Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Haihuwa da rashin haihuwa

Rayuwar yau da kullum

Haihuwa da rashin haihuwa a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (39), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Haihuwa

  • Mace mai naƙuda takan manta da zafin don farin cikin haihuwarYoh 16:21
    Ayoyin
    Yoh 16:21Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya.
  • Ungozoman Ibraniyawa Shofra da Fuwa, da kujerun haihuwaFit 1:15–16
    Ayoyin
    Fit 1:15–16Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce, “Sa’ad da kuke taimakon matan Ibraniyawa lokacin haihuwa, in jaririn namiji ne ku kashe shi, amma in ta mace ce, ku bar ta da rai.”
  • Matan Ibraniyawa “sukan haihu kafin ungozomomin su kai wurinsu”Fit 1:19
    Ayoyin
    Fit 1:19Ungozoman suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Ai, matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gwarzaye ne, sukan haihu kafin ungozomomin su kai wurinsu.”
  • Naƙudar Rahila ta yi wuya; ungozomar ta ce, “kin sami wani ɗa”Far 35:16–17
    Ayoyin
    Far 35:16–17Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai. Sa’ad da take cikin zafin haihuwa, sai macen da ta karɓi haihuwar ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”
  • Rahila ta mutu a hanya zuwa BetlehemFar 35:18–19
    Ayoyin
    Far 35:18–19Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin. Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem).
  • Matar Finehas ta haihu da ta ji labarin, ta kuma mutu1Sam 4:19–20
    Ayoyin
    1Sam 4:19–20Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta. Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.
  • Bayan ɗa namiji, uwa takan zama marar tsarki kwana bakwai, sa’an nan ta jira a tsabtace taFir 12:2–4
    Ayoyin
    Fir 12:2–4“Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta. A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya. Sa’an nan dole macen ta jira kwana talatin don a tsabtacce ta daga zub da jini. Ba za tă taɓa wani abu mai tsarki, ko ta je wuri mai tsarki ba sai kwanakin tsabtaccewarta sun cika.
  • Bayan ’ya mace, mako biyu marar tsarki, sa’an nan tsabtacewa mafi tsawoFir 12:5
    Ayoyin
    Fir 12:5In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta.
  • Sa’an nan akan miƙa ɗan rago da tsuntsu, ko tsuntsaye biyu in ita matalauciya ceFir 12:6, Fir 12:8
    Ayoyin
    Fir 12:6“ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi.
    Fir 12:8In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’ ”
  • Maƙwabtan Elizabet da danginta sun yi farin ciki tare da itaLuk 1:57–58
    Ayoyin
    Luk 1:57–58Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.

Masu reno

  • Mai renon Rebeka ta tafi tare da ita zuwa Kan’anaFar 24:59
    Ayoyin
    Far 24:59Saboda haka suka sallame Rebeka, ’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa.
  • Saratu: “wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara?”Far 21:7
    Ayoyin
    Far 21:7Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”
  • Musa: “in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri”Ƙid 11:12
    Ayoyin
    Ƙid 11:12Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu?
  • Bulus: mai taushi, kamar uwa mai shayarwa da take kula da ’ya’yanta1Tes 2:7
    Ayoyin
    1Tes 2:7amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta.

