Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Yunwa da fari

Abubuwan ban mamaki

Yunwa da fari a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (33), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

A cikin Farawa

  • Abram ya gangara zuwa Masar domin yunwar ta yi tsananiFar 12:10
    Ayoyin
    Far 12:10To, a lokacin, an yi yunwa a ƙasar, sai Abram ya gangara zuwa Masar don yă zauna a can na ɗan lokaci, domin yunwa ta yi tsanani.
  • A wata yunwa Ishaku ya tafi Gerar, ba Masar baFar 26:1–2
    Ayoyin
    Far 26:1–2Aka yi yunwa a ƙasar; ban da yunwar da aka yi da fari a zamanin Ibrahim, sai Ishaku ya tafi wurin Abimelek sarkin Filistiyawa a Gerar. Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ishaku ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar; ka yi zauna a ƙasar da zan faɗa maka.
  • A Masar shekara bakwai na yalwa, sa’an nan shekara bakwai na yunwaFar 41:29–30, Far 41:54
    Ayoyin
    Far 41:29–30Shekaru bakwai na yalwar abinci suna zuwa a dukan ƙasar Masar, amma shekaru bakwai na yunwa za su biyo bayansu. Tsananin yunwar za tă sa a manta da dukan isashen abincin da aka samu a ƙasar Masar, yunwa kuwa za tă rufe dukan ƙasar.
    Far 41:54sai shekaru bakwai na yunwa suka soma shigowa, kamar yadda Yusuf ya faɗa. Aka yi yunwa ko’ina amma ban da ƙasar Masar. Don akwai abinci.
  • Yusuf ya tara hatsi kamar yashin tekuFar 41:48–49
    Ayoyin
    Far 41:48–49Yusuf ya tattara dukan abincin da aka samu a waɗannan shekaru bakwai na yalwa a Masar, ya kuma yi ajiyarsu a cikin birane. A kowane birni, ya sa abincin da aka nome a kewayensa. Sai Yusuf ya tara hatsi da yawan gaske, kamar yashi a bakin teku, har sai da ya kāsa iya auna shi, gama ba a iya aunawa.
  • Kowace al’umma ta zo wurin Yusuf a Masar don ta sayi hatsiFar 41:56–57
    Ayoyin
    Far 41:56–57Sa’ad da yunwa ta bazu a dukan ƙasar, sai Yusuf ya buɗe gidajen ajiya, ya kuma sayar da hatsi ga Masarawa, gama yunwa ta yi tsanani a dukan Masar. Dukan ƙasashe kuwa suka zo Masar don saya hatsi daga Yusuf, gama yunwa ta yi tsanani a dukan duniya.
  • ’Yan’uwan Yusuf goma sun gangara don su sayi hatsiFar 42:1–3
    Ayoyin
    Far 42:1–3Sa’ad da Yaƙub ya sami labari cewa akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa ’ya’yansa maza, “Don me kuke duban juna kawai?” Ya ci gaba, “Na ji cewa akwai hatsi a Masar. Ku gangara can ku sayo mana, domin mu rayu kada mu mutu.” Sai goma daga cikin ’yan’uwan Yusuf suka gangara don su saya hatsi daga Masar.
  • Shekara biyu na yunwa, da ƙarin biyar ba noma ba girbiFar 45:6
    Ayoyin
    Far 45:6Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.
  • Masarawa sun biya abinci da kuɗi, sa’an nan da dabbobinsuFar 47:13–17
    Ayoyin
    Far 47:13–17A yanzu, a cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwa ta yi tsanani ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka shiga matsananciyar wahala! Yusuf ya tattara dukan kuɗaɗen da suke a Masar da Kan’ana don biyan hatsin da suke saya, ya kuwa kawo su a fadan Fir’auna. Sa’ad da kuɗin mutanen Masar da Kan’ana suka ƙare, dukan Masar ta zo wurin Yusuf ta ce, “Ka ba mu abinci. Me zai sa mu mutu a idanunka? Kuɗinmu duk sun ƙare.” Yusuf ya ce, “To, ku kawo dabbobinku, zan sayar muku da abinci a madadin dabbobinku, tun da kuɗinku ya ƙare.” Saboda haka suka kawo dabbobinsu wa Yusuf, ya kuma ba su abinci a madadin dawakai, tumaki da awaki, shanu da jakunansu. Ya kuwa ba su abinci a madadin dabbobinsu, a wannan shekara.
  • Sa’an nan suka sayar da gonakinsu, ƙasar kuma ta zama ta Fir’aunaFar 47:19–20
    Ayoyin
    Far 47:19–20Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakinmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna. Ka ba mu iri don mu rayu, kada mu mutu, don kuma kada gonakin ƙasarmu su zama kango.” Ta haka Yusuf ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da gonakinsu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama mallakar Fir’auna.
  • Tun daga lokacin kashi ɗaya bisa biyar na girbi ya zama na Fir’aunaFar 47:23–24
    Ayoyin
    Far 47:23–24Yusuf ya ce wa mutane, “Yanzu da na saye ku da kuma gonakinku a yau wa Fir’auna, ga iri don ku shuka a gonaki. Amma sa’ad da hatsi suka nuna, za ku ba da kashi ɗaya bisa biyar ga Fir’auna. Sauran kashi huɗu bisa biyar kuma ku riƙe a matsayin iri don gonaki da kuma abinci wa kanku da gidajenku da kuma ’ya’yanku.”

