Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Gādo da wasiyya

Rayuwar yau da kullum

Gādo da wasiyya a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (39), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Misalai

  • Abram marar ɗa: wani bawa, Eliyezer na Damaskus, shi zai gāje niFar 15:2–3
    Ayoyin
    Far 15:2–3Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?” Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.”
  • Saratu: ɗan baiwa ba zai yi rabon gādon Ishaku baFar 21:10
    Ayoyin
    Far 21:10sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.”
  • Ibrahim ya bar wa Ishaku kome ya kuma sallami ’ya’yan ƙwaraƙwaransa da kyautaiFar 24:36, Far 25:5–6
    Ayoyin
    Far 24:36Saratu matar maigidana ta haifa masa ɗa a tsufanta, ya kuma ba shi duk mallakarsa.
    Far 25:5–6Ibrahim ya bar wa Ishaku kome da ya mallaka. Amma yayinda Ibrahim yake da rai, ya ba wa ’ya’yan ƙwarƙwaransa maza kyautai, ya kuma sallame su daga ɗansa Ishaku zuwa ƙasashen gabas.
  • Rahila da Liyatu: “Muna da wani rabo a gādon kayan mahaifinmu ne?”Far 31:14–16
    Ayoyin
    Far 31:14–16Sai Rahila da Liyatu suka amsa suka ce, “Muna da wani rabo a gādon kayan mahaifinmu ne? Ba kamar baƙi ne yake ɗaukarmu ba? Ba sayar da mu kaɗai ya yi ba, har ma ya yi amfani da abin da aka biya saboda mu. Tabbatacce dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga mahaifinmu ya zama namu da ’ya’yanmu. Saboda haka ka yi duk abin da Allah ya faɗa maka.”
  • Yaƙub ya ba Yusuf gona fiye da ’yan’uwansaFar 48:21–22
    Ayoyin
    Far 48:21–22Sa’an nan Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ina gab da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku Kuma gare ka, a matsayi wanda yake kan ’yan’uwanka, na ba da gonar da na karɓe daga Amoriyawa da takobi da kuma bakana.”
  • Hakkin ɗan fari na Ruben ya koma ga ’ya’yan Yusuf maza1Tar 5:1–2
    Ayoyin
    1Tar 5:1–2’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila (shi ne ɗan fari, amma sa’ad da ya ƙazantar da gadon auren mahaifinsa, sai aka ba wa ’yancin ɗan farinsa wa ’ya’yan Yusuf maza ɗan Isra’ila; don kada a lissafta shi a tarihin zuriya bisa ga matsayin haihuwarsa, ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin ’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi, ’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne),
  • ’Ya’yan Zelofehad mata sun sami ƙasa a cikin ’yan’uwan mahaifinsuƘid 27:1–4, Yosh 17:3–4
    Ayoyin
    Ƙid 27:1–4’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza. Da suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada, sai suka tsaya a gaban Musa, Eleyazar firist, shugabannin da sauran taro, suka ce, “Mahaifinmu ya mutu a hamada. Ba ya cikin mabiyan Kora waɗanda suka taru suka tayar wa Ubangiji, amma ya mutu ne saboda zunubinsa, bai kuma bar ’ya’ya maza ba. Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace a kabilarsa don kawai ba shi da ɗa? Ka ba mu gādo cikin ’yan’uwan mahaifinmu.”
