Rayuwar yau da kullum
Gwauraye a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (37), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
A cikin Doka
- Kada ku wulaƙanta gwauruwa ko marayaFit 22:22–24
Ayoyin
Fit 22:22–24“Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya. In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu. Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu.
- Dammunan da aka manta, zaitun da inabi ana bar su domin gwauruwaM Sh 24:19–21
Ayoyin
M Sh 24:19–21Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku. Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa. Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.
- Zakkar kowace shekara ta uku tana ciyar da gwauruwa, maraya da baƙoM Sh 14:28–29
Ayoyin
M Sh 14:28–29A ƙarshen kowace shekara uku, ku kawo dukan zakkarku na amfanin gona na wannan shekara, ku ajiye su a cikin birane, saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku.
- Gwauraye suna shiga farin cikin bukukuwaM Sh 16:11, M Sh 16:14
Ayoyin
M Sh 16:11Ku kuma yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawan cikin biranenku, har ma da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikinku.
M Sh 16:14Ku yi farin ciki a Bikinku, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawa, da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikin biranenku.
- Kada ka karɓi mayafin gwauruwa jinginaM Sh 24:17
Ayoyin
M Sh 24:17Ba za ku danne hakkin baƙon da yake zama a cikinku ko na marayu ba, ba za ku ɗauki rigar matar da mijinta ya mutu a matsayin jingina ba.
- Wa’adin gwauruwa yana ɗaure taƘid 30:9
Ayoyin
Ƙid 30:9“Duk wani alkawari ko rantsuwar da gwauruwa, ko macen da aurenta ya mutu, ta yi, zai tabbata a kanta.
- ’Yar firist gwauruwa marar ɗa tana iya ci a teburin mahaifintaFir 22:13
Ayoyin
Fir 22:13Amma idan ’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da ’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin.
- Babban firist ba zai auri gwauruwa baFir 21:14
Ayoyin
Fir 21:14Ba zai auri matan da mijinta ya mutu, ko macen da mijinta ya rabu da ita, ko macen da ta ɓata kanta ta wurin karuwanci ba, sai dai yă auri budurwa daga cikin mutanensa,
- Ɗan’uwa yakan auri gwauruwar ɗan’uwansa da ya mutu babu ɗaM Sh 25:5–10
Ayoyin
M Sh 25:5–10In ’yan’uwa suna zama tare, in ɗayansu ya mutu babu ɗa, kada gwauruwar tă yi aure waje da iyalin. Ɗan’uwan mijinta zai ɗauke ta, yă aure ta, yă kuma cika abin da yă kamaci ɗan’uwan miji yă yi. Ɗan farin da ta haifa zai ɗauki sunan ɗan’uwan da ya rasu saboda kada sunansa yă ɓace daga Isra’ila. Amma fa, in mutum ba ya so yă auri matar ɗan’uwansa, sai tă tafi wurin dattawa a ƙofar gari tă ce, “Ɗan’uwan mijina ya ƙi yă wanzar da sunan ɗan’uwansa a Isra’ila. Ya ƙi yă cika abin da ya kamaci ɗan’uwan miji yă yi gare ni.” Sai dattawan garinsa su kira shi, su kuma yi masa magana. In ya nace yana cewa, “Ba na so in aure ta,” sai gwauruwan nan, matar ɗan’uwansa tă haura wurinsa a gaban dattawa, tă tuɓe takalminsa guda, ta tofa masa miyau a fuska, tă ce, “Haka za a yi ga mutumin da zai ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.” Za a kira zuriyarsa a Isra’ila Iyalin da aka tuɓe masa takalmi.
Maganganu
- Allah shi ne “mai kāre gwauraye”Zab 68:5, Zab 146:9
- Annabawa: ku kāre hakkin gwauruwaIsh 1:17, Irm 22:3, Zak 7:10
Ayoyin
Ish 1:17Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci. Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta. Ku ba wa marayu hakkinsu, ku taimaki gwauruwa.
Irm 22:3Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.
