Bincika › Jigogi › Kishi da hassada
Rayuwar yau da kullum
Kishi da hassada a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (26), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Kishi yakan husata mijiK Mag 6:34
Ayoyin
K Mag 6:34Gama kishi kan tā da hasalar miji, kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.
- Fushi kamar rigyawa ne, amma wa zai iya tsayayya da kishi?K Mag 27:4
Ayoyin
K Mag 27:4Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?
- Hassada takan ruɓar da ƙasusuwaK Mag 14:30
Ayoyin
K Mag 14:30Zuciya mai salama kan ba jiki rai, amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo.
- Wahala da nasara sukan fito daga hassadar maƙwabciM Had 4:4
Ayoyin
M Had 4:4Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
- Ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, kishinta kuma kamar muguntar kabariWW 8:6
Ayoyin
WW 8:6Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka, kamar hatimi a hannunka; gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, kishinta yana kamar muguntar kabari, yana ƙuna kamar wuta mai ci, kamar gagarumar wuta.
- Inda kishi yake, akwai rikiciYaƙ 3:16
Ayoyin
Yaƙ 3:16Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.
- Gwajin Doka domin matar da mijinta mai kishi yake zargiƘid 5:12–31
Ayoyin
Ƙid 5:12–31“Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In matar wani ta kauce, ta kuma yi rashin aminci gare shi ta wurin kwana da wani dabam, wannan kuwa ya kasance a ɓoye ga mijinta, rashin tsarkinta kuwa bai tonu ba (da yake babu shaida, ba a kuma kama ta tana yi ba), in kuma kishi ya sha kan mijinta kuma tana da ƙazanta, ko kuwa idan yana kishi yana kuma zatonta ko ma ba ta da ƙazanta mijin zai kai matansa a gaban firist, yă kuma kawo hadayar abubuwan da ake bukata; abubuwa kamar, garin sha’ir garwa ɗaya, amma kada yă zuba mai a kan garin sha’ir, kada kuma yă sa turaren wuta a kansa, domin hadaya ce ta miji mai tuhumar matarsa da aka kawo domin gaskiya tă fito fili. “ ‘Firist zai kawo ta, yă sa tă tsaya a gaban Ubangiji. Sa’an nan zai ɗebi ruwa mai tsarki a tulun laka, yă zuba ƙurar da ya ɗebo daga daɓen tabanakul a cikin ruwan. Bayan da firist ya sa matan ta tsaya a gaban Ubangiji, sai yă kunce gashin kanta, yă kuma sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi, yayinda shi kansa zai riƙe ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana. Sa’an nan firist zai sa tă yi rantsuwa, yă kuma ce mata, “In ba wani mutumin da ya kwana da ke kuma ba ki kauce kin ƙazantar da kanki yayinda kike auren mijinki ba, kada wannan ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, yă cuce ki. Amma in kin kauce yayinda kike auren mijinki, kika kuma ƙazantar da kanki ta wurin kwana da wani dabam da ba mijinki ba,” (a nan firist zai sa macen a ƙarƙashin la’anar rantsuwa cewa) “bari Ubangiji yă sa mutanenki su la’ance ki, su kuma yi Allah wadai da ke, sa’ad da Ubangiji ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbura. Bari wannan ruwa mai jawo la’ana, yă shiga jikinki saboda cikinki yă kumbura, cinyarki kuma yă shanye.” “ ‘Sai macen tă ce, “Amin. Bari yă zama haka.” “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci. Sai yă sa macen tă sha ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, wannan ruwa kuwa zai shiga cikinta yă kawo mata wahala mai zafi. Firist zai karɓi hadaya ta gari don kishi daga hannuwanta, yă kaɗa shi a gaban Ubangiji sa’an nan yă kawo a bagade. Sa’an nan firist zai ɗiba hatsi na hadaya cike da hannunsa don hadayar tunawa, yă kuma ƙone a bagade; bayan haka sai yă sa macen tă sha ruwan. In ta ƙazantar da kanta ta kuma ci amanar mijinta, to, yayinda aka sa tă sha ruwa mai jawo la’ana, ruwan zai shiga cikinta, yă jawo mata wahala mai zafi; cikinta zai kumbura, cinyarta kuma yă shanye, tă kuwa zama la’ananniya a cikin mutanenta. Amma fa, in macen ba tă ƙazantar da kanta ba, ba tă kuma da ƙazanta, za a kuɓutar da ita daga laifin, za tă kuma iya haihuwa. “ ‘Wannan dai, ita ce dokar kishi sa’ad da mace ta kauce, ta kuma ƙazantar da kanta yayinda take aure da mijinta, ko kuma sa’ad da mijin yana kishi domin yana shakkar matarsa. Firist zai sa tă tsaya a gaban Ubangiji, yă kuma yi amfani da wannan doka gaba ɗaya a kanta. Mijin zai zama marar laifi daga kowane laifi, amma matar za tă ɗauki muguntarta, idan ta yi laifin.’ ”
Misalai
- Kayinu, da ya ji haushi cewa an karɓi hadayar Habila, ya kashe shiFar 4:4–8
Ayoyin
Far 4:4–8Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace? Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.” To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.
- Hagar mai ciki ta raina Saira, Saira kuma ta wulaƙanta taFar 16:4–6
Ayoyin
Far 16:4–6Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki. Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta. Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.” Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta.