    Yosh 17:3–4Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse ba shi da ’ya’ya maza, sai dai mata. Ga sunayensu, Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza. Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “ Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji.
  • An hana Yefta gādo domin shi ɗan wata mace neMah 11:2
    Ayoyin
    Mah 11:2Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.”
  • Bowaz ya sayi ƙasar Elimelek don a riƙe sunan mamacinRut 4:5–6, Rut 4:9–10
    Ayoyin
    Rut 4:5–6Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.” Da jin haka, sai dangin nan mai fansa ya ce, “To, ba zan iya fanshe shi ba don kada in yi wa nawa mallakar rauni. Za ka iya fanshe shi wa kanka. Ni dai ba zan iya ba.”
    Rut 4:9–10Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon. Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!”
  • Nabot ba zai sayar da gādon kakanninsa ba1Sar 21:2–3
    Ayoyin
    1Sar 21:2–3Sai Ahab ya ce wa Nabot, “Ka ba ni gonar inabinka in yi amfani da ita don kayan lambu, da yake tana kusa da fadana. Zan ba ka wata gonar inabin da ta fi wannan, ko kuma in ka gwammace, sai in biya ka duk abin da ya dace da ita.” Amma Nabot ya amsa wa Ahab ya ce, “ Ubangiji yă sawwaƙe in ba ka gādon kakannina.”
  • Yehoshafat ya ba ’ya’yansa maza kyautai da birane, mulkin kuma ga ɗan fari2Tar 21:3
    Ayoyin
    2Tar 21:3Mahaifinsu ya ba su kyautai masu yawa na azurfa da zinariya da kayayyaki masu daraja, tare da birane masu katanga a Yahuda, amma ya ba da mulki ga Yehoram domin shi ne ɗan farinsa.
  • Ayuba ya ba ’ya’yansa mata gādo tare da ’yan’uwansu mazaAyu 42:15
    Ayoyin
    Ayu 42:15Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza.
  • Irmiya ya sayi gonar ɗan kawunsa bisa ga hakkin fansaIrm 32:7–8
    Ayoyin
    Irm 32:7–8Hananel ɗan Shallum ɗan’uwan mahaifinka zai zo wurinka ya ce, ‘Saya filina a Anatot, domin a matsayinka na dangi na kurkusa hakkinka ne kuma kai ya wajaba ka saye shi.’ “Sa’an nan, kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa, sai ga Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina ya zo wurina a sansanin matsara ya ce, ‘Saya filina a Anatot a yankin Benyamin. Da yake hakkinka ne ka fanshe shi ka kuma mallake shi, ka sayo shi wa kanka.’ “Sai na gane cewa wannan maganar Ubangiji ce;
  • “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni”Luk 12:13
    Ayoyin
    Luk 12:13Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.”
  • Ƙaramin ɗa ya roƙi rabonsa na dukiya (misali)Luk 15:12–13
    Ayoyin
    Luk 15:12–13Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa. “Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza.
  • Manoman haya sun yi shirin kashe magājin su ƙwace gādon (misali)Mar 12:7
    Ayoyin
    Mar 12:7“Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’

