Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Binnewa da kaburbura

Rayuwar yau da kullum

Binnewa da kaburbura a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (42), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Akan binne matattu da sauri, sau da yawa a ranarM Sh 21:23, Ayy M 5:6, Ayy M 5:10
    Ayoyin
    M Sh 21:23kada ku bar jikinsa a kan itacen yă kwana. Ku tabbata kun binne shi a ranar, domin duk wanda aka rataye a kan itace la’ananne ne ga Allah. Kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo.
    Ayy M 5:6Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne.
    Ayy M 5:10Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta.
  • Akan ƙuna wuta don girmama sarakunan da suka mutuIrm 34:5
    Ayoyin
    Irm 34:5za ka mutu cikin salama. Yadda mutane suka ƙuna wutar jana’iza don girmama kakanninka, sarakunan da suka riga ka, haka za su ƙuna wuta don girmama da kuma makokinka suna cewa, “Kaito, ya maigida!” Ni kaina na yi wannan alkawari, in ji Ubangiji.’ ”
  • Sarki Dawuda ya bi makarar Abner ya yi kuka a kabarinsa2Sam 3:31–32
    Ayoyin
    2Sam 3:31–32Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya. Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner.
  • A Nayin babban taro yana bin ɗa tilo na wata gwauruwa zuwa kabariLuk 7:12
    Ayoyin
    Luk 7:12Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita.

Jana’iza

  • Dattawan Fir’auna, kekunan yaƙi da mahayan dawakai sun haura don su binne YaƙubFar 50:7–9
    Ayoyin
    Far 50:7–9Saboda haka Yusuf ya haura don yă binne mahaifinsa. Dukan hafsoshin Fir’auna suka yi masa rakiya tare da manyan mutanen gidan Fir’auna, da kuma dukan manyan mutanen Masar da kuma dukan membobin gidan Yusuf, da ’yan’uwansa da kuma waɗanda suke na gidan mahaifinsa. Yara kaɗai da garkunansu da kuma shanunsu ne aka bari a Goshen. Kekunan yaƙi da mahayan dawakai su ma suka haura tare da shi. Babbar ƙungiya jama’a ce ƙwarai.
  • Ishaku da Ishmayel sun binne Ibrahim; Isuwa da Yaƙub sun binne IshakuFar 25:9, Far 35:29
    Ayoyin
    Far 25:9’Ya’yansa maza kuwa Ishaku da Ishmayel suka binne shi cikin kogon Makfela, kusa da Mamre, a cikin filin Efron ɗan Zohar mutumin Hitti,
    Far 35:29sa’an nan ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuwa mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa da kyakkyawan tsufa da kuma cikakken shekaru. ’Ya’yansa maza, Isuwa da Yaƙub suka binne shi.
  • Dukan Isra’ila sun yi makokin Sama’ila suka binne shi a gidansa a Rama1Sam 25:1, 1Sam 28:3
    Ayoyin
    1Sam 25:1Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran.
    1Sam 28:3Sama’ila dai ya riga ya rasu, dukan Isra’ila suka yi makokinsa suka binne shi a garinsa a Rama. Shawulu kuma ya kori duk masu duba da masu maitanci daga ƙasar.
  • Mutanen Yabesh sun yi tafiya dukan dare don su ɗauko gawar Shawulu1Sam 31:11–13
    Ayoyin
    1Sam 31:11–13Sa’ad da mutanen Yabesh Gileyad suka sami labarin abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu. Sai dukan jarumawansu suka tashi cikin dare suka tafi Bet-Shan suka saukar da gawar Shawulu da na ’ya’yansa daga kan katangan Bet-Shan suka tafi Yabesh inda suka ƙone su. Sai suka kwashi ƙasusuwansu suka binne a gindin itace tsamiya a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
  • Dawuda ya kwashe ƙasusuwan Shawulu da Yonatan zuwa kabarin Kish2Sam 21:12–14
    Ayoyin
    2Sam 21:12–14sai ya je ya kwashe ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga mutanen Yabesh Gileyad (Gama mutanen sun saci gawawwakin Shawulu da Yonatan daga inda Filistiyawa suka kakkafa su a kan itace a filin Bet-Shan, bayan da Filistiyawa suka kashe su a Gilbowa.) Dawuda ya kawo ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga can, a kuma aka tattara dukan ƙasusuwan waɗanda Gibeyonawan suka kashe, suka kuma rataye. Suka binne ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan a kabarin Kish, mahaifin Shawulu, a Zela a Benyamin. Suka kuma yi kome da sarki ya umarta. Bayan wannan Allah ya ji addu’arsu a madadin ƙasar.
  • Mutane masu tsoron Allah sun binne Istifanus suka yi makoki ƙwarai saboda shiAyy M 8:2
    Ayoyin
    Ayy M 8:2Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.

