata guda1Sar 4:7
    Ayoyin
    1Sar 4:7Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.
  • Tanajin Solomon na rana guda1Sar 4:22–23
    Ayoyin
    1Sar 4:22–23Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci, shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.
  • Aikin gandu domin gine-ginen Solomon1Sar 9:15
    Ayoyin
    1Sar 9:15Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer.
  • Adoniram shi ne shugaban aikin gandu2Sam 20:24, 1Sar 4:6
    Ayoyin
    2Sam 20:24Adoniram kuwa shi ne shugaban aikin gandu; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubucin tarihi;
    1Sar 4:6Ahishar, shi ne sarkin fada. Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu.
  • Isra’ila sun roƙi Rehobowam ya sauƙaƙa nauyin karkiya1Sar 12:4
    Ayoyin
    1Sar 12:4“Mahaifinka ya sa mana kaya mai nauyin gaske, amma yanzu ka sassauta wannan aiki mai zafi, da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
  • Isra’ila sun jajjefe Adoniram har ya mutu; Rehobowam ya tsere1Sar 12:18
    Ayoyin
    1Sar 12:18Sarki Rehobowam ya aiki Adoniram wanda yake shugaban aikin gandu, amma Isra’ila suka jajjefe shi da dutse har ya mutu. Sarki Rehobowam, ya sullale ya hau keken yaƙinsa ya tsere zuwa Urushalima.
  • Menahem ya ba Ful talenti dubu na azurfa2Sar 15:19–20
    Ayoyin
    2Sar 15:19–20Sai Ful sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar hari, Menahem kuwa ya ba shi talenti dubu na azurfa don yă sami goyon bayansa, yă kuma ƙarfafa kahuwa mulkin. Menahem ya tara kuɗin ne ta hanyar haraji a Isra’ila inda ya sa kowane attajiri ya ba da shekel hamsin don a ba sarkin Assuriya. Sa’an nan sarkin Assuriya ya janye, bai ƙara kasance a ƙasar ba.
  • Yehohiyakim ya sa wa ƙasar haraji don ya biya Fir’auna Neko2Sar 23:35
    Ayoyin
    2Sar 23:35Yehohiyakim ya riƙa biyan Fir’auna Neko azurfa da zinariyar da ya umarta. Don yă yi haka sai ya riƙa karɓar azurfa da zinariya daga mutanen ƙasar, kowa bisa ga ƙarfinsa.
  • Abokan gāba sun gargaɗi sarki: Urushalima za ta daina biyan harajiEzr 4:13, Ezr 4:20
    Ayoyin
    Ezr 4:13Ya kamata fa, sarki ya san cewa in aka sāke gina wannan birni duk da katangar birnin, mutanen birnin ba za su dinga biyan haraji, da kuɗin shiga, da na fitar da kaya ba, wannan zai sa aljihun masarauta yă bushe.
    Ezr 4:20Urushalima ta yi sarakuna masu iko sosai waɗanda suka yi mulkin Kewayen Kogin Yuferites gaba ɗaya, an kuma biya masu haraji, da kuɗin shiga da na fita na kaya.
  • Mutane sun ci bashin kuɗi don su biya harajin sarki a kan gonakinsuNeh 5:4
    Ayoyin
    Neh 5:4Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.
  • Harajin hatsi da ake karɓa daga matalautaAmos 5:11
    Ayoyin
    Amos 5:11Kuna matsa wa matalauta kuna sa su dole su ba ku hatsi. Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, ba za ku zauna a cikinsu ba; ko da yake kun nome gonaki masu kyau, ba za ku sha ruwan inabinsu ba.

A cikin Linjila

  • Kaisar Augustus ya umarta a ƙidaya mutanen dukan daularLuk 2:1–3
    Ayoyin
    Luk 2:1–3A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.) Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.
  • Harajin haikali: kuɗi a bakin kifiMat 17:24–27
    Ayoyin
    Mat 17:24–27Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?” Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?” Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan. Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”
  • “Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”Mat 22:17–21
    Ayoyin
    Mat 22:17–21To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?” Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari, sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?” Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
  • Yohanna ga masu karɓar haraji: “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa”Luk 3:12–13
    Ayoyin
    Luk 3:12–13Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?” Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”
  • An kira Lawi daga wurin karɓar harajiMar 2:14, Luk 5:27
    Ayoyin
    Mar 2:14Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi.
    Luk 5:27Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.”
  • Yesu ya ci abinci tare da masu karɓar haraji, Farisiyawa kuma suka yi ƙorafiMat 9:10–11, Mat 11:19
    Ayoyin
    Mat 9:10–11Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa. Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”
    Mat 11:19Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”
  • Misali: Bafarisiye da mai karɓar haraji a haikaliLuk 18:10–13
    Ayoyin
    Luk 18:10–13“Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’ “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’
  • Zakka, shugaban masu karɓar haraji, zai mayar da ninki huɗuLuk 19:2, Luk 19:8
    Ayoyin
    Luk 19:2Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma.
    Luk 19:8Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”
  • Bulus: ku biya haraji ga wanda ya kamaci harajiRom 13:6–7
    Ayoyin
    Rom 13:6–7Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci. Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.