Bible Explorer

Bincika › Jigogi › ’Yan’uwa maza

Rayuwar yau da kullum

’Yan’uwa maza a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (42), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Abram ya ce wa ɗan ɗan’uwansa Lot, “mu ’yan’uwa ne”Far 12:5, Far 13:8
    Ayoyin
    Far 12:5Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana.
    Far 13:8Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne.
  • Kayinu ya kashe Habila: “ni mai gadin ɗan’uwana ne?”Far 4:8–9
    Ayoyin
    Far 4:8–9To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”
  • Isuwa ya sayar wa Yaƙub hakkinsa na ɗan fari saboda miyaFar 25:29–34
    Ayoyin
    Far 25:29–34Wata rana sa’ad da Yaƙub yana dafa fate. Isuwa ya shigo daga jeji, da yunwa sosai. Ya ce wa Yaƙub, “Ina roƙonka, ka ɗan ɗiba mini faten nan! Ina fama da yunwa!” (Shi ya sa aka kira shi Edom.) Yaƙub ya amsa ya ce, “Ka fara sayar mini da matsayinka na ɗan fari tukuna.” Isuwa ya ce, “Duba, ina gab da mutuwa, me matsayina na ɗan fari zai yi mini?” Amma Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini tukuna.” Don haka ya rantse masa, ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yaƙub. Sa’an nan Yaƙub ya ba wa Isuwa burodi da ɗan miyan lansir. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya tashi ya tafi. Ta haka Isuwa ya yi banza da matsayinsa na ɗan fari.
  • Isuwa ya yi niyya ya kashe Yaƙub bayan mutuwar mahaifinsuFar 27:41
    Ayoyin
    Far 27:41Isuwa ya riƙe Yaƙub a zuciya saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Ya ce wa kansa, “Kwanakin mutuwar mahaifina sun yi kusa; sa’an nan zan kashe ɗan’uwana Yaƙub.”
  • Yaƙub yana tsoron Isuwa da mutanensa ɗari huɗuFar 32:6–7
    Ayoyin
    Far 32:6–7Sa’ad da manzannin suka komo wurin Yaƙub, suka ce, “Mun tafi wurin ɗan’uwanka Isuwa, yanzu kuwa yana zuwa ya sadu da kai, da kuma mutum ɗari huɗu tare da shi.” Da tsoro mai yawa da kuma damuwa, Yaƙub ya rarraba mutanen da suke tare da shi ƙungiyoyi biyu, haka ma garkunan tumaki da awaki, da garkunan shanu da raƙuma.
  • Isuwa ya ruga ya rungumi Yaƙub, dukansu kuma suka yi kukaFar 33:4
    Ayoyin
    Far 33:4Amma Isuwa ya ruga a guje ya sadu da Yaƙub ya rungume shi; ya faɗa a wuyansa ya sumbace shi. Suka kuma yi kuka.
  • Simeyon da Lawi sun rama wa ’yar’uwarsu DinaFar 34:25, Far 34:31
    Ayoyin
    Far 34:25Bayan kwana uku, yayinda dukansu suna cikin zafi mikin kaciya, sai biyu daga cikin ’ya’yan Yaƙub maza, Simeyon da Lawi, ’yan’uwan Dina, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka kashe kowane namiji.
    Far 34:31Amma ’ya’yansa suka amsa, “To, ya dace ke nan da ya yi da ’yar’uwarmu kamar karuwa?”
  • Ruben ya yi ƙoƙari ya ceci Yusuf daga ramiFar 37:21–22, Far 37:29
    Ayoyin
    Far 37:21–22Sa’ad da Ruben ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă cece shi daga hannuwansu. Ya ce, “Kada mu ɗauki ransa. Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa.
    Far 37:29Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa.
  • Yahuda: “mu sayar da shi … shi ɗan’uwanmu ne”Far 37:26–27
    Ayoyin
    Far 37:26–27Yahuda ya ce wa ’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa? Ku zo, mu sayar da shi wa mutanen Ishmayelawan nan, kada mu sa hannuwanmu a kansa; ban da haka ma, shi ɗan’uwanmu ne, jiki da jininmu.” Sai ’yan’uwansa suka yarda.
  • “Bayinka dā su goma sha biyu ne, ’yan’uwa … ɗayan kuma ya rasu”Far 42:13
    Ayoyin
    Far 42:13Amma suka amsa suka ce, “Bayinka dā su goma sha biyu ne, ’yan’uwa, ’ya’yan mutum guda maza, wanda yake zama a ƙasar Kan’ana. Ƙaraminmu yanzu yana tare da mahaifinmu, ɗayan kuma ya rasu.”
  • Yusuf ya shiga ɗaki na ciki don ya yi kuka da ya ga BenyaminFar 43:30
    Ayoyin