Burin game da binnewa

  • Yaƙub ya roƙa a binne shi tare da kakanninsa, ba a Masar baFar 47:30, Far 49:29–32
    Ayoyin
    Far 47:30amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.” Yusuf ya ce, “Zan yi yadda ka faɗa.”
    Far 49:29–32Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti, kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu. Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.”
  • Yusuf ya sa Isra’ilawa suka rantse za su kwashe ƙasusuwansa daga MasarFar 50:25
    Ayoyin
    Far 50:25Yusuf kuwa ya sa ’ya’yan Isra’ila maza suka yi rantsuwa, ya kuma ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, ku kuma dole ku ɗauki ƙasusuwana, ku haura da su daga wannan wuri.”
  • Barzillai yana so ya mutu kusa da kabarin mahaifinsa da mahaifiyarsa2Sam 19:37
    Ayoyin
    2Sam 19:37Ka bar bawanka yă koma, don in mutu a garina, kusa da kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ga bawanka Kimham. Bari yă ƙetare tare da ranka yă daɗe, sarki. Ka yi abin da ka ga dama da shi.”
  • Wani tsohon annabi ya roƙa a binne shi kusa da mutumin Allah1Sar 13:30–31
    Ayoyin
    1Sar 13:30–31Sai ya kwantar da gawar a kabarinsa, suka yi makoki a kansa, ya kuma ce, “Ayya, abokina!” Bayan an binne shi, sai ya ce wa ’ya’yansa, “Sa’ad da na mutu, ku binne ni a kabarin da aka binne mutumin Allah; ku kwantar da ƙasusuwana kusa da ƙasusuwansa.

