Rayuwar yau da kullum
Gulma a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (24), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Kada ka yi ta yawo kana baza ƙarya a cikin mutanenkaFir 19:16
Ayoyin
Fir 19:16“ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.
- Wa zai zauna tare da Allah? Wanda ba ya ɓata suna da harshensaZab 15:3
Ayoyin
Zab 15:3ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,
- Mai gulma yakan tona asiri; amintacce yakan ɓoye maganaK Mag 11:13, K Mag 20:19
Ayoyin
K Mag 11:13Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.
K Mag 20:19Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.
- Mai gulma yakan raba abokai na kurkusaK Mag 16:28, K Mag 17:9
Ayoyin
K Mag 16:28Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
K Mag 17:9Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
- Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi sukeK Mag 18:8, K Mag 26:22
Ayoyin
K Mag 18:8Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.
K Mag 26:22Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum.
- Ba itace, wuta takan mutu; ba gulma, faɗa yakan ƙareK Mag 26:20–21
Ayoyin
K Mag 26:20–21In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba. Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.
- Jita-jita kan kawo fushiK Mag 25:23
Ayoyin
K Mag 25:23Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.
- Irmiya ya ji raɗa: “Mu kai kararsa!”Irm 20:10
Ayoyin
Irm 20:10Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa, “Razana ta kowace fuska! Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!” Dukan abokaina suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa, “Mai yiwuwa a ruɗe shi; sai mu yi nasara a kansa mu ɗau fansa a kansa.”
- Gwauraye ’yan mata marasa aiki sukan zama masu gulma da masu shisshigi1Tim 5:13
Ayoyin
1Tim 5:13Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.
- Bulus yana tsoron ɓata suna da gulma a Korint2Kor 12:20
Ayoyin
2Kor 12:20Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi.
- Kada ku ɓata sunan junaYaƙ 4:11
Ayoyin
Yaƙ 4:11’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.
Misalai
- Yusuf ya kawo wa mahaifinsa mummunan labari game da ’yan’uwansaFar 37:2
Ayoyin
Far 37:2Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa.
- ’Yan leƙen asiri sun baza mummunan labari game da ƙasarƘid 13:32, Ƙid 14:36
Ayoyin
Ƙid 13:32Sai suka yaɗa labari marar kyau ga Isra’ilawa game da ƙasar da suka binciko. Suka ce, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zama a cikinta. Dukan mutanen da muka gani a wurin, ƙatti ne.
Ƙid 14:36Saboda haka mutanen da Musa ya aika, su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama’a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar,
- Doyeg mutumin Edom ya gaya wa Shawulu cewa Ahimelek ya taimaki Dawuda1Sam 22:9–10
Ayoyin
1Sam 22:9–10Amma Doyeg mutumin Edom da yake tsaye tare da fadawan Shawulu ya ce, “Na ga ɗan Yesse ya zo wurin Ahimelek ɗan Ahitub a Nob. Ahimelek ya roƙi Ubangiji saboda shi, ya kuma ba shi guzuri da takobin Goliyat Bafilistin.”
- An gaya wa Yowab cewa Abner ya zo ya tafi lafiya2Sam 3:23
Ayoyin
2Sam 3:23Sa’ad da Yowab da dukan sojoji suka dawo, aka gaya masa cewa Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya sallame shi, ya kuma tafi lafiya.
- Ziba ya ce Mefiboshet yana sa rai zai sāke samun mulkin2Sam 16:3
Ayoyin
2Sam 16:3Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?” Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima gama yana tsammani cewa, ‘Yau gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar kakana.’ ”
- Jita-jitar Sanballat cewa Yahudawa suna shirin tawayeNeh 6:6–9
Ayoyin
Neh 6:6–9wadda aka rubuta cewa, “An ba da labari cikin al’ummai, kuma Geshem ya ce gaskiya ne, cewa kai da Yahudawa kun shirya tawaye, saboda haka kuke sāke ginin katangar. Ban da haka ma, bisa ga waɗannan rahotanni kana shirin zaman sarkinsu har ma ka naɗa annabawa su yi wannan shela game da kai a Urushalima, su ce, ‘Akwai sarki a Yahuda!’ To, wannan rahoto zai koma wurin sarki; saboda haka ka zo, mu tattauna wannan batu.” Sai na aika masa wannan amsa, na ce, “Babu wani abu haka da yake faruwa; ka dai ƙaga wannan daga tunaninka ne.” Suka dai yi ƙoƙari su tsoratar da mu, suna cewa, “Hannuwansu za su rasa ƙarfin yin aiki, ba kuwa za su ƙare aikin ba.” Amma na yi addu’a na ce, “Yanzu, ya Allah, ka ƙarfafa hannuwana.”
- Manyan mutanen Yahuda suna kai labari tsakanin Tobiya da NehemiyaNeh 6:17–19
Ayoyin
Neh 6:17–19A waɗannan kwanaki, manyan garin Yahuda suka yi ta aika wasiƙu masu yawa zuwa ga Tobiya, shi kuma ya yi ta aika musu da amsoshi. Gama mutane da yawa a cikin Yahuda sun rantse wa Tobiya za su goyi bayansa, domin ya auri ’yar Shekaniya, ɗan Ara. Ɗansa kuma, wato, Yehohanan, ya auri ’yar Meshullam, ɗan Berekiya. Ban da haka ma, mutanen sun yi ta ba ni labarin ayyuka masu kyau da Tobiya ya yi, sa’an nan kuma suna faɗa masa duk abin da na faɗa. Tobiya kuwa ya aika wasiƙu don yă tsorata ni.
- An zuga mutane su ce Istifanus ya yi magana a kan MusaAyy M 6:11
Ayoyin
Ayy M 6:11Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”
- Mugun ɓata sunan da Diyotirefes ya yi a kan Yohanna3Yoh 1:9–10
Ayoyin
3Yoh 1:9–10Na rubuta wa ikkilisiya, amma Diyotirefes, wanda yake son zama na farko, ya ƙi yă yi hulɗa da mu. Saboda haka in na zo, zan tone abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har yana ƙin marabtar ’yan’uwa. Yana hana waɗanda suke so yin haka, yana ma korinsu daga ikkilisiya.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.