Rayuwar yau da kullum
Abinci a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (38), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Abin da mutane suke ci
- Madarar awaki domin iyaliK Mag 27:27
Ayoyin
K Mag 27:27Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.
- Kindirmo, madara, kitsen ’yan raguna da alkama mafi kyauM Sh 32:14
Ayoyin
M Sh 32:14da kindirmo da madara daga shanu da tumaki da ƙibabbun tumaki da awaki, da zaɓaɓɓun ragunan Bashan da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa.
- Cuku goma domin shugaban sojoji1Sam 17:17–18
Ayoyin
1Sam 17:17–18Yesse ya ce wa ɗansa Dawuda, “Ka ɗauki wannan gasasshen hatsi da waɗannan curin burodi goma, ka kai wa ’yan’uwanka a sansani da sauri. Ka haɗa da waɗannan cuku guda goma, ka kai wa komandan rundunarsu. Ka ga lafiyar ’yan’uwanka, ka kawo mini labari daga wurinsu.
- Alkama, sha’ir, wake, waken lentil, zuma da cuku domin mutanen Dawuda2Sam 17:28–29
Ayoyin
2Sam 17:28–29suka kawo wa Dawuda da mutanensa tabarmai, da kwanoni, da kayayyakin da aka yi da yumɓu. Suka kuma kawo alkama da sha’ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa, da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu wa Dawuda da mutanensa su ci. Gama sun ce, “Mutanen suna jin yunwa, sun kuma gaji, ga ƙishirwa a hamada.”
- Ibrahim ya ba da burodi, ɗan maraƙi mai taushi, kindirmo da madaraFar 18:5–8
Ayoyin
Far 18:5–8Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.” Suka ce, “To, sai ka yi abin da ka ce.” Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.” Sa’an nan Ibrahim ya yi gudu zuwa garkensa, ya zaɓi ɗan maraƙi ya ba wa bawansa, bawansa kuma ya yi sauri ya gyara shi. Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.
- Rut ta tsoma burodi a cikin ruwan tsami ta ci gasasshen hatsiRut 2:14
Ayoyin
Rut 2:14A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.
- Burodi, wainar dabino da wainar zabibi ga kowa2Sam 6:19
Ayoyin
2Sam 6:19Sa’an nan ya rarraba abinci, da ƙosai, dabino, da waina ga kowane mutum a cikin dukan jama’ar Isra’ila, maza da mata. Dukan mutane kuwa suka watse zuwa gidajensu.
- Abigiyel ta kawo burodi, ruwan inabi, tumaki, zabibi da wainar ɓaure1Sam 25:18
Ayoyin
1Sam 25:18Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna.
- Ziba ya kawo wa Dawuda burodi, busasshen inabi da kosan ’ya’yan itace ɓaure2Sam 16:1–2
Ayoyin
2Sam 16:1–2Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi. Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?” Ziba ya ce, “Jakuna domin iyalin gidan sarki su hau ne, burodi da ’ya’yan itace domin mutane su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suka gaji a hamada.”
- Wani Bamasare da yunwa ta kusan kashe ya farfaɗo da wainar ɓaure da zabibi1Sam 30:11–12
Ayoyin
1Sam 30:11–12Suka sami wani mutumin Masar a fili suka kawo shi wurin Dawuda. Suka ba shi abinci ya ci, suka kuma ba shi ruwa ya sha. Suka ba shi saura wainan ’ya’yan ɓaure da kuma wainan ’ya’yan inabi, ya ci ya sami ƙarfi. Gama bai ci ba, bai sha ba, har yini uku da dare uku.
- Kifi, kokwamba, guna, kabewa, albasa da tafarnuwa a MasarƘid 11:5
Ayoyin
Ƙid 11:5Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, haka ma kayan lambu irin su kukumba, guna, safa, albasa da kuma tafarnuwa.
- Burodi da miyar waken lentilFar 25:34
Ayoyin
Far 25:34Sa’an nan Yaƙub ya ba wa Isuwa burodi da ɗan miyan lansir. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya tashi ya tafi. Ta haka Isuwa ya yi banza da matsayinsa na ɗan fari.
- Manna yana da ɗanɗano kamar wainar da aka yi da zumaFit 16:31
Ayoyin
Fit 16:31Mutanen Isra’ila suka kira burodin Manna. Manna yana nan fari kamar farin riɗi, ɗanɗanonsa kuma yana kama da masa da aka yi da zuma.