    Far 43:30Saboda motsi mai zurfi da zuciyarsa ta yi da ganin ɗan’uwansa, sai Yusuf ya gaggauta ya fita, ya nemi wuri yă yi kuka. Ya shiga ɗakinsa ya yi kuka a can.
  • Yahuda ya miƙa kansa ya zauna bawa a madadin BenyaminFar 44:33–34
    Ayoyin
    Far 44:33–34“To, yanzu, ina roƙonka bari bawanka yă zauna a nan a matsayin bawanka, ranka yă daɗe a maimakon saurayin, a kuma bar saurayin yă koma da ’yan’uwansa. Yaya zan koma ga mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? A’a! Kada ka bari in ga baƙin cikin da zai auko wa mahaifina.”
  • “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar!”Far 45:3–4
    Ayoyin
    Far 45:3–4Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa. Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar!
  • Yusuf ya rungumi Benyamin ya sumbaci dukan ’yan’uwansaFar 45:14–15
    Ayoyin
    Far 45:14–15Sa’an nan ya rungume ɗan’uwansa Benyamin ya yi kuka, sai Benyamin ya rungume shi yana kuka. Ya sumbaci dukan ’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai ’yan’uwansa suka yi masa magana.
  • Yusuf: “Kada ku yi faɗa a hanya!”Far 45:24
    Ayoyin
    Far 45:24Sa’an nan ya sallami ’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!”
  • Bayan mutuwar Yaƙub Yusuf ya kwantar wa ’yan’uwansa da suke tsoro raiFar 50:15–21
    Ayoyin
    Far 50:15–21Sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka ga cewa mahaifinsu ya mutu, sai suka ce, “Mai yiwuwa Yusuf yana riƙe da mu a zuciya, wataƙila zai rama dukan abubuwa marasa kyau da muka yi masa?” Saboda haka suka aika wa Yusuf suna cewa, “Mahaifinka ya bar waɗannan umarnai kafin yă rasu. Ga abin da za ku ce wa Yusuf, ‘Na roƙe ka, ka gafarta wa ’yan’uwanka zunubai da laifofin da suka aikata na abubuwa marasa kyau da suka yi maka.’ Yanzu muna roƙonka ka gafarta zunuban bayin Allah na mahaifinka.” Sa’ad da saƙonsu ya zo masa, sai Yusuf ya yi kuka. ’Yan’uwansa kuwa suka zo suka fāɗi a gabansa suka ce, “Mu bayinka ne.” Amma Yusuf ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Ni Allah ne? Kun yi niyya ku yi mini lahani, amma Allah ya nufe wannan ya zama alheri don yă cika abin da yanzu yake faruwa, ceton rayuka masu yawa. Saboda haka, kada ku ji tsoro. Zan tanada muku da kuma ’ya’yanku.” Ya sāke tabbatar musu, ya kuma yi musu magana ta alheri.
  • Haruna zai yi magana da mutane a madadin ɗan’uwansa MusaFit 4:14–16
    Ayoyin
    Fit 4:14–16Sai Ubangiji ya yi fushi da Musa ya ce, “Ɗan’uwanka Haruna Balawe, ba ya nan ne? Na san ya iya magana. Ya riga ya kama hanya don yă sadu da kai, zai kuma yi farin ciki sa’ad da ya gan ka. Za ka yi masa magana. Ka kuma sa masa maganata a baki; zan kuma taimake ku magana, in koya muku abin da za ku yi. Zai yi magana da mutane a madadinka, zai zama kamar bakinka, kai kuwa kamar Allah a gare shi.
  • Abimelek ya kashe ’yan’uwansa; ƙaramin, Yotam, ya ɓuyaMah 9:5
    Ayoyin
    Mah 9:5Sai ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra kuma a dutse guda ya kashe ’yan’uwansa, ’ya’yan Yerub-Ba’al. Amma Yotam, autan ɗan Yerub-Ba’al ya tsira ta wurin ɓuya.
  • ’Yan’uwan Yefta sun kore shi daga gidan mahaifinsuMah 11:2–3
    Ayoyin
    Mah 11:2–3Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.” Saboda haka Yefta ya tsere daga ’yan’uwansa ya zauna a ƙasar Tob, inda waɗansu ’yan iska suka kewaye shi suka bi shi.
  • ’Ya’yan Yesse maza: Dawuda shi ne na bakwai1Tar 2:13–15
    Ayoyin
    1Tar 2:13–15Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya, na huɗun Netanel, na biyar Raddai, na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda.
  • Eliyab, babban ɗan, ya tsawata wa ɗan’uwansa Dawuda1Sam 17:28
    Ayoyin
    1Sam 17:28Da wansa Eliyab, ya ji yana magana da mutanen, sai ransa ya ɓace ƙwarai saboda fushi, sai ya ce wa Dawuda, “Me ka zo yi a nan? Wa kuma ka bar wa ’yan tumakin a jeji? Na san ka da taurinkai, da kuma mugun hali. Ka zo nan ne don ka yi kallon yaƙi kawai.”
