Rayuwar yau da kullum
Azumi a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (40), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Lokacin makoki da baƙin ciki
- Mutanen Yabesh sun binne ƙasusuwan Shawulu suka yi azumi kwana bakwai1Sam 31:13
Ayoyin
1Sam 31:13Sai suka kwashi ƙasusuwansu suka binne a gindin itace tsamiya a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
- Dawuda da mutanensa sun yi azumi har yamma saboda Shawulu da Yonatan2Sam 1:12
Ayoyin
2Sam 1:12Suka yi makoki, da kuka, da azumi har yamma saboda Shawulu da ɗansa Yonatan, da saboda sojojin Ubangiji, da kuma gidan Isra’ila, gama an karkashe su a yaƙi.
- Dawuda ya ƙi cin abinci har faɗuwar rana bayan mutuwar Abner2Sam 3:35
Ayoyin
2Sam 3:35Sa’an nan duk suka zo suka roƙi Dawuda yă ci wani abu tun rana ba tă fāɗi ba; amma Dawuda ya rantse ya ce, “Bari Allah yă hukunta ni, in na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta fāɗi!”
- Dawuda ya yi azumi saboda ɗansa marar lafiya, ya ci abinci da yaron ya mutu2Sam 12:16–23
Ayoyin
2Sam 12:16–23Dawuda ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi, ya kuma shiga gidansa ya kwana kwance a ƙasa. Dattawan iyalinsa suka tsaya kusa da shi don su ɗaga shi daga ƙasa, amma ya ƙi, bai kuwa ci wani abu tare da su ba. A rana ta bakwai sai yaron ya rasu. Barorin Dawuda suka ji tsoro su gaya masa cewa yaron ya mutu, gama sun yi tunani cewa, “Yayinda yaron yake da rai, mun yi magana da Dawuda bai ji mu ba. Yaya za mu gaya masa yaron ya mutu? Ai, zai yi wa kansa ɓarna.” Dawuda ya gane bayinsa suna wa juna raɗan wani abu, sai ya gane yaron ya mutu. Sai ya ce, “Yaron ya rasu ko?” Suka ce, “I, ya rasu.” Sa’an nan Dawuda ya tashi daga ƙasa. Bayan ya yi wanka, ya shafa mai, ya kuma canja rigunarsa, sa’an nan ya shiga gidan Ubangiji ya yi sujada. Sai ya tafi gidansa, ya nemi a ba shi abinci, aka ba shi, ya kuwa ci. Barorinsa suka ce masa, “Me ya sa kake yin haka? Yayinda yaron yake da rai, ka yi azumi, ka kuma yi kuka, amma yanzu da yaron ya mutu, ka tashi, ka kuma ci abinci!” Ya ce musu, “Yayinda yaron yake da rai, na yi azumi, na kuma yi kuka. Na yi tunani na ce, ‘Wa ya sani? Ko Ubangiji zai yi mini alheri yă bar yaron yă rayu.’ Amma yanzu da ya mutu, me zai sa in yi azumi? Zan iya dawo da shi ne? Ni zan je wajensa, ba shi zai dawo wurina ba.”
- Nehemiya ya yi makoki kwanaki, yana azumi, da ya ji labarin UrushalimaNeh 1:4
Ayoyin
Neh 1:4Da na ji waɗannan abubuwa, sai na zauna na yi kuka. Na yi kwanaki ina makoki da azumi, na kuma yi addu’a a gaban Allah na sama.
- Ezra bai ci abinci ba bai kuma sha ruwa ba, yana makokiEzr 10:6
Ayoyin
Ezr 10:6Sa’an nan Ezra ya tashi daga gidan Allah ya tafi gidan Yehohanan ɗan Eliyashib, a can ma bai ci wani abu ba, bai sha ruwa ba domin ya ci gaba da yin baƙin cikin rashin aminci na waɗanda suka dawo daga bauta.