- Filistiyawa suna hassadar garkunan tumaki da na shanu na IshakuFar 26:14
Ayoyin
Far 26:14Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa.
- Rahila tana kishin Liyatu: “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!”Far 30:1
Ayoyin
Far 30:1Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!”
- ’Yan’uwan Yusuf suna kishinsa, suka sayar da shiFar 37:4, Far 37:11, Far 37:18–28
Ayoyin
Far 37:4Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
Far 37:11’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya.
Far 37:18–28Amma da suka gan shi daga nesa, kafin yă kai wurinsu, sai suka ƙulla su kashe shi. Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa! Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.” Sa’ad da Ruben ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă cece shi daga hannuwansu. Ya ce, “Kada mu ɗauki ransa. Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa. Saboda haka sa’ad da Yusuf ya zo wurin ’yan’uwansa, sai suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai gwanin kyau da ya sa, suka kuma ɗauke shi suka jefa a cikin rijiya. To, rijiyar wofi ce, babu ruwa a ciki. Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar. Yahuda ya ce wa ’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa? Ku zo, mu sayar da shi wa mutanen Ishmayelawan nan, kada mu sa hannuwanmu a kansa; ban da haka ma, shi ɗan’uwanmu ne, jiki da jininmu.” Sai ’yan’uwansa suka yarda. Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.
- Musa ga Yoshuwa: “Kana kishi domina ne?”Ƙid 11:28–29
Ayoyin
Ƙid 11:28–29Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!” Amma Musa ya amsa ya ce, “Kana kishi domina ne? Da ma a ce dukan mutanen Ubangiji annabawa ne, da ma a kuma ce Ubangiji ya sa Ruhunsa a kansu mana!”
- Miriyam da Haruna: “Ubangiji ya yi magana ta wurin Musa ne kaɗai?”Ƙid 12:1–2
Ayoyin
Ƙid 12:1–2Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa ’yar ƙasar Kush da ya aura. Suka ce, “ Ubangiji ya yi magana ta wurin Musa ne kaɗai? Ashe, bai yi magana ta wurinmu mu ma ba?” Ubangiji kuwa ya ji wannan.
- Mutanen Efraim sun ji haushin Gideyon da Yefta don ba su kira su baMah 8:1, Mah 12:1
Ayoyin
Mah 8:1To, mutanen Efraim suka ce wa Gideyon, “Me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ba ka kira mu lokacin da ka tafi yaƙi da Midiyawa ba?” Suka zarge shi sosai.
Mah 12:1Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”
- Shawulu ya ji haushin waƙar “Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai”1Sam 18:7–9
Ayoyin
1Sam 18:7–9Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.” Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?” Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda.
- Yowab ya kashe Abner, wanda Dawuda ya sallame shi lafiya2Sam 3:24–27
Ayoyin
2Sam 3:24–27Sai Yowab ya je wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka. Don me ka ƙyale shi yă tafi? Ga shi kuwa ya tafi! Ka san Abner ɗan Ner ya zo ne yă ruɗe ka, yă ga fitarka da shigarka, yă kuma binciki kome da kake yi.” Yowab ya tashi daga gaban Dawuda ya tafi ya aika manzanni su bi Abner. Suka same shi a rijiyar Sira suka komo da shi, Dawuda kuwa bai sani ba. To, da Abner ya komo Hebron, Yowab ya ratse da shi zuwa hanyar shigar gari kamar zai gana da shi a kaɗaice. Amma a can ya soki Abner a ciki, ya kashe shi don yă rama mutuwar ɗan’uwansa Asahel.
- Isra’ila da Yahuda sun yi gardama a kan wa ya komo da sarki2Sam 19:41–43
Ayoyin
2Sam 19:41–43Nan take sai ga mutane Isra’ila suna zuwa wurin sarki, suna cewa, “Don me ’yan’uwanmu, mutanen Yahuda, suka saci sarki, suka kawo shi da iyalinsa a ƙetaren Urdun, tare da dukan mutanensa?” Dukan mutanen Yahuda suka ce wa mutanen Isra’ila, “Mun yi haka domin sarki danginmu na kurkusa ne. Don me kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abu daga cikin kayan sarki ne? Mun ɗauki wani abu wa kanmu ne?” Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa mutanen Yahuda, “Muna da rabo goma a wurin sarki; ban da haka ma, muna da hakki mafi yawa a wurin Dawuda fiye da ku. Don me kuke mana reni? Ba mu ne ma muka fara magana dawowa da sarki ba?” Amma mutanen Yahuda suka ɗauka maganar da zafi fiye da mutanen Isra’ila.
- Wan ɗa mai ɓarna ya ƙi ya shiga gidaLuk 15:25–30
Ayoyin
Luk 15:25–30“Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa. Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa. Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’ “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi. Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba. Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’
- Bilatus ya san sun ba da Yesu ne saboda hassadaMat 27:18
Ayoyin
Mat 27:18Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi.
- Babban firist da Sadukiyawa sun cika da kishiAyy M 5:17
Ayoyin
Ayy M 5:17Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi.
- Taron mutane masu kishi sun yi gāba da Bulus a Antiyok da TessalonikaAyy M 13:45, Ayy M 17:5
Ayoyin
Ayy M 13:45Sa’ad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi.
Ayy M 17:5Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ’yan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka tā da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.