  • Yowab, Abishai da Asahel, ’ya’ya maza uku na Zeruhiya2Sam 2:18
    Ayoyin
    2Sam 2:18’Ya’yan Zeruhiya, maza uku sun kasance a can. Su ne, Yowab, Abishai da Asahel. To, Asahel mai gudu ne kamar barewa.
  • Absalom ya sa aka kashe Amnon saboda ya kunyata ’yar’uwarsu Tamar2Sam 13:22, 2Sam 13:28–29
    Ayoyin
    2Sam 13:22Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar.
    2Sam 13:28–29Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.” Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.
  • Solomon ya sa aka kashe wansa Adoniya1Sar 2:22–25
    Ayoyin
    1Sar 2:22–25Sarki Solomon ya amsa wa mahaifiyarsa ya ce, “Me ya sa kika roƙar wa Adoniya Abishag mutuniyar Shunam kawai? Ki ma sa a ba shi mulkin mana. Ai, shi yayana ne. I, ki roƙa dominsa, da domin Abiyatar firist, da kuma domin Yowab ɗan Zeruhiya mana!” Sai Sarki Solomon ya rantse da sunan Ubangiji ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani, idan ban sa Adoniya ya biya wannan roƙo da ransa ba! Yanzu kuwa, muddin Ubangiji yana a raye, shi wanda ya kafa ni sosai a kan kujerar sarautar mahaifina Dawuda, ya kuma kafa mini mulki kamar yadda ya yi alkawari; za a kashe Adoniya yau!” Saboda haka Sarki Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada yă kashe Adoniya; ya kuwa kashe shi.
  • Yehoram ya kashe dukan ’yan’uwansa da takobi2Tar 21:4
    Ayoyin
    2Tar 21:4Sa’ad da Yehoram ya kafa kansa sosai a bisa mulkin mahaifinsa, sai ya kashe dukan ’yan’uwansa da takobi tare da waɗansu sarakunan Isra’ila.
  • ’Yan’uwa masunta biyu-biyu a bakin Tekun GaliliMat 4:18, Mat 4:21
    Ayoyin
    Mat 4:18Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.
    Mat 4:21Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su,
  • Andarawus ya fara samun ɗan’uwansa Siman ya kawo shi wurin YesuYoh 1:40–42
    Ayoyin
    Yoh 1:40–42Andarawus ɗan’uwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu. Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi). Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan).
  • Marta da Maryamu: “da ɗan’uwana bai mutu ba”Yoh 11:21, Yoh 11:32
    Ayoyin
    Yoh 11:21Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.
    Yoh 11:32Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.”
  • ’Yan’uwan Yesu Yaƙub, Yusuf, Yahuda da SimanMar 6:3
    Ayoyin
    Mar 6:3Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.
  • ’Yan’uwansa ba su gaskata ba, amma daga baya sun yi addu’a tare da almajiraiYoh 7:5, Ayy M 1:14
    Ayoyin
    Yoh 7:5Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.
    Ayy M 1:14Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa.

A cikin Doka da maganganu

  • Kada ka riƙe ƙiyayya a zuciyarka game da ɗan’uwankaFir 19:17
    Ayoyin
    Fir 19:17“ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.
  • Ka mayar wa ɗan’uwanka sansa ko tunkiyarsa da ta ɓaceM Sh 22:1–2
    Ayoyin
    M Sh 22:1–2In kun ga saniya ko tunkiyar ɗan’uwanku wadda ta ɓace, kada ku ƙyale ta, amma ku tabbata kun komar da ita gare shi. In ɗan’uwan ba ya zama kusa da ku, ko kuwa ba ku san shi ba, sai ku kai ta gida ku ajiye ta sai ya zo nemanta. Sa’an nan ku ba shi ita.
  • Yana da kyau sa’ad da ’yan’uwa suke zama tare cikin haɗin kaiZab 133:1
    Ayoyin
    Zab 133:1Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!
  • Ɗan’uwan da aka ɓata wa rai ya fi birni mai kagara wuyar rinjayaK Mag 18:19
    Ayoyin
    K Mag 18:19Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.
  • Ka fara shirya da ɗan’uwanka, sa’an nan ka miƙa kyautarkaMat 5:23–24
    Ayoyin
    Mat 5:23–24“Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.