A Isra’ila

  • A zamanin alƙalai wani iyali daga Betlehem ya ƙaura zuwa MowabRut 1:1
    Ayoyin
    Rut 1:1A kwanakin da mahukunta suke mulki an yi yunwa a ƙasar, sai wani mutum daga Betlehem a Yahuda tare da matarsa da ’ya’yansu maza biyu, suka tafi su yi zama na ɗan lokaci a ƙasar Mowab.
  • Na’omi ta koma gida da ta ji abinci ya samu kumaRut 1:6
    Ayoyin
    Rut 1:6Sa’ad da ta ji a Mowab cewa Ubangiji ya zo don yă taimaki mutanensa ta wurin tanada musu da abinci, sai Na’omi tare da surukanta suka shirya su koma gida daga can.
  • A zamanin Dawuda yunwa ta yi shekara uku a jere2Sam 21:1
    Ayoyin
    2Sam 21:1Lokacin da Dawuda yake mulki, an yi yunwa shekara uku a jere; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji. Ubangiji ya ce, “Saboda Shawulu ne da alhakin jinin gidansa; domin ya kashe Gibeyonawa.”
  • Iliya ga Ahab: ba raɓa ko ruwan sama sai da maganata1Sar 17:1
    Ayoyin
    1Sar 17:1To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”
  • Hankaki sun kawo wa Iliya burodi da nama safe da yamma1Sar 17:6
    Ayoyin
    1Sar 17:6Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin.
  • Gari a tulun gwauruwa da mai a kwalabarta ba su ƙare ba1Sar 17:14–16
    Ayoyin
    1Sar 17:14–16Gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tulun garin ba zai ƙare ba, kwalabar man kuma ba zai bushe ba sai ranar da Ubangiji ya bayar da ruwan sama a ƙasar.’ ” Sai ta tafi, ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Saboda haka aka kasance da abinci kowace rana wa Iliya da kuma don macen da iyalinta. Gama tulun garin bai ƙare ba, kwalabar man kuma bai bushe ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Iliya.
  • A shekara ta uku yunwa ta yi tsanani a Samariya1Sar 18:1–2
    Ayoyin
    1Sar 18:1–2Bayan dogon lokaci, a cikin shekara ta uku, maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Tafi, ka gabatar da kanka ga Ahab, zan kuwa aika da ruwan sama a ƙasar.” Saboda haka Iliya ya tafi ya gabatar da kansa ga Ahab. Yanzu dai yunwa ta tsananta a Samariya,
  • Ahab ya aiki Obadiya ya nemi ciyawa domin dawakai da alfadarai1Sar 18:5
    Ayoyin
    1Sar 18:5Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka ratsa ƙasar zuwa dukan maɓulɓulai da fadamu. Mai yiwuwa ka sami ciyawa mu ba dawakai da alfadarai don su rayu, don kada mu kashe dabbobinmu.”
  • Daga baya an tuna: ba ruwan sama shekara uku da rabiLuk 4:25, Yaƙ 5:17
    Ayoyin
    Luk 4:25Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar.
    Yaƙ 5:17Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi.
  • Yunwa a Gilgal: kabewar jeji a cikin fate, “akwai dafi a cikin tukunyan nan!”2Sar 4:38–40
    Ayoyin
    2Sar 4:38–40Sai Elisha ya koma Gilgal, a can kuwa ana yunwa a yankin. Yayinda ƙungiyar annabawa suke tattaunawa da shi, sai ya ce wa Gehazi bawansa, “Ka sa babban tukunya a wuta, ka yi wa mutanen nan fate.” Ɗaya daga cikin mutanen ya shiga gona don neman ganyaye, ya kuwa sami kabewar jeji. Ya tsinko ’ya’yanta cike da shafin rigarsa. Da ya dawo, sai ya yayyanka su ya zuba a cikin tukunyar faten, ko da yake ba wanda ya san ko mene ne. Sai aka zuba wa mutanen faten, amma da suka fara ci, sai suka yi ihu suna cewa, “Ya mutumin Allah, akwai dafi a cikin tukunyan nan!” Suka kuwa kāsa ci.
