Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Noma

Rayuwar yau da kullum

Noma a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (37), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • An sa mutumin a Eden don ya nome shi ya kuma lura da shiFar 2:15
    Ayoyin
    Far 2:15Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.
  • Kayinu manomi ne; Habila makiyayin tumaki neFar 4:2
    Ayoyin
    Far 4:2Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.
  • Nuhu, manomi, ya shuka gonar inabiFar 9:20
    Ayoyin
    Far 9:20Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi.
  • Ishaku ya yi shuka ya girbe ninki ɗari a shekararFar 26:12
    Ayoyin
    Far 26:12Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi.
  • Rut ta yi kala a bayan masu girbi: kamar efa ta sha’irRut 2:2–3, Rut 2:17
    Ayoyin
    Rut 2:2–3Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je, ’yata.” Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek.
    Rut 2:17Saboda haka Rut ta yi kala a gonar har yamma. Sa’an nan ta sussuka hatsin sha’ir da ta kalata ta sami kamar efa.
  • Bowaz yana shiƙar sha’ir da dare a masussukaRut 3:2
    Ayoyin
    Rut 3:2Bowaz wanda kike aiki da bayinsa ’yan mata ba danginmu ne na kusa ba? Da daren yau zai sussuka sha’ir nasa a masussuka.
  • Gideyon yana sussukar alkama a wurin matsewar inabi don ya ɓoye ta daga MidiyawaMah 6:11
    Ayoyin
    Mah 6:11Sai mala’ikan Ubangiji ya zo ya zauna a ƙarƙashin itacen oak a Ofra na Yowash mutumin Abiyezer, inda ɗansa Gideyon yake sussukar alkama a wurin matsin inabi don yă ɓoye daga Midiyawa.
  • Mutanen Bet-Shemesh suna girbin alkama a kwari1Sam 6:13
    Ayoyin
    1Sam 6:13A lokacin kuwa mutanen Bet-Shemesh suna girbin alkamansu a kwari da suka ɗaga ido suka hangi akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi farin ciki ganinsa.
  • Isra’ilawa sukan je wurin Filistiyawa don su wasa garmuna da laujeji1Sam 13:19–21
    Ayoyin
    1Sam 13:19–21Ba a sami maƙeri ɗaya a dukan ƙasar Isra’ila ba domin Filistiyawa sun ce, “In ba haka ba Ibraniyawa za su ƙera wa kansu takuba ko māsu.” Saboda haka dukan Isra’ila sukan gangara zuwa wajen Filistiyawa domin su gyara bakin garemaninsu, da fartanansu, da gaturansu, da kuma laujunansu. Duk lokacin da za su gyara bakin garmansu da fartanyarsu sai sun biya tsabar azurfa biyu. Haka ma idan za su gyara gatari ko bakunan abin korar shanun noma sai sun biya tsabar azurfa ɗaya.
  • Elisha yana noma da shanu nau’i goma sha biyu1Sar 19:19
    Ayoyin
    1Sar 19:19Sai Iliya ya tafi daga can ya sami Elisha ɗan Shafat, yana noma da shanu goma sha biyu masu garman noma, shi kansa yana jan na goma sha biyun. Iliya ya tafi wurinsa ya jefa mayafinsa a kan Elisha.
  • Hakiman Dawuda a kan gonaki, gonakin inabi, itatuwan zaitun da garkuna1Tar 27:26–31
    Ayoyin
    1Tar 27:26–31Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da ma’aikatan gona waɗanda suke nome ƙasar. Shimeyi mutumin Ramat shi ne mai lura da gonakin inabi. Zabdi mutumin Shifam shi ne mai lura da amfanin gonakin inabi don matsin ruwan inabi. Ba’al-Hanan mutumin Geder shi ne mai lura da itatuwan zaitun da na al’ul a gindin tuddan yamma. Yowash shi ne mai lura da tanadin man zaitun. Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon. Shafat ɗan Adlai shi ne mai lura da garkuna a kwari. Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma. Yedehiya mutumin Meronot shi ne mai lura da jakuna. Yaziz mutumin Hagiri shi ne mai lura da tumaki. Dukan waɗannan shugabanni ne masu lura da mallakar Sarki Dawuda.
  • Uzziya, mai son ƙasa, yana da manoma da masu gyaran inabi2Tar 26:10
    Ayoyin
    2Tar 26:10Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma.
  • Solomon ya shuka gonakin inabi da lambuna ya kuma gina tafkunaM Had 2:4–6
    Ayoyin
    M Had 2:4–6Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi. Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu. Na yi tankuna don in yi banruwan kurmin itatuwa.
  • Noma, shuka a jeri, da sussukar kowane hatsi a hanyarsaIsh 28:24–28
    Ayoyin
    Ish 28:24–28Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne? Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne? Sa’ad da ya shirya wuri da kyau, ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba? Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa sha’ir a kunyoyinsa, tamba kuma a filinsa ba? Allahnsa ya umarce shi ya kuma koya masa hanyar da take daidai. Ba a bugan kanumfari da ƙaton sanda ko a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya; akan buga kanumfari da siririn sanda ɗaɗɗoya kuma da tsumagiya. Dole a niƙa hatsi don a yi burodi; saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba. Ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.
  • Manomi yakan jira ruwan sama na kaka da na bazaraYaƙ 5:7
    Ayoyin
    Yaƙ 5:7Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka.
  • Almajirai sun zagi zangarkun hatsi yayinda suke ratsa gonakiMat 12:1
    Ayoyin
    Mat 12:1A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.
  • Iri a hanya, a kan dutse, cikin ƙaya, a ƙasa mai kyau (misali)Mat 13:3–8
    Ayoyin
    Mat 13:3–8Sa’an nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa, “Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su. Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi. Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su. Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka.
  • An yi hayar ma’aikata a gonar inabi a dinari guda a yini (misali)Mat 20:1–2
    Ayoyin
    Mat 20:1–2“Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa. Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.

