Rayuwar yau da kullum
Cin hanci a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (27), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Kada ka karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makantar da idanuFit 23:8, M Sh 16:19
Ayoyin
Fit 23:8“Kada ka karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta waɗanda suke gani, yakan kuma karkatar da maganar masu adalci.
M Sh 16:19Kada ku ɓata shari’a, ko ku nuna bambanci. Kada ku karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta idanu mai hikima, yă murɗe maganar mai gaskiya.
- La’ananne ne wanda ya karɓi cin hanci don ya kashe marar laifiM Sh 27:25
Ayoyin
M Sh 27:25“La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
- Sama’ila: “Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku?”1Sam 12:3
Ayoyin
1Sam 12:3Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”
- Sarki Yehoshafat ga alƙalansa: ba son kai ko cin hanci2Tar 19:7
Ayoyin
2Tar 19:7Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”
- Wa zai zauna tare da Allah? Wanda ya ƙi cin hanciZab 15:5, Ish 33:15
Ayoyin
Zab 15:5wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.
Ish 33:15Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,
- Maganganu a Karin Magana: kyauta takan buɗe hanya; kyauta a ɓoye takan kwantar da fushiK Mag 17:8, K Mag 18:16, K Mag 21:14
Ayoyin
K Mag 17:8Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara.
K Mag 18:16Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.
K Mag 21:14Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.
- Wanda yake ƙin cin hanci zai rayuK Mag 15:27
Ayoyin
K Mag 15:27Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.
- Cin hanci yakan ɓata zuciyaM Had 7:7
Ayoyin
M Had 7:7Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa, cin hanci kuma yakan lalace hali.
- Annabawa sun zargi shugabanni da alƙalai masu son cin hanciIsh 1:23, Ish 5:23, Mik 3:11, Mik 7:3, Amos 5:12
Ayoyin
Ish 1:23Masu mulkinki ’yan tawaye ne, abokan ɓarayi; dukansu suna ƙaunar cin hanci suna bin kyautai. Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a; ba sa taimakon gwauruwa.
Ish 5:23waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci, amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.
Mik 3:11Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne, firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su, annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa, “Ba Ubangiji yana tare da mu ba? Ba bala’in da zai zo mana.”
Mik 7:3Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta; shugabanni suna nema a ba su kyautai, alƙalai suna nema a ba su cin hanci, masu iko suna faɗar son zuciyarsu, duk suna ƙulla makirci tare.
Amos 5:12Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.
Misalai
- ’Ya’yan Sama’ila maza suna cin hanci suna kuma karkatar da shari’a1Sam 8:3
Ayoyin
1Sam 8:3Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.
- Sarakunan Filistiyawa sun yi wa Delila alkawarin azurfa don ta ci amanar SamsonMah 16:5
Ayoyin
Mah 16:5Sai shugabannin Filistiyawa suka tafi wurinta suka ce, “Ki yi ƙoƙari ki ga ko za ki rarrashe shi yă nuna miki asirin ƙarfinsa da yadda za mu iya shan ƙarfinsa don mu ɗaura shi mu yi nasara a kansa. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu ɗari ɗaya na azurfa.”
- Asa ya aika wa Ben-Hadad da azurfa da zinariyar haikali1Sar 15:18–19
Ayoyin
1Sar 15:18–19Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”
- Ahaz ya aika wa sarkin Assuriya da azurfa da zinariyar haikali2Sar 16:8
Ayoyin
2Sar 16:8Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyar da suke a haikalin Ubangiji da suke kuma a ma’ajin fada ya aika wa sarkin Assuriya kyauta.
- An yi hayar mashawarta don su hana sāke gina haikaliEzr 4:5
Ayoyin
Ezr 4:5Suka yi hayar mashawarta don su ga cewa sun ɓata ƙoƙarinsu dukan kwanakin mulkin Sairus sarkin Farisa har zuwa kwanakin mulkin Dariyus sarkin Farisa.
- An yi hayar Shemahiya don ya tsorata Nehemiya ya ɓuya a haikaliNeh 6:10–13
Ayoyin
Neh 6:10–13Wata rana na tafi gidan Shemahiya ɗan Delahiya, ɗan Mehetabel, wanda aka hana fita a gidansa. Ya ce mini, “Mu sadu gobe a gidan Allah, a cikin haikali, mu kuma kulle ƙofofin haikali, gama mutane suna zuwa su kashe ka, tabbatacce za su zo da dare su kashe ka.” Amma na ce, “Ya kamata mutum kamar ni yă gudu? Ko kuwa ya kamata wani kamar ni yă shiga cikin haikali don yă ceci ransa? Ba zan tafi ba!” Na gane cewa Allah bai aike shi ba, ya yi annabci a kaina domin Tobiya da Sanballat sun yi hayarsa ne. An yi hayarsa don yă sa in ji tsoro in yi zunubi ta yin haka, sa’an nan za su ba ni mugun suna, su wofinta ni.
- Haman ya yi alkawarin talenti dubu goma saboda doka a kan YahudawaEsta 3:9
Ayoyin
Esta 3:9In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.”
- Manyan firistoci sun biya Yahuda azurfa talatinMat 26:15
Ayoyin
Mat 26:15ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.
- An biya sojoji kuɗi don su ce almajirai sun sace jikinMat 28:12–15
Ayoyin
Mat 28:12–15Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa. Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’ In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.” Sai sojojin suka karɓi kuɗin, suka kuma yi kamar yadda aka umarce su. Wannan labarin kuwa shi ne ake bazawa ko’ina a cikin Yahudawa, har yă zuwa yau.
- Gwamna Felis yana sa rai Bulus zai ba shi cin hanciAyy M 24:26
Ayoyin
Ayy M 24:26A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.