Waɗanda suka daɗe ba ’ya’ya

  • Saira bakararriya ce; ba ta da ’ya’yaFar 11:30
    Ayoyin
    Far 11:30Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.
  • Saira ta ba Abram baiwarta Hagar don ta sami iyaliFar 16:1–2
    Ayoyin
    Far 16:1–2To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar, saboda haka sai ta ce wa Abram, “ Ubangiji ya hana mini haihuwar ’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.” Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa.
  • Saratu ta yi dariya: ta wuce shekarun haihuwaFar 18:11–14
    Ayoyin
    Far 18:11–14Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa. Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, “Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?” Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’ Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.”
  • Saratu ta haifi Ishaku; Ibrahim yana da shekara ɗariFar 17:17, Far 21:2, Far 21:5
    Ayoyin
    Far 17:17Ibrahim ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, ya yi dariya, ya ce wa kansa, “Za a haifi ɗa wa mutum mai shekaru ɗari? Saratu za tă haifi ɗa tana da shekaru tasa’in?”
    Far 21:2Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari.
    Far 21:5Ibrahim yana da shekara ɗari, sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.
  • Ishaku ya yi addu’a domin Rebeka bakararriya, ta kuma yi cikiFar 25:21
    Ayoyin
    Far 25:21Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki.
  • Rahila: “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!”Far 30:1–2
    Ayoyin
    Far 30:1–2Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!” Yaƙub ya fusata da ita ya ce, “Ina a matsayin Allah ne wanda ya hana ke samun ’ya’ya?”
  • Rahila da Liyatu sun yi ciniki game da manta-uwaFar 30:14–16
    Ayoyin
    Far 30:14–16A lokacin girbin alkama, sai Ruben ya je jeji ya ɗebo manta-uwa ya kawo wa mahaifiyarsa Liyatu. Sai Rahila ta ce wa Liyatu, “Ina roƙonki ki ɗan sam mini manta-uwa ɗanki.” Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?” Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.” Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare.
  • Rahila ta haifi Yusuf: “Allah ya ɗauke mini kunyata”Far 30:22–24
    Ayoyin
    Far 30:22–24Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta. Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.” Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”
  • Matar Manowa, bakararriya, ta haifi SamsonMah 13:2–3, Mah 13:24
    Ayoyin
    Mah 13:2–3Akwai wani mutumin Zora, mai suna Manowa, daga kabilar Dan, matarsa kuwa bakararriya ce, ba ta haihuwa. Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa.
    Mah 13:24Matar kuwa ta haifi ɗa, aka sa masa suna Samson. Ya yi girma Ubangiji kuma ya albarkace shi,
  • Elkana ya ba Hannatu marar ɗa rabo biyu1Sam 1:2, 1Sam 1:5
    Ayoyin
    1Sam 1:2Yana da mata biyu, ɗaya sunanta Hannatu, ɗayan kuwa ana kiranta Feninna. Ita Feninna tana da ’ya’ya, amma Hannatu ba ta da ’ya’ya.
    1Sam 1:5Amma Hannatu kuwa sai yă ba ta babban rabo gama yana ƙaunarta ko da yake Ubangiji ya kulle mahaifarta.
  • Feninna tana tsokanar Hannatu shekara bayan shekara1Sam 1:6–7
    Ayoyin
    1Sam 1:6–7Saboda Ubangiji ya kulle mahaifarta, sai kishiyarta ta dinga tsokanarta don tă ba ta haushi. Wannan ya ci gaba shekara da shekaru. Duk lokacin da Hannatu ta haura zuwa haikalin Ubangiji, sai kishiyarta tă tsokane ta har tă yi ta kuka tă kuma ƙi cin abinci.
  • Hannatu ta yi kuka ta yi wa’adi; ta haifi Sama’ila1Sam 1:10–11, 1Sam 1:19–20
    Ayoyin
    1Sam 1:10–11A cikin baƙin ciki, Hannatu ta yi kuka mai zafi ta yi addu’a ga Ubangiji. Ta yi ta cewa, “Ya Ubangiji Maɗaukaki. In har ka dubi baƙin cikin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuma manta da baiwarka ba, amma ka ba ta ɗa, ni ma zan miƙa shi ga Ubangiji dukan rayuwarsa, aska kuwa ba za tă taɓa kansa ba.”
    1Sam 1:19–20Kashegari da sassafe suka tashi suka yi sujada a gaban Ubangiji, sai suka koma garinsu a Rama. Elkana kuwa ya kwana da matarsa Hannatu, Ubangiji kuma ya tuna da ita. Ana nan sai Hannatu ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Ta ba shi suna Sama’ila; tana cewa, “Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji.”
  • Daga baya Hannatu ta sami ƙarin ’ya’ya1Sam 2:21
    Ayoyin
    1Sam 2:21Hannatu kuwa ta sami alfarma daga Ubangiji. Ta yi ciki. Ana cikin haka Sama’ila kuwa sai girma yake ta yi a gaban Ubangiji.
  • Matar Shunam, wadda mijinta tsoho ne, ta sami ɗa a shekara mai zuwa2Sar 4:14–17
    Ayoyin
    2Sar 4:14–17Sai Elisha ya tambayi Gehazi ya ce, “Me za mu yi mata?” Sai ya amsa ya ce, “Ba ta da ɗa, ga shi kuma mijinta ya tsufa.” Sai Elisha ya ce, “Ka kira ta.” Sai ya kira ta, ta zo ta tsaya a bakin ƙofa. Elisha ya ce mata, “War haka baɗi, za ki riƙe ɗa na kanki.” Sai ta ce masa, “A’a, ranka yă daɗe, mutumin Allah, kada ka ruɗi baiwarka!” Amma matan ta yi ciki, a shekara ta biye kuwa a daidai lokacin, sai ta haifi ɗa kamar yadda Elisha ya faɗa mata.
  • Mikal ba ta haifi ɗa ba har mutuwarta2Sam 6:23
    Ayoyin
    2Sam 6:23Mikal ’yar Shawulu kuwa ba tă haifi ɗa ba har mutuwarta.
  • Elizabet, bakararriya kuma tsohuwa, ta yi ciki ta kuma ɓoye kanta wata biyarLuk 1:7, Luk 1:24–25, Luk 1:36
    Ayoyin
    Luk 1:7Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa.
    Luk 1:24–25Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar. Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.”
    Luk 1:36’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida.
  • Yakan zaunar da bakararriya a gidanta kamar uwa mai farin cikiZab 113:9
    Ayoyin
    Zab 113:9Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.