Bincika › Jigogi › Tebur da abinci
Rayuwar yau da kullum
Tebur da abinci a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (36), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Tebur
- Gado, tebur, kujera da fitila a ƙaramin ɗakin Elisha2Sar 4:10
Ayoyin
2Sar 4:10Bari mu yi ɗan ɗaki a rufin gida mu kuma sa masa gado da tebur da kujera da kuma fitila. Saboda a duk lokacin da ya zo wurinmu, sai yă sauka a can.”
- Sarakuna saba’in sun yi kalan abinci a ƙarƙashin teburin Adoni-BezekMah 1:7
Ayoyin
Mah 1:7Sa’an nan Adoni-Bezek ya ce, “Sarakuna saba’in waɗanda aka yayyanka manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, sun yi kalan abinci a ƙarƙashin teburina. Ga shi yanzu Allah ya rama abin da na yi musu.” Suka zo da shi Urushalima, a can kuwa ya mutu.
- Teburin tabanakul: itacen ƙirya da aka dalaye da zinariya, da sandunan ɗaukaFit 25:23–28
Ayoyin
Fit 25:23–28“Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya. Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya. Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke. Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin. Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin.
- Burodi goma sha biyu a jeri biyu a kan teburin zinariya kowane AsabbaciFir 24:5–8
Ayoyin
Fir 24:5–8“Ɗauki gari mai laushi a gasa dunƙulen burodi goma sha biyu, a yi amfani da humushi biyu na garwan gari don kowace burodi. A shirya su jeri biyu, guda shida a kowane jeri a kan teburin da aka yi da zinariya zalla, a gaban Ubangiji. Za a zuba turare a kowane layin dunƙulen burodin don yă kasance abin tunawa a bisa burodin. Turaren zai ƙone a madadin burodin don yă zama kamar hadayar da aka miƙa da wuta ga Ubangiji. Za a shirya wannan gurasa a gaban Ubangiji kowane Asabbaci, a madadin Isra’ilawa a matsayin madawwamin alkawari.
- Teburan zinariya da teburan azurfa domin haikali1Tar 28:16
Ayoyin
1Tar 28:16yawan zinariya don kowane tebur saboda burodi mai tsaki; da kuma yawan azurfa saboda teburin azurfa;
- Yesu ya birkice teburan masu canjin kuɗiYoh 2:15
Ayoyin
Yoh 2:15Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu.
- Karnuka a ƙarƙashin tebur sukan ci gutsattsarin abincin yaraMat 15:27, Mar 7:28
- Lazarus yana marmarin gutsattsari daga teburin attajiri (misali)Luk 16:21
Ayoyin
Luk 16:21Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.
- ’Ya’yanka maza kamar tohon zaitun kewaye da teburinkaZab 128:3
Ayoyin
Zab 128:3Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.
Zama da kishingiɗa
- Ibrahim ya tsaya kusa da baƙinsa a ƙarƙashin itace yayinda suke ciFar 18:8
Ayoyin
Far 18:8Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.
- Rut ta zauna kusa da masu girbi lokacin cin abinciRut 2:14
Ayoyin
Rut 2:14A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.
- Haman ya fāɗi a kan kujerar da Sarauniya Esta take kishingiɗeEsta 7:8
Ayoyin
Esta 7:8Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sarki ya tā da murya da ƙarfi ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya yayinda take tare da ni a cikin gida?” Sarki bai ma rufe baki ba, sai bayin sarki suka rufe fuskar Haman.
- Yesu ya kishingiɗa a tebur tare da Sha BiyunMat 26:20
Ayoyin
Mat 26:20Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.
- Wani almajiri da yake kishingiɗe kusa da Yesu ya jingina baya ya tambaye shiYoh 13:23–25
Ayoyin
Yoh 13:23–25Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi. Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?” Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?”
- Wani Bafarisiye ya gayyaci Yesu cin abinci, ya kuma kishingiɗa a teburLuk 7:36
Ayoyin
Luk 7:36To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur.
- Marta tana hidima, Lazarus kuma yana kishingiɗe a tebur tare da YesuYoh 12:2
Ayoyin
Yoh 12:2A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi.
