Rayuwar yau da kullum
Wasiƙu a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (38), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Sarakuna da ma’aikata
- Dawuda ya aiki Uriya da wasiƙar da ta umarta a kashe shi2Sam 11:14–15
Ayoyin
2Sam 11:14–15Da safe Dawuda ya rubuta wa Yowab wasiƙa ya ba wa Uriya. A ciki wasiƙar ya rubuta, “Tura Uriya a gaba inda yaƙi ya fi zafi. Sa’an nan ka janye daga gare shi don a buge shi yă mutu.”
- Yezebel ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab, ta hatimce su da hatiminsa1Sar 21:8–11
Ayoyin
1Sar 21:8–11Sai ta rubuta wasiƙu a sunan Ahab, ta buga hatiminsa a kansu, sa’an nan ta aika su ga dattawa da manyan gari waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake. Cikin waɗannan wasiƙu ta rubuta, “Ku yi shelar ranar azumi, ku zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane. Amma ku zaunar da waɗansu ’yan iska biyu ɗaura da shi, ku sa su ba da shaida cewa ya zagi Allah da sarki. Sa’an nan ku ɗauke shi ku jajjefe shi da dutse sai ya mutu.” Sai dattawa da manyan gari, waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake, suka yi kamar yadda Yezebel ta umarta a cikin wasiƙun da ta rubuta.
- Sarkin Aram ya aiki Na’aman da wasiƙa2Sar 5:5–7
Ayoyin
2Sar 5:5–7Sarkin Aram ya ce, “Ko ta ƙaƙa, ka tafi, zan aika da wasiƙa ga sarkin Isra’ila.” Sai Na’aman ya tashi, ɗauke da talenti goma na azurfa, shekel dubu shida na zinariya, da tufafi kashi goma. Wasiƙar da ya kai wa sarkin Isra’ila ta ce, “Da wannan wasiƙa ina aika Na’aman gare ka don ka warkar da kuturtarsa.” Da sarkin Isra’ila ya karanta wasiƙar, sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne? Zan iya ɗauke rai ko in mai da shi? Me ya sa wannan mutum ya turo mini wannan mutum in warkar da kuturtarsa? Dubi fa yadda yake nemana da faɗa!”
- Yehu ya rubuta wa masu renon ’ya’ya maza saba’in na Ahab2Sar 10:1–7
Ayoyin
2Sar 10:1–7To, akwai ’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da ’ya’yan Ahab. Ya ce, “Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake ’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai, sai ku zaɓi mafi cancanta a cikin ’ya’yan maigidanku ku sa shi a kan kursiyin mahaifinsa. Sa’an nan ku yi yaƙi don gidan maigidanku.” Amma suka razana suka ce, “Idan sarakuna biyu ba su iya yin tsayayya da shi ba, wane mu?” Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da ’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.” Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan ’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To, ’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su. Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.
- Hezekiya ya shimfiɗa wasiƙar sarkin Assuriya a gaban Ubangiji2Sar 19:14, Ish 37:14
Ayoyin
2Sar 19:14Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji.
Ish 37:14Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji.
- Sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu da kyauta2Sar 20:12, Ish 39:1
Ayoyin
2Sar 20:12A wannan lokaci, Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu tare da kyauta, domin ya sami labarin rashin lafiyar Hezekiya.
Ish 39:1A wannan lokaci Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu da kuma kyauta, domin ya ji rashin lafiyarsa da kuma warkarwarsa.
- Wasiƙa daga Iliya ta zo wa Sarki Yehoram2Tar 21:12
Ayoyin
2Tar 21:12Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba.
- ’Yan aike sun kai gayyatar Hezekiya ta Bikin Ƙetarewa ko’ina a Isra’ila2Tar 30:1, 2Tar 30:6
Ayoyin
2Tar 30:1Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
2Tar 30:6Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.