Zak 7:10Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’
- Ayuba: “Na faranta wa gwauruwa zuciya”Ayu 29:13, Ayu 31:16
- Yesu ya yi gargaɗi game da mutanen da suke cinye gidajen gwaurayeMar 12:40
Ayoyin
Mar 12:40Suna ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sukan yi dogayen addu’o’i. Irin mutanen nan, za su sha hukunci mai tsanani sosai.”
- Bulus: iyalai su riƙa tallafa wa gwaurayensu1Tim 5:3–5, 1Tim 5:16
Ayoyin
1Tim 5:3–5Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako.
1Tim 5:16In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.
- Gwauruwar da za a lasafta domin tallafi sai ta kai shekara sittin aƙalla1Tim 5:9–10
Ayoyin
1Tim 5:9–10Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta, aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.
- Gwauruwa tana da ’yancin sāke yin aure1Kor 7:39
Ayoyin
1Kor 7:39Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da ’yanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji.
Misalai
- Tamar ta zauna gwauruwa a gidan mahaifinta, da tufafin gwauranciFar 38:11, Far 38:14, Far 38:19
Ayoyin
Far 38:11Sai Yahuda ya ce wa surukarsa Tamar, “Ki yi zama kamar gwauruwa a gidan mahaifinki sai ɗana Shela ya yi girma.” Gama ya yi tunani, “Shi ma zai mutu, kamar ’yan’uwansa.” Saboda haka Tamar ta je ta zauna a gidan mahaifinta.
Far 38:14sai ta tuɓe rigunan gwaurancinta ta rufe kanta da lulluɓi don ta ɓad da kamanninta, sa’an nan ta je ta zauna a ƙofar shigar Enayim, wadda take a hanyar zuwa Timna. Gama ta lura cewa ko da yake Shela yanzu ya yi girma, ba a ba da ita gare shi ta zama matarsa ba.
Far 38:19Bayan ta tafi, sai ta tuɓe lulluɓin, ta sāke sa tufafin gwaurancinta.
- Na’omi ta rasa mijinta da ’ya’yanta maza biyu a MowabRut 1:3–5
Ayoyin
Rut 1:3–5To, Elimelek mijin Na’omi ya rasu, aka bar ta da ’ya’yanta maza biyu. Suka auri mata Mowabawa, sunan ɗaya Orfa ɗayan kuma Rut. Bayan sun zauna a can kamar shekara goma, sai Malon da Kiliyon suka mutu su ma, aka kuma bar Na’omi babu ’ya’yanta maza biyu da kuma mijinta.
- Rut ta yi kalan hatsi a gonaki don ta ciyar da Na’omiRut 2:2–3
Ayoyin
Rut 2:2–3Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je, ’yata.” Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek.
- Wata mace daga Tekowa ta yi kamar gwauruwa a gaban Dawuda2Sam 14:2–5
Ayoyin
2Sam 14:2–5Saboda haka Yowab ya aiki wani zuwa Tekowa, ya sa a zo da wata mace mai hikima. Ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki. Ki sa rigar makoki, kada kuwa ki shafa mai. Ki yi kamar macen da ta yi kwanaki da yawa, tana makokin matattu. Sa’an nan ki je wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai Yowab ya faɗa mata duk abin da za tă faɗa. Da macen da ta fito daga Tekowa ta je wajen sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma, sai ta ce, “Ka taimake ni, ya sarki!” Sarki ya ce mata, “Mece ce matsalarki?” Sai ta ce, “Tabbatacce, ni gwauruwa ce; mijina ya mutu.
- Huram, maƙerin tagulla na Solomon, ɗan gwauruwa ne1Sar 7:14
Ayoyin
1Sar 7:14wanda mahaifiyarsa gwauruwa ce daga kabilar Naftali, wanda kuma mahaifinsa mutumin Taya ne, shi Huram, gwani ne a aikin tagulla. Huram gwani ne sosai kuma ya saba da yin kowane irin aikin tagulla. Sai ya zo wurin Sarki Solomon ya kuma yi dukan aikin da aka sa shi.
