Rayuwar yau da kullum
Yara a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (57), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
A lokacin haihuwa
- Akan yi wa jarirai wanka, a goge su da gishiri, a naɗe su cikin tsummokiEzk 16:4
Ayoyin
Ezk 16:4A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki.
- An nannaɗe Yesu a zane aka kwantar da shi cikin kwamiLuk 2:7, Luk 2:12
- Ungozoma ta ɗaura jan zare a hannun ɗaya daga cikin tagwayeFar 38:27–30
Ayoyin
Far 38:27–30Sa’ad da lokaci ya yi da za tă haihu, ashe, tagwaye ’yan maza ne suke cikinta. Yayinda take haihuwa, ɗaya daga cikinsu ya fid da hannunsa; sai ungonzomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, ta ce, “Wannan ne ya fito da farko.” Amma sa’ad da ya janye hannunsa, sai ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “Wato, haka ne ka keta ka fito!” Sai aka ba shi suna Ferez. Sa’an nan ɗan’uwansa wanda yake da jan zare a hannunsa ya fito, aka kuma ba shi suna Zera.
- An haifi Isuwa ja da gashi a jiki, Yaƙub kuma ya kama diddigensaFar 25:24–26
Ayoyin
Far 25:24–26Da lokaci ya yi da za tă haihu, sai ga ’yan biyu maza a mahaifarta. Wanda ya fara fita ja ne, dukan jikinsa kuwa kamar riga mai gashi. Don haka aka sa masa suna Isuwa. Bayan wannan, ɗan’uwansa ya fito, da hannunsa yana riƙe da ɗiɗɗigen Isuwa; don haka aka sa masa suna Yaƙub. Ishaku yana da shekara sittin, lokacin da Rebeka ta haife su.
- Ana yi wa ’ya’ya maza kaciya a rana ta takwasFar 17:12, Fir 12:3, Luk 2:21
Ayoyin
Far 17:12Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan zamananku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba.
Fir 12:3A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya.
Luk 2:21A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da mala’ika ya ba shi kafin a yi cikinsa.
- Iyayen da suka yi addu’a domin ɗa: Ishaku, Hannatu, ZakariyaFar 25:21, 1Sam 1:11, 1Sam 1:20, Luk 1:13
Ayoyin
Far 25:21Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki.
1Sam 1:11Ta yi ta cewa, “Ya Ubangiji Maɗaukaki. In har ka dubi baƙin cikin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuma manta da baiwarka ba, amma ka ba ta ɗa, ni ma zan miƙa shi ga Ubangiji dukan rayuwarsa, aska kuwa ba za tă taɓa kansa ba.”
1Sam 1:20Ana nan sai Hannatu ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Ta ba shi suna Sama’ila; tana cewa, “Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji.”
Luk 1:13Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna.
Raɗa suna
- Liyatu da Rahila sun ba kowane ɗa suna tare da daliliFar 29:32–35, Far 30:6–13, Far 30:22–24
Ayoyin
Far 29:32–35Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben, gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.” Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon. Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa ’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi. Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda. Sa’an nan ta daina haihuwa.
Far 30:6–13Sa’an nan Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni; ya saurari roƙona ya kuma ba ni ɗa.” Saboda wannan ta ba shi suna Dan. Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu. Sai Rahila ta ce, “Na yi kokawa sosai da ’yar’uwata, na kuwa yi nasara.” Saboda haka ta kira shi Naftali. Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa. Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa. Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad. Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu. Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.
Far 30:22–24Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta. Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.” Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”
- Rahila tana mutuwa ta ba ɗanta suna Ben-Oni; Yaƙub ya kira shi BenyaminFar 35:18
Ayoyin
Far 35:18Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin.
- Hannatu ta ba shi suna Sama’ila: “Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji”1Sam 1:20
Ayoyin
1Sam 1:20Ana nan sai Hannatu ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Ta ba shi suna Sama’ila; tana cewa, “Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji.”
- Ikabod: “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”1Sam 4:21
Ayoyin
1Sam 4:21Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta.
- ’Yar Fir’auna ta ba shi suna Musa: “Na tsamo shi daga ruwa”Fit 2:10
Ayoyin
Fit 2:10Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.”
- ’Yan’uwa sun so a ba jaririn sunan mahaifinsa; Elizabet ta ce YohannaLuk 1:59–63
Ayoyin
Luk 1:59–63A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.” Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.” Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.