- Wasiƙa a kan Urushalima, da aka rubuta da Arameyik, zuwa ga ArtazerzesEzr 4:7–8, Ezr 4:11
Ayoyin
Ezr 4:7–8A zamanin Artazerzes sarkin Farisa kuma, sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da sauran abokansu suka rubuta wasiƙa zuwa ga Artazerzes. Aka rubuta wasiƙar da harufan Arameyik, aka kuma fassara ta a yaren Arameyik. Rehum shugaban rundunar soja, da Shimshai marubuci, suka rubuta wasiƙar a kan Urushalima zuwa ga sarki Artazerzes, suka ce.
Ezr 4:11(Ga abin da suka rubuta.) Zuwa ga sarki Artazerzes. Daga bayinka, mutanen Kewayen Kogin Yuferites.
- Rahoton Gwamna Tattenai ga Sarki DariyusEzr 5:6–7
Ayoyin
Ezr 5:6–7Ga wasiƙar da Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu masu riƙe da muƙamai a Kewayen Kogin Yuferites suka aika wa Sarki Dariyus. Ga rahoton da suka aika masa. Zuwa ga Sarki Dariyus. Gaisuwa da fatan alheri.
- Nehemiya ya roƙi wasiƙun izinin wucewa da na katakoNeh 2:7–9
Ayoyin
Neh 2:7–9Na kuma ce masa, “In ya gamshi sarki, zai yi kyau in sami wasiƙu zuwa ga gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, domin su tanada kāriya har sai na isa Yahuda? A kuma ba ni wasiƙa zuwa ga Asaf, sarkin daji, yă ba ni katako don yin ƙofofin kagara na kusa da fadar haikali da kuma don katangar birni, da na wurin da zan zauna?” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni. Saboda haka na tafi wurin gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, na ba su wasiƙun sarki. Sarki kuma ya aika da hafsoshin mayaƙa da kuma mahayan dawakai tare da ni.
- Sanballat ya aika wa Nehemiya wasiƙa wadda ba a hatimce baNeh 6:5–7
Ayoyin
Neh 6:5–7Sai sau na biya, Sanballat ya aiki mataimakinsa gare ni da irin saƙo guda, kuma a hannunsa akwai wasiƙar da ba a yimƙe ba wadda aka rubuta cewa, “An ba da labari cikin al’ummai, kuma Geshem ya ce gaskiya ne, cewa kai da Yahudawa kun shirya tawaye, saboda haka kuke sāke ginin katangar. Ban da haka ma, bisa ga waɗannan rahotanni kana shirin zaman sarkinsu har ma ka naɗa annabawa su yi wannan shela game da kai a Urushalima, su ce, ‘Akwai sarki a Yahuda!’ To, wannan rahoto zai koma wurin sarki; saboda haka ka zo, mu tattauna wannan batu.”
- ’Yan aike sun kai wasiƙun Haman zuwa kowane lardiEsta 3:13
Ayoyin
Esta 3:13Aka aika ’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu.
- Mordekai ya hatimce wasiƙu da zoben sarki; ’yan aike sun hau dawakai masu sauriEsta 8:10
Ayoyin
Esta 8:10Mordekai ya yi rubutu da sunan Sarki Zerzes, ya hatimce saƙonin da zoben hatimin sarki, ya kuma aika da su ta hannun masu ’yan aika a kan dawakai, waɗanda sukan hau dawakai masu gudu sosai, da aka yi kiwonsu musamman saboda sarki.
- Wasiƙun Mordekai game da Furim zuwa ga Yahudawa na kusa da na nesaEsta 9:20
Ayoyin
Esta 9:20Sai Mordekai ya rubuta waɗannan abubuwa, ya kuma aika wasiƙu ga dukan Yahudawa ko’ina a lardunan Sarki Zerzes, na kusa da na nesa.
- Wasiƙar Irmiya ga waɗanda aka kai bauta a BabilonIrm 29:1
Ayoyin
Irm 29:1Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.