- Zeruwa mahaifiyar Yerobowam gwauruwa ce1Sar 11:26
Ayoyin
1Sar 11:26Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa.
- Gwauruwar Zarefat tana da ɗan gari hannu guda da ɗan mai kawai1Sar 17:10–16
Ayoyin
1Sar 17:10–16Saboda haka sai ya tafi Zarefat. Sa’ad da ya isa ƙofar gari, sai ga wata gwauruwa tana tattara ’yan itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa a tulu don in sha.” Da ta kama hanya za tă tafi tă kawo, sai ya sāke kiranta ya ce, “Ina roƙonki, ki kuma kawo mini ɗan abinci.” Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara ’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.” Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Ki tafi gida, ki yi yadda kika ce. Amma da farko ki yi mini ’yar wainar burodi daga abin da kike da shi ki kawo mini, sa’an nan ki yi wani abu wa kanki da kuma ɗanki. Gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tulun garin ba zai ƙare ba, kwalabar man kuma ba zai bushe ba sai ranar da Ubangiji ya bayar da ruwan sama a ƙasar.’ ” Sai ta tafi, ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Saboda haka aka kasance da abinci kowace rana wa Iliya da kuma don macen da iyalinta. Gama tulun garin bai ƙare ba, kwalabar man kuma bai bushe ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Iliya.
- Elisha ya ceci ’ya’yan gwauruwa daga mai bin ta bashi ta wurin mai2Sar 4:1–7
Ayoyin
2Sar 4:1–7Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.” Elisha ya amsa mata ya ce, “Me kike so in yi miki? Ki faɗa mini, me kike da shi a gidanki?” Sai ta ce, “Baiwarka ba ta da kome a can, sai ɗan tulun man zaitun.” Elisha ya ce, “Ki je wurin dukan maƙwabtanki, ki nemi tulunan da babu kome a ciki. Kada ki nemo kaɗan kawai. Sa’an nan ki shiga ciki, ki kulle ƙofar da ke da ’ya’yanki kuke ciki. Ku ɗuɗɗura man a dukan tulunan, sa’ad da kowanne ya cika, sai ki ajiye a gefe.” Ta tashi ta shiga tare da ’ya’yanta maza, suka kulle ƙofa. ’Ya’yanta suka kawo mata tuluna, ita kuma tana ɗurawa. Da dukan tulunan suka cika, sai ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tulu.” Amma ya amsa ya ce, “Ai, ba saura.” Sa’an nan man ya daina zuba. Sai ta tafi ta faɗa wa mutumin Allah. Shi kuwa ya ce mata, “Tafi, ki sayar da man, ki biya bashinki. Ki biya bukatanki da na ’ya’yanki da sauran da ya rage.”
- Anna, gwauruwa har shekara tamanin da huɗu, ba ta taɓa barin haikali baLuk 2:36–38
Ayoyin
Luk 2:36–38Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure, ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a. Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.
- Wata matalauciya gwauruwa ta saka anini biyu a baitulmaliMar 12:41–44
Ayoyin
Mar 12:41–44Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo. Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan. Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.”
- Yesu ya tā da ɗa tilo na wata gwauruwa a NayinLuk 7:11–15
Ayoyin
Luk 7:11–15Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi. Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita. Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, “Kada ki yi kuka.” Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!” Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.
- Ba a kula da gwaurayen masu jin Hellenanci a raba abinci na yau da kullumAyy M 6:1
Ayoyin
Ayy M 6:1A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.
- Gwauraye sun nuna wa Bitrus tufafin da Dokas ta ɗinkaAyy M 9:39
Ayoyin
Ayy M 9:39Sai Bitrus ya tafi tare da su, sa’ad da ya iso sai aka kai shi ɗakin saman. Duka gwauraye suka tsaya kewaye da shi, suna kuka suna nunnuna masa riguna da kuma waɗansu tufafin da Dokas ta yi yayinda take tare da su.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.