- Gasasshen hatsin ƙasar; sa’an nan manna ya daina zuwaYosh 5:11–12
Ayoyin
Yosh 5:11–12A kashegarin Bikin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, burodi marar yisti da hatsin da aka gasa. Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, Manna ta yanke, mutanen Isra’ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan’ana.
- Burodin alkama, sha’ir, wake, waken lentil, gero da maiwaEzk 4:9
Ayoyin
Ezk 4:9“Ka ɗauki alkama da sha’ir, wake da acca, gero da maiwa; ka sa su a tulun ajiya ka kuma yi amfani da su don yin burodi wa kanka. Za ka ci shi a kwanaki 390 da za ka kwanta a gefenka.
- Daniyel ya roƙa a ba su ganye da ruwa kawaiDan 1:12
Ayoyin
Dan 1:12“Ina roƙonka ka gwada bayinka kwana goma. Kada ka ba mu kome sai kayan lambu mu ci da kuma baƙin ruwa mu sha.
- Hankaki sun kawo wa Iliya burodi da nama safe da yamma1Sar 17:6
Ayoyin
1Sar 17:6Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin.
- Yohanna Mai Baftisma yakan ci fāra da zumar jejiMat 3:4
Ayoyin
Mat 3:4Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji.
- Gara ɗan ganye inda akwai ƙauna da sa mai ƙibaK Mag 15:17
Ayoyin
K Mag 15:17Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.
- Ɗa yakan roƙi burodi ko kifiMat 7:9–10
Ayoyin
Mat 7:9–10“Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji?
- Kifi da burodi a kan garwashin wuta a bakin tafkiYoh 21:9
Ayoyin
Yoh 21:9Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.
- Yesu da ya tashi ya ci gasasshen kifiLuk 24:42
Ayoyin
Luk 24:42Suka ba shi ɗan gasasshen kifi,
A teburin abinci
- Rebeka ta shirya abinci mai daɗi daga ’yan awaki biyuFar 27:9
Ayoyin
Far 27:9Je garke ka kawo mini awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi wa mahaifinka, kamar yadda dai yake so.
- Mata sukan yi aiki a matsayin masu dafa abinci da masu toya burodi1Sam 8:13, K Mag 31:15
Ayoyin
1Sam 8:13Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye.
K Mag 31:15Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
- Masarawa ba sa cin abinci tare da IbraniyawaFar 43:32
Ayoyin
Far 43:32Sai aka raba musu abinci, nasa shi kaɗai su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sa cin abinci tare da Ibraniyawa, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa.
- Ana godiya kafin a gutsuttsura burodiMar 8:6, Luk 24:30, Ayy M 27:35
Ayoyin
Mar 8:6Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka.
Luk 24:30Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su.
Ayy M 27:35Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci.
- An rera waƙa bayan Jibin ƘarsheMat 26:30
Ayoyin
Mat 26:30Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
Abincin da aka hana
- Dabbobin ƙasa: sai masu rababben kofato da masu tuƙa kawaiFir 11:3–4
Ayoyin
Fir 11:3–4Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa. “ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku.
- Halittun ruwa: sai masu ƙege da kamɓori kawaiFir 11:9–10
Ayoyin
Fir 11:9–10“ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori. Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku.
- Ba za a ci gaggafa, ungulu da sauran tsuntsayen da aka lissafa baFir 11:13
Ayoyin
Fir 11:13“ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu,
- Ana iya cin fāra, gyare, ƙwanso da danginsuFir 11:21–22
Ayoyin
Fir 11:21–22Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle. Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu.
- Akan zubar da jini a rufe shi da ƙasaFir 17:13–14
Ayoyin
Fir 17:13–14“ ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa, domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.”
- Ba a cin naman dabbar da namun jeji suka kashe a filiFit 22:31
Ayoyin
Fit 22:31“Za ku kasance mutanena masu tsarki. Saboda kada ku ci naman da namun jeji suka kashe; ku jefa wa karnuka.
- Kada ka dafa ɗan akuya cikin madarar mahaifiyarsaFit 23:19, M Sh 14:21
Ayoyin
Fit 23:19“Dole ne ku kawo mafi kyau daga nunan fari na gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.
M Sh 14:21Kada ku ci abin da kun samu ya riga ya mutu. Za ku iya ba wa baren da yake zama a cikin wani daga biranenku, zai kuwa iya cinsa, ko kuwa za ku iya sayar da shi wa baƙo. Amma ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madara mamansa.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.