- Kwamanda Kalaudiyus Lisiyas ya rubuta wa Gwamna FelisAyy M 23:25–30
Ayoyin
Ayy M 23:25–30Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka, Kalaudiyus Lisiyas. Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis. Gaisuwa. Yahudawa sun kama wannan mutum suna kuma dab da kashe shi, amma na zo da sojojina na ƙwato shi, saboda na ji shi ɗan ƙasar Roma ne. Na so in san abin da ya sa suke zarginsa, saboda haka na kawo shi a gaban Majalisarsu. Na tarar cewa zargin da ake masa ya shafi waɗansu abubuwan da suka shafi dokarsu ne, amma ba wani zargi a kansa da ya isa kisa ko a daure shi. Sa’ad da na sami labari cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, sai na aika shi wurinka nan da nan. Na kuma umarci masu zarginsa su kai ƙararsu gare ka.
A ikkilisiyar farko
- Luka ya rubuta labari bi da bi domin TiyofilusLuk 1:3, Ayy M 1:1
- Shawulu ya roƙi wasiƙu zuwa majami’un DamaskusAyy M 9:2
Ayoyin
Ayy M 9:2ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majami’un Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yă kama su a matsayin ’yan kurkuku yă kai Urushalima.
- An karanta wasiƙar taron Urushalima a AntiyokAyy M 15:23, Ayy M 15:30
Ayoyin
Ayy M 15:23Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa.
Ayy M 15:30Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar.
- ’Yan’uwa sun rubuta don a karɓi Afollos a AkayyaAyy M 18:27
Ayoyin
Ayy M 18:27Sa’ad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai ’yan’uwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata.
- Shugabannin Yahudawa na Roma: “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba”Ayy M 28:21
Ayoyin
Ayy M 28:21Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai.
- Tertiyus ne ya rubuta wasiƙa zuwa ga RomawaRom 16:22
Ayoyin
Rom 16:22Ni, Tertiyus, wanda ya rubuta wannan wasiƙa, ina gai da ku cikin Ubangiji.
- Bulus ya ambaci wata wasiƙar farko zuwa Korint1Kor 5:9
Ayoyin
1Kor 5:9Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata.
- Wasiƙun shaida2Kor 3:1
Ayoyin
2Kor 3:1Yabon kanmu ne kuma muka fara yi? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi?
- “Ku dubi irin manya-manyan harufan … da hannuna!”Gal 6:11
Ayoyin
Gal 6:11Ku dubi irin manya-manyan harufan da na yi amfani da su yayinda nake rubuta muku da hannuna!
- Gaisuwa da hannun Bulus kansa alama ce a kowace wasiƙa2Tes 3:17
Ayoyin
2Tes 3:17Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.
- Ku yi hankali da wasiƙar “da an ce daga wurinmu ne”2Tes 2:2
Ayoyin
2Tes 2:2kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo.
- Kolossi da Lawodiseya za su musanya wasiƙuKol 4:16
Ayoyin
Kol 4:16Bayan an karanta muku wannan wasiƙa, ku tabbata an karanta ta kuma a ikkilisiyar Lawodiseyawa; ku ma ku karanta wasiƙar da ta zo daga Lawodiseya.
- Bulus ya rubuta wa Filemon game da OnesimusFlm 1:1, Flm 1:10
- Bitrus: waɗansu sassan wasiƙun Bulus suna da wuyan ganewa2Bit 3:16
Ayoyin
2Bit 3:16Haka yake rubutu cikin dukan wasiƙunsa, yana magana a cikinsu a kan waɗannan al’amura. Wasiƙunsa sun ƙunshi waɗansu abubuwa masu wuyar fahimta, waɗanda jahilai da kuma waɗanda ba tsayayyu ba ne suke murɗe ma’anarsu, kamar yadda suke yi da sauran Nassosi, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.