A cikin Doka

  • Ku yi shuka shekara shida; a ta bakwai ƙasar ta hutaFit 23:10–11, Fir 25:3–5
    Ayoyin
    Fit 23:10–11“Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar, amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.
    Fir 25:3–5Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu. Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi. Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu.
  • Ku huta a rana ta bakwai, ko lokacin noma da girbiFit 34:21
    Ayoyin
    Fit 34:21“Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta.
  • Ku bar gefen gona da inabin da suka fāɗi domin matalautaFir 19:9–10
    Ayoyin
    Fir 19:9–10“ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku. Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
  • Damin da aka manta akan bar shi domin baƙo, maraya da gwauruwaM Sh 24:19–21
    Ayoyin
    M Sh 24:19–21Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku. Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa. Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.
  • Kada ku shuka iri biyu tare; kada ku haɗa sa da jaki a karkiyaFir 19:19, M Sh 22:9–10
    Ayoyin
    Fir 19:19“ ‘Ku kiyaye farillaina. “ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
    M Sh 22:9–10Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku; in kuka yi haka, ba abin da kuka shuka ne kaɗai zai ƙazantu ba, amma har da inabinku ma. Kada ku haɗa bijimi da jaki su yi noma tare.
  • Ba a cin ’ya’yan sabon itacen da aka shuka har shekara ukuFir 19:23–25
    Ayoyin
    Fir 19:23–25“ ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai ’ya’ya na ci, ku ɗauki ’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci. Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba. A shekara ta huɗu, dukan ’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji. Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin ’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku.
  • Biyan diyya saboda dabbobin da suka yi yawo ko wutar da ta ci gonaFit 22:5–6
    Ayoyin
    Fit 22:5–6“In mutum ya sa dabbobinsa su yi kiwo a fili ko a gonar inabi, ya kuma bar dabbobinsa suka yi ɓarna a cikin gonar wani, sai a sa mai dabbar yă biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka. “In gobara ta tashi, ta kuma bazu cikin ƙayayyuwa, har ta cinye tarin hatsi, ko hatsin da ke tsaye, ko dukan gonar, dole wanda ya sa wutar, yă biya taran da aka yanka masa saboda ɓarnan da wutar ta yi.
  • Ka ci iyakar ƙoshinka a gonar inabin maƙwabci, amma kada ka cika kwandoM Sh 23:24–25
    Ayoyin
    M Sh 23:24–25In kun shiga gonar inabin maƙwabcinku, za ku iya cin inabin da kuke so, amma kada ku sa wani a kwandonku. In kun shiga gonar hatsin maƙwabcinku, za ku iya murmure tsabar da hannuwanku, amma kada ku sa lauje ku yanka hatsinsa da yake tsaye.
  • Kada ka sa wa sa takunkumi yayinda yake sussukar hatsiM Sh 25:4
    Ayoyin
    M Sh 25:4Kada ku yi wa saniya takunkumi sa’ad da take tattaka hatsi.
  • Mutumin da bai riga ya ci amfanin sabuwar gonar inabinsa ba akan mai da shi gida daga yaƙiM Sh 20:6
    Ayoyin
    M Sh 20:6Ko akwai wani da ya shuka inabi, bai kuwa fara jin daɗinsa ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă ji daɗinsa.

Maganganu

  • Wanda yake noma ƙasarsa zai sami abinci da yawaK Mag 12:11
    Ayoyin
    K Mag 12:11Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
  • Gonar rago cike da ƙaya, katangar dutsenta ta rusheK Mag 24:30–31
    Ayoyin
    K Mag 24:30–31Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci; ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe.
  • Ka shuka iri da safe; kada ka huta hannuwanka da yammaM Had 11:6
    Ayoyin
    M Had 11:6Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.
  • Ka san lafiyar garkunan tumakinka da na shanunkaK Mag 27:23–27
    Ayoyin
    K Mag 27:23–27Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka; domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara. Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai, gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki. Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.
  • Wanda ya yi shuka kaɗan zai kuma girbe kaɗan2Kor 9:6
    Ayoyin
    2Kor 9:6Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace.
  • Manomi mai aiki tuƙuru ya kamata ya fara samun rabo daga amfanin gona2Tim 2:6
    Ayoyin
    2Tim 2:6Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.