  • Matar Shunam ta zauna shekara bakwai cikin Filistiyawa lokacin yunwa2Sar 8:1–3
    Ayoyin
    2Sar 8:1–3To, Elisha ya riga ya ce wa matan da ya tā da ɗanta daga matattu, “Ki kwashe iyalinki ku tafi duk inda za ku tafi na ɗan lokaci, domin Ubangiji ya sa a yi yunwa na shekara bakwai a ƙasar.” Sai macen ta yi kamar yadda mutumin Allah ya faɗa. Ita da iyalinta suka tafi ƙasar Filistiyawa suka zauna shekara bakwai. A ƙarshen shekara bakwai ɗin sai ta dawo daga ƙasar Filistiyawa, ta kuma tafi wajen sarki ta roƙa a mayar mata da gidanta da filinta.
  • Kutare huɗu sun iske sansanin Arameyawa a bayan Samariya ba kowa2Sar 7:3–5
    Ayoyin
    2Sar 7:3–5To, akwai waɗansu kutare huɗu a ƙofar gari. Suka ce wa junansu, “Don me za mu zauna a nan sai mun mutu? In muka ce, ‘Za mu shiga cikin birni’ yunwa tana can, za mu kuwa mutu. Idan kuwa muka zauna a nan, za mu mutu. Saboda haka, bari mu ƙetare zuwa sansanin Arameyawa mu miƙa kai. Idan suka bar mu da rai, to; idan kuwa suka kashe mu, shi ke nan.” Da yamma sai suka tashi suka tafi sansanin Arameyawa. Yayinda suka shiga tsakiyar sansanin Arameyawa kuwa, sai suka tarar ba kowa a can,
  • Sa’an nan aka sayar da mudu na gari mai laushi a shekel guda2Sar 7:16
    Ayoyin
    2Sar 7:16Sa’an nan jama’a suka fita suka kwashi ganima a sansanin Arameyawa. Aka kuwa sayar da gari mai laushi a farashin shekel guda, mudu biyu na sha’ir kuma a shekel guda, yadda Ubangiji ya faɗi.
  • A kewayewar Urushalima mutanen ƙasar ba su da abinci2Sar 25:3, Irm 52:6
    Ayoyin
    2Sar 25:3A rana ta tara ta watan huɗu, lokacin da yunwa ta yi tsanani a birnin, babu kuma abinci domin mutane su ci.
    Irm 52:6A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.
  • Irmiya: ƙasa ta tsattsage; barewa ta bar ɗanta don rashin ciyawaIrm 14:4–5
    Ayoyin
    Irm 14:4–5Ƙasa ta tsattsage saboda babu ruwan sama a ƙasar; manoma sun sha kunya suka kuma rufe kawunansu. Har barewa a kurmi ma ta gudu ta bar ’ya’yan da ta haihu sababbi saboda babu ciyawa.
  • Makoki: ƙananan yara suna roƙon burodiMako 4:4
    Ayoyin
    Mako 4:4Domin ƙishirwa harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu; yaran suna roƙo a ba su burodi, amma ba wanda ya ba su.
  • A zamanin Nehemiya mutane sun jinginar da gonaki da gidaje don su sayi hatsiNeh 5:3
    Ayoyin
    Neh 5:3Waɗansu kuwa suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”

A cikin Sabon Alkawari

  • A labarin Yesu babbar yunwa ta bar ƙaramin ɗan cikin bukataLuk 15:14
    Ayoyin
    Luk 15:14Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi.
  • Agabus ya faɗi babbar yunwa za ta zo; ta zo a zamanin KalaudiyusAyy M 11:28
    Ayoyin
    Ayy M 11:28Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.)
  • Almajirai sun aika da taimako zuwa Yahudiya ta hannun Barnabas da ShawuluAyy M 11:29–30
    Ayoyin
    Ayy M 11:29–30Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya. Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.