- Mai zabura ya yi azumi cikin tsummokin makoki sa’ad da waɗansu suke ciwoZab 35:13
Ayoyin
Zab 35:13Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,
Lokacin haɗari da wahala
- Esta: “Kada ku ci ko ku sha, dare da rana har kwana uku”Esta 4:16
Ayoyin
Esta 4:16“Ka tafi, ka tattara dukan Yahudawan da suke Shusha, ku yi azumi saboda ni. Kada ku ci ko ku sha, dare da rana har kwana uku. Ni kuwa da bayina za mu yi azumi yadda kuke yi. Idan aka yi haka, zan tafi wurin sarki, ko da yake wannan karya doka ce. Idan na hallaka, to, na hallaka.”
- Yehoshafat ya yi shelar azumi a dukan Yahuda2Tar 20:3
Ayoyin
2Tar 20:3A firgice, Yehoshafat ya yanke shawara yă nemi nufin Ubangiji, ya kuma yi shelar azumi a dukan Yahuda.
- Ezra ya yi shelar azumi a Kogin Ahawa domin tafiya lafiyaEzr 8:21–23
Ayoyin
Ezr 8:21–23A can, a bakin rafin Ahawa, na sa mu yi azumi, domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu kuma roƙe shi yă kiyaye mana hanya, da mu da ’ya’yanmu da kayanmu duka. Na ji kunya in roƙi sarki yă haɗa mu da sojoji da masu dawakai don su yi mana rakiya su kāre mu daga magabta a kan hanya, gama mun ce wa sarki, “Alherin Allah yana tare da duk wanda yake dogara gare shi, amma kuma fushinsa yana kan duk wanda ya juya masa baya.” Saboda haka sai muka yi azumi, muka kai roƙonmu a wurin Allah, ya kuwa amsa mana.
- Isra’ila sun yi kuka suka yi azumi a Betel lokacin yaƙi da BenyaminMah 20:26
Ayoyin
Mah 20:26Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji.
- A Mizfa mutane sun zuba ruwa suka yi azumi1Sam 7:6
Ayoyin
1Sam 7:6Sa’ad da suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa suka zuba a gaban Ubangiji. A wannan rana suka yi azumi suka tuba, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi!” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.
- Isra’ila sun taru suna azumi, saye da tsummokin makoki, da ƙura a kansuNeh 9:1
Ayoyin
Neh 9:1A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, Isra’ilawa suka taru, suna yin azumi, suna sa rigunan makoki, suna kuma zuba toka a kansu.
- Ahab ya kece tufafinsa, ya sa tsummokin makoki ya kuma yi azumi1Sar 21:27
Ayoyin
1Sar 21:27Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai.
- An yi shelar azumi a Urushalima a zamanin YehohiyakimIrm 36:9
Ayoyin
Irm 36:9A watan tara na shekara ta biyar ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, an yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji ga dukan mutanen Urushalima da waɗanda suka zo daga garuruwan Yahuda.
- Sarki Dariyus ya kwana yana azumi yayinda Daniyel yake tare da zakokiDan 6:18
Ayoyin
Dan 6:18Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.
- Daniyel ya yi addu’a da azumi, da tsummokin makoki da tokaDan 9:3
Ayoyin
Dan 9:3Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.
- Daniyel bai ci abinci mai daɗi, nama ko ruwan inabi ba har mako ukuDan 10:2–3
Ayoyin
Dan 10:2–3A wannan lokaci ni Daniyel na yi makoki har na sati uku. Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.
- Ninebe ta yi azumi cikin tsummokin makoki — har da shanu da tumakiYun 3:5–8
Ayoyin
Yun 3:5–8Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki. Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka. Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi.
- Shawulu ya hana sojojinsa cin abinci kafin yamma1Sam 14:24
Ayoyin
1Sam 14:24A wannan rana, Isra’ilawa suka sha wahala ƙwarai domin Shawulu ya sa mutane suka yi rantsuwa cewa, “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana, kafin in ɗauki fansa a kan abokan gābana.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.
- Abokan gāban Bulus sun rantse ba za su ci ba sai sun kashe shiAyy M 23:12
Ayoyin
Ayy M 23:12Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus.
Kwana arba’in
- Musa kwana arba’in dare da rana ba burodi ba ruwaFit 34:28, M Sh 9:9, M Sh 9:18
Ayoyin
Fit 34:28Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.