Kaburbura da wuraren binnewa

  • Ibrahim ya sayi kogon Makfela da shekel ɗari huɗu na azurfaFar 23:16–20
    Ayoyin
    Far 23:16–20Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin. Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin. Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana. Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta.
  • Yaƙub ya kafa ginshiƙi a kan kabarin Rahila a hanya zuwa BetlehemFar 35:19–20
    Ayoyin
    Far 35:19–20Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem). Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.
  • An binne su a ƙarƙashin itatuwa: Debora a ƙarƙashin oak, Shawulu a ƙarƙashin tsamiyaFar 35:8, 1Sam 31:13
    Ayoyin
    Far 35:8To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.
    1Sam 31:13Sai suka kwashi ƙasusuwansu suka binne a gindin itace tsamiya a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
  • An binne sarakunan Yahuda a Birnin Dawuda1Sar 2:10, 2Tar 32:33
    Ayoyin
    1Sar 2:10Sa’an nan Dawuda ya huta tare da kakanninsa. Sai aka binne shi a Birnin Dawuda.
    2Tar 32:33Hezekiya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a kan tudu inda makabartan zuriyar Dawuda suke. Dukan Yahuda da kuma mutanen Urushalima suka girmama shi sa’ad da ya mutu. Sai Manasse ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
  • An binne firist Yehohiyada tare da sarakuna2Tar 24:16
    Ayoyin
    2Tar 24:16Aka binne shi tare da sarakuna a cikin Birnin Dawuda, saboda kirkin da ya yi a Isra’ila wa Allah da haikalinsa.
  • An binne Yowash da Yehoram, amma ba a kaburburan sarakuna ba2Tar 24:25, 2Tar 21:20
    Ayoyin
    2Tar 24:25Sa’ad da Arameyawa suka janye, suka bar Yowash da mummunan rauni. Hafsoshinsa suka haɗa baki a kansa saboda kisan ɗan Yehohiyada firist da ya yi, suka kashe shi a kan gadonsa. Ta haka ya mutu aka kuma binne shi makabartan sarakuna.
    2Tar 21:20Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas. Ya mutu, ba ma wanda ya kula, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda, amma ba a makabartan sarakuna ba.
  • An binne Uzziya, kuturu, a wani fili kusa da kaburburan sarakuna2Tar 26:23
    Ayoyin
    2Tar 26:23Uzziya ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi kusa da su a fili don binnewar da take ta sarakuna, domin mutane sun ce, “Yana da kuturta.” Sai Yotam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
  • An binne Manasse da Amon a lambun Uzza2Sar 21:18, 2Sar 21:26
    Ayoyin
    2Sar 21:18Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a lambun fadansa, lambun Uzza. Sai Amon ɗansa ya gāje shi.
    2Sar 21:26Aka binne shi a kabarinsa a lambun Uzza. Yosiya ɗansa kuma ya gāje shi.
  • An binne Yowab a gidansa a jeji1Sar 2:34
    Ayoyin
    1Sar 2:34Sai Benahiya ɗan Yehohiyada ya haura ya bugi Yowab, ya kashe shi, ya kuwa binne shi a gidansa a ƙauye.
  • Yosiya ya ga kaburbura a gefen tudu da wata alama a kan ɗaya2Sar 23:16–17
    Ayoyin
    2Sar 23:16–17Da Yosiya ya dubi kewaye da shi, ya ga kaburburan da suke can a gefen tudu, sai ya sa aka kwaso ƙasusuwan da suke cikinsu aka ƙone a kan bagade don yă lalatar da shi bisa ga maganar Ubangiji ta bakin mutumin Allah, wanda ya yi annabcin waɗannan abubuwa. Sarkin ya yi tambaya, ya ce, “Wane kabari ke nan nake gani?” Mutanen birnin suka ce, “Ai, kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuda, shi ne ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.”
  • An kwantar da Yesu a sabon kabari a wani lambu kusa da wurin gicciyeYoh 19:41–42
    Ayoyin
    Yoh 19:41–42A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba. Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.
  • Matan suna mamakin wa zai mirgine babban dutse daga kabarinMar 16:3–4
    Ayoyin
    Mar 16:3–4sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?” Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne.
  • An sayi filin maginin tukwane ya zama makabartar baƙiMat 27:7
    Ayoyin
    Mat 27:7Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi.
  • An jefar da gawar Uriya a makabartar talakawaIrm 26:23
    Ayoyin
    Irm 26:23Suka dawo da Uriya daga Masar suka kawo shi wurin Sarki Yehohiyakim, wanda ya kashe shi da takobi aka kuma jefar da gawarsa a makabartar talakawa.)
  • An jefar da Absalom cikin rami a ƙarƙashin babban tarin duwatsu2Sam 18:17
    Ayoyin
    2Sam 18:17Suka ɗauki Absalom, suka jefa shi cikin wani babban rami a kurmin, suka kuwa tula tsibin duwatsu a kansa. Ana cikin haka, sai dukan Isra’ilawa suka tsere zuwa gidajensu.
  • Ba wanda ya san inda kabarin Musa yakeM Sh 34:6
    Ayoyin
    M Sh 34:6Aka binne shi a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake.
  • Wani mutum mai aljanu yana zama cikin kaburburaMar 5:3, Luk 8:27, Mat 8:28
    Ayoyin
    Mar 5:3Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma.
    Luk 8:27Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura.
    Mat 8:28Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.