- Matan maƙwabta sun ba jikan Na’omi suna ObedRut 4:17
Ayoyin
Rut 4:17Matan da suke zama a wurin suka ce, “Na’omi ta sami yaro.” Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda.
Shayarwa da yaye
- Ibrahim ya yi babban biki a ranar da aka yaye IshakuFar 21:8
Ayoyin
Far 21:8Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki.
- Hannatu ta riƙe Sama’ila har aka yaye shi, sa’an nan ta kai shi Shilo1Sam 1:22–28
Ayoyin
1Sam 1:22–28Hannatu kuwa ba tă bi su ba. Ta gaya wa mijinta cewa, “Sai bayan na yaye yaron, zan kai shi in miƙa shi a gaban Ubangiji, yă kuma kasance a wurin koyaushe.” Elkana mijinta ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi miki kyau. Ki jira har sai bayan kin yaye shi. Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Saboda haka matar ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta har ta yaye shi. Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo. Bayan an yanka bijimin, sai suka kawo yaron wurin Eli. Sai ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ba ka gane ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana addu’a ga Ubangiji. Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi. Saboda haka, na ba da shi ga Ubangiji muddin ransa, zai zama na Ubangiji.” A can kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.
- An biya mahaifiyar Musa kanta ta shayar da shiFit 2:7–9
Ayoyin
Fit 2:7–9Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?” Sai ta amsa ta ce, “I, tafi.” Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron. Diyar Fir’auna ta ce mata, “Ɗauki jaririn, ki yi mini renonsa, zan kuwa biya ki.” Saboda haka ta ɗauki yaron, ta yi renonsa.
- Na’omi ta ɗauki jariri Obed a cinyartaRut 4:16
Ayoyin
Rut 4:16Sai Na’omi ta ɗauki yaron, ta kwantar da shi a cinyarta ta kuma kula da shi.
- Mai reno ta gudu da Mefiboshet ɗan shekara biyar; ya fāɗi ya gurgunce2Sam 4:4
Ayoyin
2Sam 4:4(Yonatan ɗan Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet wanda yake gurgu a duka ƙafafu. Yana da shekara biyar ne sa’ad da labarin mutuwar Shawulu da Yonatan ya zo daga Yezireyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi ta gudu, amma yayinda take hanzari tă gudu, sai ya fāɗo, ya gurgunce.)
- An ɓoye jariri Yowash tare da mai renonsa daga Ataliya2Sar 11:2
Ayoyin
2Sar 11:2Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yoram, ’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.
Girma
- Kowace shekara Hannatu takan ɗinka wa yaro Sama’ila ’yar ƙaramar riga1Sam 2:18–19
Ayoyin
1Sam 2:18–19Amma yaron nan Sama’ila, yana hidima a gaban Ubangiji yana sanye da efod na lilin. Kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka ’yar taguwa ta kai masa sa’ad da ita da mijinta suka je miƙa hadaya ta shekara.
- Iyaye sukan koya wa ’ya’yansu a gida da kuma a hanyaM Sh 6:7, M Sh 11:19
Ayoyin
M Sh 6:7Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
M Sh 11:19Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
- Sa’ad da ɗanka ya tambaya, “Mene ne manufar wannan?” — ka faɗa masa labarinFit 13:14
Ayoyin
Fit 13:14“A kwanaki masu zuwa, in ɗanka ya tambaye ka, ‘Mene ne manufar wannan?’ Ka faɗa masa cewa, ‘Da hannu mai iko Ubangiji ya fito da mu daga Masar, daga ƙasar bauta.
- Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă biK Mag 22:6
Ayoyin
K Mag 22:6Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
- Maganganu a Karin Magana game da sandar horoK Mag 13:24, K Mag 29:15
Ayoyin
K Mag 13:24Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba, amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
K Mag 29:15Sandar gyara kan ba da hikima, amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
- Yara sun saurara sa’ad da aka karanta Doka da babbar muryaYosh 8:35, Neh 8:2–3
Ayoyin
Yosh 8:35Babu wata kalmar da Musa ya umarta da Yoshuwa bai karanta wa dukan taron Isra’ilawa ba, haɗe da mata, da yara, da baƙin da suke zama tare da su.
