Bincika › Jigogi › Farauta da tarko
Rayuwar yau da kullum
Farauta da tarko a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (14), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Nimrod, “babban maharbi a gaban Ubangiji”Far 10:9
Ayoyin
Far 10:9Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
- Ishmayel ya yi girma a jeji ya zama gwanin maharbin bakaFar 21:20
Ayoyin
Far 21:20Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi.
- Isuwa ya zama gwanin maharbi, mutumin jejiFar 25:27
Ayoyin
Far 25:27Yaran suka yi girma, Isuwa kuwa ya zama riƙaƙƙen maharbi, mutumin jeji, yayinda Yaƙub, shiru-shiru ne mai son zama a tentuna.
- Ishaku yana son naman farauta, yana kuma ƙaunar IsuwaFar 25:28
Ayoyin
Far 25:28Ishaku, mai son ci naman jeji, ya ƙaunaci Isuwa, amma Rebeka ta ƙaunaci Yaƙub.
- Ishaku ya aiki Isuwa da kwari da baka ya je farautaFar 27:3–5
Ayoyin
Far 27:3–5Saboda haka yanzu, ka ɗauki makamanka, kwari da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama. Ka shirya mini irin abinci mai daɗin da nake so, ka kawo mini in ci, domin in sa maka albarka kafin in mutu.” Ashe, Rebeka tana ji sa’ad da Ishaku ya yi wa ɗansa Isuwa magana. Da Isuwa ya tafi jeji don yă farauto nama yă kawo,
- Isuwa ya dawo daga farauta a makare domin albarkarFar 27:30–33
Ayoyin
Far 27:30–33Bayan Ishaku ya gama sa masa albarka, Yaƙub yana fita daga mahaifinsa ke nan, sai ga ɗan’uwansa Isuwa ya dawo daga farauta. Shi ma ya shirya abinci mai daɗi ya kawo wa mahaifinsa. Sa’an nan ya ce masa, “Babana, tashi ka zauna ka ci daga abin da na farauto, domin ka sa mini albarka.” Mahaifinsa Ishaku ya tambaye shi, “Wane ne kai?” Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.” Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce, “To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!”
A cikin Doka
Tarkuna da taruna
- Taru, raga, tarko, shingi da igiyar da aka ɓoye a ƙasaAyu 18:8–10
Ayoyin
Ayu 18:8–10Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar. Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam. An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.
- Barewa da aka kama da tarkoIsh 51:20
Ayoyin
Ish 51:20’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki.
- Masu kafa tarko sukan yi kwanto su kafa tarkunaIrm 5:26
Ayoyin
Irm 5:26“A cikin mutanena an sami mugaye waɗanda suke kwanton ɓauna kamar masu sa tarko wa tsuntsaye kamar waɗanda suke kafa tarko don su kama mutane.
- Igiyoyin taru da aka shimfiɗa a gefen hanya, da tarkunan da aka kafaZab 140:5
Ayoyin
Zab 140:5Masu girman kai sun sa mini tarko; sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu sun kuma shirya mini tarko a hanyata. Sela
Kwatanci
- Dawuda: kamar mai farautar kazan duwatsu1Sam 26:20
Ayoyin
1Sam 26:20Kada ka yarda jinina yă zuba a ƙasa nesa da gaban Ubangiji. Sarkin Isra’ila ya fito yă nemi kuɗin cizo kamar mai farautar kazan duwatsu.”
- “Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu”Mako 3:52
Ayoyin
Mako 3:52Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu.
- An cece shi “daga tarkon mai farauta”Zab 91:3
Ayoyin
Zab 91:3Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.