Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Basussuka da rance

Rayuwar yau da kullum

Basussuka da rance a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (28), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Kada ku riƙe bashin kowa, sai dai bashin ƙaunar junaRom 13:8
    Ayoyin
    Rom 13:8Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.
  • Mai karɓar rance bawan mai ba da rance neK Mag 22:7
    Ayoyin
    K Mag 22:7Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.
  • Kada ka tsaya wa wani a kan bashi, don kada a ɗauke gadonkaK Mag 22:26–27, K Mag 11:15
    Ayoyin
    K Mag 22:26–27Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi; gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.
    K Mag 11:15Duk wanda ya ɗauki lamunin wani tabbatacce zai sha wahala, amma duk wanda ya ƙi ya sa hannu a ɗaukar lamuni ba ruwansa.
  • Ka tsaya wa maƙwabci? Tafi nan da nan ka ’yantar da kankaK Mag 6:1–5
    Ayoyin
    K Mag 6:1–5Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani, in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko, to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka! Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma. Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.

A cikin Doka

  • Ba karɓar ruwa daga matalauci ɗan ƙasa; daga baƙo an yardaFit 22:25, M Sh 23:19–20
    Ayoyin
    Fit 22:25“In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa.
    M Sh 23:19–20Kada ku nemi ɗan’uwanku yă biya bashin da kuka ba shi da ruwa, ko kuɗi, ko abinci, ko kowane irin abin da yana iya ba da ruwa. Za ku iya nemi ruwa a bashin da kuka ba baƙo, amma ba ɗan’uwanku mutumin Isra’ila ba, domin Ubangiji Allahnku yă sa muku albarka a kowane abin da kuka sa hannunku a kai, a ƙasar da kuke shiga ku ci gādonta.
  • Mayafin da aka karɓa jingina akan mayar da shi kafin faɗuwar ranaFit 22:26–27, M Sh 24:12–13
    Ayoyin
    Fit 22:26–27In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana, domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne.
    M Sh 24:12–13In matalauci ne, kada ku kwana da abin da zai bayar a matsayin jingina a wurinku. Ku mayar da rigarsa a fāɗuwar rana saboda yă sami abin rufuwa. Yin haka zai sa yă gode muku, za a kuma ɗauka wannan a matsayin aikin adalci da kuka yi a gaban Ubangiji Allahnku.
  • Mai ba da rance yakan jira a waje a fito masa da jinginarM Sh 24:10–11
    Ayoyin
    M Sh 24:10–11Sa’ad da kuka ba da rance na kowane iri ga maƙwabcinku, kada ku shiga gidansa don karɓar wani abu a matsayin jingina. Ku tsaya a waje ku bar mutumin da yake karɓan rancen yă kawo muku abin da zai bayar a matsayin jingina.
  • Ba a karɓar duwatsun niƙa jinginaM Sh 24:6
    Ayoyin
    M Sh 24:6Kada ku karɓi jinginar dutsen niƙa tare da ɗan dutsen niƙan, domin yin haka zai zama karɓar jinginar rai ne.
  • Akan yafe basussuka kowace shekara ta bakwaiM Sh 15:1–3
    Ayoyin
    M Sh 15:1–3A ƙarshen kowace shekara ta bakwai, dole ku yafe basusuwan da kuke bi. Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi. Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa.
  • Ɗan ƙasa da ya sayar da kansa yakan yi aiki kamar ɗan ƙodagoFir 25:39–41
    Ayoyin
    Fir 25:39–41“ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa. Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna. Sa’an nan a sake shi da ’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa.
  • Dabbar aro da ta mutu dole a biya ta gaba ɗayaFit 22:14
    Ayoyin
    Fit 22:14“In mutum ya yi aron dabba daga wurin maƙwabcinsa, sai dabbar ta ji rauni ko ta mutu, yayinda mai shi ba ya nan, dole wanda ya yi aron dabbar yă biya.