Neh 8:2–3Saboda haka a rana ta farko ga watan bakwai, Ezra firist, ya kawo Doka a gaban taro, wanda ya ƙunshi maza da mata da dukan waɗanda za su iya fahimta. Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar.
- Yara suna tsalle suna wasa a titunaAyu 21:11, Zak 8:5
- Yesu yana da shekara goma sha biyu a haikali, yana yi wa malamai tambayoyiLuk 2:41–47
Ayoyin
Luk 2:41–47Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa. Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada. Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba. Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin ’yan’uwansu da abokansu. Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa. Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi. Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa.
- Yesu ya yi girma cikin hikima da tsawoLuk 2:40, Luk 2:52
- Bulus ya yi karatu a ƙarƙashin GamaliyelAyy M 22:3
Ayoyin
Ayy M 22:3“Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau.
- Timoti ya koya daga kakarsa Loyis da mahaifiyarsa Yunis2Tim 1:5, 2Tim 3:15
Ayoyin
2Tim 1:5An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.
2Tim 3:15da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
- Yara suna ihu “Hosanna” a filin haikaliMat 21:15
Ayoyin
Mat 21:15Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.
- Yesu ya sa wa ƙananan yara albarkaMat 19:13–15, Mar 10:13–16
Ayoyin
Mat 19:13–15Sa’an nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don yă ɗibiya musu hannuwansa, yă kuma yi musu addu’a. Amma almajirai suka tsawata wa waɗanda suka kawo su. Yesu ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.” Sa’ad da ya ɗibiya musu hannuwansa, sai ya tafi abinsa.
Mar 10:13–16Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su. Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.
Misalai
- Yaƙub ya fi ƙaunar Yusuf ya kuma ba shi riga mai launi iri-iriFar 37:3–4
Ayoyin
Far 37:3–4Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau. Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
- Doka ta kāre rabo biyu na ɗan fari na matar da ba a ƙaunaM Sh 21:15–17
Ayoyin
M Sh 21:15–17In mutum yana da mata biyu, yana kuwa ƙaunar ɗaya, ba ya kuma ƙaunar ɗayan, su biyun kuwa suka haifi masa ’ya’ya maza, sai ya zamana cewa ɗan farin ya kasance na wadda ba ya ƙauna, to, a ranar da zai yi faɗa wane ne a cikin ’ya’yansa zai riƙe gādon da zai bar musu, kada yă sa ɗan matar da yake ƙauna yă zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan matar da ba ya ƙauna, wanda shi ne ɗan farin. Dole yă yarda cewa ɗan matar da ba ya ƙaunar ne ɗan fari, ta wurin ba shi rabo kashi biyu na dukan abin da yake da shi, gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.
- Wata ƙaramar yarinya Ba’isra’iliya ta gaya wa matar Na’aman game da annabin2Sar 5:2–3
Ayoyin
2Sar 5:2–3To, daga cikin hare haren da mutanen Aram suke kaiwa, sai suka kama wata yarinya daga ƙasar Isra’ila, aka sa ta zama mai yi wa matar Na’aman aiki. Sai ta ce wa uwargijiyarta, “Da dai shugabana zai ga annabin da yake Samariya, da annabin zai warkar da shi daga kuturtarsa.”
- Yowash ya zama sarki yana da shekara bakwai, Yosiya kuma yana da takwas2Sar 11:21, 2Sar 22:1
Ayoyin
2Sar 11:21Yowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya fara mulki.
2Sar 22:1Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat.
- An ɗauki yara bayi saboda bashin iyayensu2Sar 4:1, Neh 5:5
Ayoyin
2Sar 4:1Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.”
Neh 5:5Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa ’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin ’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”
- Fir’auna ya umarta a jefa jarirai maza na Ibraniyawa cikin NiluFit 1:22
Ayoyin
Fit 1:22Sai Fir’auna ya ba da umarni wa mutanensa ya ce, “Duk yaron da yake namijin da haka haifa, dole ku jefa shi cikin kogi, amma ku bar yara mata su rayu.”
- Hiridus ya kashe yara maza na Betlehem daga masu shekara biyu zuwa ƙasaMat 2:16
Ayoyin
Mat 2:16Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.
- Jikoki su ne rawanin tsofaffiK Mag 17:6
Ayoyin
K Mag 17:6Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.