M Sh 9:9Sa’ad da na hau kan dutse don in karɓi allunan dutse, allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutse yini arba’in da dare arba’in; ban ci abinci ba, ban sha ruwa ba.
M Sh 9:18Sai nan da nan kuma na fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji, yini arba’in da dare arba’in; ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda dā na yi, duka saboda zunubin da kuka aikata a gaban Ubangiji. Ta haka kuka tsokane shi don yă yi fushi.
- Iliya ya yi tafiya kwana arba’in da ƙarfin abinci guda1Sar 19:8
Ayoyin
1Sar 19:8Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah.
- Yesu ya yi azumi kwana arba’in dare da ranaMat 4:2
Ayoyin
Mat 4:2Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa.
Al’adu
- Ranar Kafara: “dole ku yi mūsu kanku”Fir 16:29
Ayoyin
Fir 16:29“Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare ku. A rana ta goma ga wata na bakwai, dole ku yi mūsu kanku, ba kuwa za ku yi wani aiki ba, ko da mutum baƙo ne a cikinku ko kuwa ɗan ƙasa,
- Azumi a wata na huɗu, na biyar, na bakwai da na gomaZak 7:5, Zak 8:19
Ayoyin
Zak 7:5“Ka tambayi dukan mutanen ƙasar da firistoci cewa, ‘Sa’ad da kuka yi makoki da azumi a wata na biyar da na bakwai dukan shekaru saba’in nan, a ainihi saboda ni kuka yi azumi?
Zak 8:19Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Azumin wata na huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai da na watan goma za su zama lokutan farin ciki da murna da kuma bukukkuwa na murna ga Yahuda. Saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.”
- Ishaya: azumin da yake tafiya tare da kyautata wa ma’aikataIsh 58:3–7
Ayoyin
Ish 58:3–7Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi, ba ka kuma gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, ba ka kuma lura da wannan ba?’ “Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata. Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi, kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe. Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau ku zaci za a ji muryarku can sama. Irin azumin da na zaɓa ke nan, rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa? Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai kuna kuma kwance a tsummoki da toka? Abin da kuke kira azumi ke nan rana yardajje ga Ubangiji? “Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya? Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?
- Anna ta yi sujada dare da rana, tana azumi tana addu’aLuk 2:37
Ayoyin
Luk 2:37ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.
- Wani Bafarisiye: “Ina azumi sau biyu a mako”Luk 18:12
Ayoyin
Luk 18:12Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’
- Me ya sa almajiran Yohanna suke azumi, amma almajiran Yesu ba sa yi?Mat 9:14–15
Ayoyin
Mat 9:14–15Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?” Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.
- Yesu: sa’ad da kuke azumi, ku wanke fuskarkuMat 6:16–18
Ayoyin
Mat 6:16–18“Sa’ad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. Amma sa’ad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka, domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
- Shawulu daga Tarshish bai ci ba bai kuma sha ba har kwana ukuAyy M 9:9
Ayoyin
Ayy M 9:9Kwana uku yana a makance, bai ci ba bai kuma sha kome ba.
- Ikkilisiya a Antiyok ta yi azumi kafin ta aiki Barnabas da ShawuluAyy M 13:2–3
Ayoyin
Ayy M 13:2–3Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.” Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.
- An naɗa dattawa da addu’a da azumiAyy M 14:23
Ayoyin
Ayy M 14:23Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.
- Bulus ya sha zama ba abinci2Kor 11:27
Ayoyin
2Kor 11:27Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.
- Tafiya a teku ta zama da hatsari bayan “Azumi”Ayy M 27:9
Ayoyin
Ayy M 27:9An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su,
- Abokan tafiyar Bulus a jirgi sun yi kwana goma sha huɗu ba abinciAyy M 27:33
Ayoyin
Ayy M 27:33Kafin gari ya waye Bulus ya roƙe su duka su ci abinci. Ya ce, “Kwana goma sha huɗu ke nan, kuna zama cikin zulumi kun kuma kasance ba abinci, ba ku ci kome ba.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.