Misalai

  • Yahuda ya bar hatiminsa, igiyarsa da sandansa jinginaFar 38:17–18
    Ayoyin
    Far 38:17–18Ya ce, “Zan aika miki da ɗan akuya daga garkena.” Sai ta ce, “Za ka ba ni wani abu jingina, kafin ka aika da shi?” Ya ce, “Wace jingina zan ba ki?” Sai ta amsa, “Hatiminka da ka rataye a wuya da kuma sandan da yake a hannunka.” Ya ba da su gare ta, ya kuma kwana da ita, sai ta yi ciki.
  • Dukan masu bashi sun taru wajen Dawuda1Sam 22:2
    Ayoyin
    1Sam 22:2Dukan mutanen da suke cikin wahala, da waɗanda ake binsu bashi, da masu damuwoyi, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Yawansu ya kai ɗari huɗu.
  • Mai bin bashi ya zo don ya ɗauki ’ya’ya maza biyu na gwauruwa bayi2Sar 4:1–7
    Ayoyin
    2Sar 4:1–7Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.” Elisha ya amsa mata ya ce, “Me kike so in yi miki? Ki faɗa mini, me kike da shi a gidanki?” Sai ta ce, “Baiwarka ba ta da kome a can, sai ɗan tulun man zaitun.” Elisha ya ce, “Ki je wurin dukan maƙwabtanki, ki nemi tulunan da babu kome a ciki. Kada ki nemo kaɗan kawai. Sa’an nan ki shiga ciki, ki kulle ƙofar da ke da ’ya’yanki kuke ciki. Ku ɗuɗɗura man a dukan tulunan, sa’ad da kowanne ya cika, sai ki ajiye a gefe.” Ta tashi ta shiga tare da ’ya’yanta maza, suka kulle ƙofa. ’Ya’yanta suka kawo mata tuluna, ita kuma tana ɗurawa. Da dukan tulunan suka cika, sai ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tulu.” Amma ya amsa ya ce, “Ai, ba saura.” Sa’an nan man ya daina zuba. Sai ta tafi ta faɗa wa mutumin Allah. Shi kuwa ya ce mata, “Tafi, ki sayar da man, ki biya bashinki. Ki biya bukatanki da na ’ya’yanki da sauran da ya rage.”
  • “kayan aro ne fa!” — kan gatari ya fāɗi cikin Urdun2Sar 6:4–6
    Ayoyin
    2Sar 6:4–6Ya kuma tafi tare da su. Suka tafi Urdun suka fara saran itatuwa. Yayinda ɗayansu yake cikin saran itace, sai kan gatarin ya fāɗi a ruwa, sai ya ce, “Kash, ranka yă daɗe, kayan aro ne fa!” Sai mutumin Allah ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?” Da ya nuna masa wurin, sai Elisha ya yanka ɗan sanda ya jefa a wurin, ya sa kan gatarin ya taso sama.
  • Yunwa: mutane sun jinginar da gonaki da gidaje; Nehemiya ya hana cin ruwaNeh 5:3–5, Neh 5:10–12
    Ayoyin
    Neh 5:3–5Waɗansu kuwa suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.” Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu. Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa ’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin ’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”
    Neh 5:10–12Ni ma da ’yan’uwana da kuma mutanena muna ba wa mutane bashin kuɗi da kuma hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa! Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.” Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.” Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari.
  • An ƙwace jaririn iyali matalauta saboda bashiAyu 24:9
    Ayoyin
    Ayu 24:9Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.
  • Tufafin da aka karɓa jinginaAyu 22:6, Amos 2:8
    Ayoyin
    Ayu 22:6Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili; ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.
    Amos 2:8Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade a kan tufafin da suka karɓe jingina. A gidajen allolinsu sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.
  • Misali: bawa mai bashin talenti dubu gomaMat 18:23–34
    Ayoyin
    Mat 18:23–34“Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa. Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma. Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin. “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’ Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi. “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’ “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’ “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin. Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru. “Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni. Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’ Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa.
  • Misali: masu bashi biyu, dinari ɗari biyar da hamsinLuk 7:41–42
    Ayoyin
    Luk 7:41–42Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. Dukan biyun suka gagara biyansa, sai ya yafe musu. To, a ganinka, wa zai fi ƙaunar mutumin nan?”
  • Ka shirya da abokin gābanka tun kuna kan hanyar zuwa kotuMat 5:25–26
    Ayoyin
    Mat 5:25–26“Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku. Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.
  • Ku ba da rance ba tare da sa ran samun kome baLuk 6:34–35
    Ayoyin
    Luk 6:34–35In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyan ka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma, suna ba da bashi ga masu zunubi, da fata za a biya su tsab. Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.
  • Bulus ga Filemon: “sai ka mai da shi a kaina … Zan biya ka”Flm 1:18–19
    Ayoyin
    Flm 1:18–19In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina. Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.