- Mutum dubu biyar sun zauna a kan ciyawa ƙungiya-ƙungiya na ɗari-ɗari da hamsin-hamsinMar 6:39–40, Luk 9:14
Ayoyin
Mar 6:39–40Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin.
Luk 9:14Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar. Amma ya ce wa almajiransa, “Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin.”
Wa ya ci tare da wa
- Dawuda bai zo teburin Shawulu ba; Yonatan ya tashi daga tebur cikin fushi1Sam 20:29, 1Sam 20:34
Ayoyin
1Sam 20:29Ya ce, ‘Bari in tafi gama iyalinmu suna miƙa hadaya a gari, ’yan’uwana kuwa sun gayyace ni in kasance a can. In na sami yardarka, bari in tafi in ga ’yan’uwana.’ Dalilin ke nan da bai zo ci da sarki ba.”
1Sam 20:34Yonatan ya tashi daga tebur cin abincin da fushi. A rana ta biyun kuwa bai ci abinci ba, gama yana baƙin ciki game da rashin kunyar mahaifinsa game da Dawuda.
- Hakimai sukan tanada abinci domin dukan masu zuwa teburin Solomon1Sar 4:27
Ayoyin
1Sar 4:27Shugabannin yankuna, kowanne a watansa yakan yi tanajin abinci domin Sarki Solomon da kuma duk wanda ya zo teburin sarki. Sun tabbatar ba a rasa kome ba.
- Teburin Solomon da zaman bayinsa sun ba sarauniyar Sheba mamaki1Sar 10:4–5
Ayoyin
1Sar 10:4–5Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina. Da irin abincin da yake kan teburinsa, da irin zaman fadawansa, da irin rigunan masu hidimarsa, da irin masu shayarwarsa, da kuma hadayun ƙonawar da yake yi a haikalin Ubangiji, sai ta yi mamaki ƙwarai.
- Yahudawa da shugabanni da yawa suna ci a teburin Nehemiya, ban da baƙiNeh 5:17
Ayoyin
Neh 5:17Bugu da ƙari, Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin suna ci daga teburina, haka ma waɗanda suka zo wurinmu daga ƙasashen da suke kewaye.
- Yehohiyacin yakan ci abinci a teburin sarkin Babilon dukan ransa2Sar 25:29
Ayoyin
2Sar 25:29Don haka Yehohiyacin ya tuɓe kayan fursuna. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har iyakar ransa.
- Yesu ya ci abinci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi a gidan MattiyuMat 9:10–11, Mar 2:15–16, Luk 15:2
Ayoyin
Mat 9:10–11Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa. Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”
Mar 2:15–16Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Lawi, sai masu karɓar haraji da “masu zunubi” da yawa, suka zo suka ci tare da shi da almajiransa, gama akwai mutane da yawa da suka bi shi. Da malaman dokoki, waɗanda su ma Farisiyawa ne, suka ga yana ci tare da masu “zunubi” da masu karɓar haraji, sai suka tambayi almajiransa, suka ce, “Me ya sa yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”
Luk 15:2Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.”
- “hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni”Luk 22:21
Ayoyin
Luk 22:21Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni.
- Yesu da ya tashi: “Ku zo ku karya kumallo”Yoh 21:12
Ayoyin
Yoh 21:12Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne.
- Masu bi na farko sukan gutsuttsura burodi gida-gidaAyy M 2:46
Ayoyin
Ayy M 2:46Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya,
- Sha Biyun ba sa so su bar wa’azi don su yi hidimar abinciAyy M 6:2
Ayoyin
Ayy M 6:2Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba.
- An zargi Bitrus da cin abinci tare da marasa kaciyaAyy M 11:3
Ayoyin
Ayy M 11:3suka ce, “Ka je gidan mutanen da suke marasa kaciya ka kuwa ci tare da su.”
- A Antiyok Bitrus ya ja da baya daga cin abinci tare da Al’ummaiGal 2:12
Ayoyin
Gal 2:12Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya.
- Mai gadin kurkuku ya ba Bulus da Sila abinciAyy M 16:34
Ayoyin
Ayy M 16:34Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don yă gaskata da Allah, shi da dukan iyalinsa.
- Marar bi ya gayyace ka? Ka ci duk abin da aka sa a gabanka1Kor 10:27
Ayoyin
1Kor 10:27In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.