A cikin Doka

  • In babu ɗa: ga ’ya mace, sa’an nan ’yan’uwa, kawuna, dangi mafi kusaƘid 27:8–11
    Ayoyin
    Ƙid 27:8–11“Ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘In wani ya mutu ba shi da ɗa, a ba da gādonsa ga ’yarsa. In ba shi da diya, sai a ba wa ’yan’uwansa gādonsa. In ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga ’yan’uwan mahaifinsa. In mahaifinsa ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga danginsa na kusa, a kabilarsa don yă mallaka. Wannan ya zama ƙa’ida wa Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarci Musa.’ ”
  • Ɗan fari na matar da ba a ƙauna har yanzu yakan sami rabo biyuM Sh 21:15–17
    Ayoyin
    M Sh 21:15–17In mutum yana da mata biyu, yana kuwa ƙaunar ɗaya, ba ya kuma ƙaunar ɗayan, su biyun kuwa suka haifi masa ’ya’ya maza, sai ya zamana cewa ɗan farin ya kasance na wadda ba ya ƙauna, to, a ranar da zai yi faɗa wane ne a cikin ’ya’yansa zai riƙe gādon da zai bar musu, kada yă sa ɗan matar da yake ƙauna yă zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan matar da ba ya ƙauna, wanda shi ne ɗan farin. Dole yă yarda cewa ɗan matar da ba ya ƙaunar ne ɗan fari, ta wurin ba shi rabo kashi biyu na dukan abin da yake da shi, gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.
  • Kada ƙasar gādo ta koma daga kabila zuwa kabilaƘid 36:7–9
    Ayoyin
    Ƙid 36:7–9Ba gādon Isra’ilan da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowane mutumin Isra’ila zai riƙe gādonsa na kabilar da ya gāda daga kakanninsa. Kowace ’ya wadda ta ci gādon ƙasa, a kowace kabilar Isra’ilawa, dole tă auri wani cikin kabilar kakanninta, saboda kowane mutumin Isra’ila yă mallaki gādon kakanninsa. Ba gādon da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowace kabilar Isra’ilawa za tă riƙe mallaka da ta gāda.”
  • Akan raba ƙasar da ƙuri’a, mafi yawa ga manyan kabiluƘid 26:53–55
    Ayoyin
    Ƙid 26:53–55“Ka rarraba musu ƙasar a matsayin gādo, bisa ga yawan kabila. Ga ƙungiya mafi girma, ka ba ta rabo mafi girma; ga ƙaramar ƙungiya kuwa, ka ba ta ƙarami rabo; kowane zai karɓa rabonsa ga yawan mutanen da aka rubuta. Ka tabbatar an rarraba ƙasar ta wurin rabo. Abin da kowace ƙungiya ta gāda zai zama bisa ga sunayen kabilar kakanninta.
  • An gaya wa Haruna ba zai sami gādo a ƙasar baƘid 18:20
    Ayoyin
    Ƙid 18:20Ubangiji ya ce wa Haruna, “Ba ka da gādo a ƙasarsu, ba kuwa za ka sami rabo daga cikinsu ba; ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa.
  • Kyautar sarki ga bawa takan koma a shekarar ’yanciEzk 46:16–17
    Ayoyin
    Ezk 46:16–17“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa in sarkin ya ba wa ɗaya daga cikin ’ya’yansa kyauta daga gādonsa, zai kuwa zama na zuriyar; zai kuwa zama mallakarsu ta wurin gādo. In kuma ya ba wa ɗaya daga cikin bayinsa kyauta daga gadonsa, bawan zai iya riƙe shi sai shekarar ’yantarwa; sa’an nan ya mayar wa sarkin. Gādon sarki na ’ya’yansa maza ne kaɗai; na su ne.

Burin ƙarshe

  • Yaƙub ya harɗe hannuwansa ya sa Efraim gaban ManasseFar 48:13–14, Far 48:19–20
    Ayoyin
    Far 48:13–14Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi. Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.
    Far 48:19–20Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.” Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.
  • Yaƙub ya tara ’ya’yansa maza ya sa wa kowannensu albarka kafin ya mutuFar 49:1, Far 49:28, Far 49:33
    Ayoyin
    Far 49:1Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.
    Far 49:28Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.
    Far 49:33Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.
  • Umarnin ƙarshe na Dawuda ga Solomon1Sar 2:1–3
    Ayoyin
    1Sar 2:1–3Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce, “Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji, ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi.
  • Ishaya ga Hezekiya: “ka kintsa gidanka”2Sar 20:1
    Ayoyin
    2Sar 20:1A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.”
  • Wasiyya takan yi aiki ne kawai bayan wanda ya yi ta ya mutuIbr 9:16–17
    Ayoyin
    Ibr 9:16–17Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta, domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai.
  • Alkawarin mutum da aka tabbatar ba za a soke shi ko a ƙara masa baGal 3:15
    Ayoyin
    Gal 3:15’Yan’uwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawarwa ko yă ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu.
  • Magāji da yake yaro yana ƙarƙashin masu lura da shi da masu riƙon amanaGal 4:1–2
    Ayoyin
    Gal 4:1–2Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome. Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa.

Maganganu

  • Bawa mai hikima zai yi rabon gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwaK Mag 17:2
    Ayoyin
    K Mag 17:2Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa.
  • Dukiyar da aka rasa a cikin ciniki ba ta bar kome da za a ba ɗa baM Had 5:13–14
    Ayoyin
    M Had 5:13–14Na ga wani mugun abu a duniya, arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi, ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara, har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa, babu abin da ya bar masa.
  • Gidaje da dukiya gādo ne daga iyayeK Mag 19:14
    Ayoyin
    K Mag 19:14Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne.
  • Wa ya sani ko magājina zai zama mai hikima ko wawa?M Had 2:18–19
    Ayoyin
    M Had 2:18–19Na ƙi jinin dukan abubuwan da na yi wahala ina yi a duniya, gama dole in bar su wa na bayana. Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.