Bincika › Jigogi › Lamba bakwai
Abubuwan ban mamaki
Lamba bakwai a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (49), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Kwana bakwai
- Allah ya huta a rana ta bakwai; kwana shida na aiki, sa’an nan AsabbaciFar 2:3, Fit 20:11, M Sh 5:13–14
Ayoyin
Far 2:3Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
Fit 20:11Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
M Sh 5:13–14Kwanaki shida za ka yi aiki, ka kuma yi dukan aikinka, amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka.
- Rigyawa ta zo kwana bakwai bayan Nuhu ya shiga jirgiFar 7:4, Far 7:10
- Nuhu ya jira kwana bakwai tsakanin aikawar kurciyaFar 8:10, Far 8:12
- Yusuf ya yi makokin mahaifinsa kwana bakwaiFar 50:10
Ayoyin
Far 50:10Sa’ad da suka kai masussukar Atad, kusa da Urdun, sai suka yi kuka da ƙarfi da kuma mai zafi, a can Yusuf ya yi makoki kwana bakwai saboda mahaifinsa.
- Abokan Ayuba sun zauna tare da shi kwana bakwai shiruAyu 2:13
Ayoyin
Ayu 2:13sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.
- Kwana bakwai na burodi marar yisti a Bikin ƘetarewaFit 12:15
Ayoyin
Fit 12:15Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti. A rana ta fari, za ku fid da yisti daga gidajenku gama duk wanda ya ci abu mai yisti daga rana ta fari har zuwa rana ta bakwai, za a fid da shi daga Isra’ila.
- Kwana bakwai a cikin bukkoki a Bikin TabanakulFir 23:34, Fir 23:42
- Naɗin firistoci ya ɗauki kwana bakwaiFit 29:35
Ayoyin
Fit 29:35“Ka yi wa Haruna da ’ya’yansa maza duk abin da na umarce ka, ka ɗauki kwana bakwai don naɗinsu.
- Shawulu ya jira Sama’ila kwana bakwai a Gilgal1Sam 13:8
Ayoyin
1Sam 13:8Ya jira har kwana bakwai bisa ga lokacin da Sama’ila ya bayar. Amma Sama’ila bai zo Gilgal ba, mutanen Shawulu suka fara watsewa.
- Mutanen Yabesh sun nemi kwana bakwai kafin su miƙa kai1Sam 11:3
Ayoyin
1Sam 11:3Dattawan Yabesh suka ce masa, “Ka ba mu kwana bakwai don mu aika manzanni a dukan ƙasar Isra’ila idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, za mu ba da kanmu gare ka.”
- Mutanen Yabesh sun yi azumi kwana bakwai bayan sun binne Shawulu1Sam 31:13
Ayoyin
1Sam 31:13Sai suka kwashi ƙasusuwansu suka binne a gindin itace tsamiya a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
- Bikin auren Samson da kacici-kacicinsa sun ɗauki kwana bakwaiMah 14:12, Mah 14:17
Ayoyin
Mah 14:12Sai Samson ya ce, “Bari in yi muku kacici-kacici, in kun ba ni amsa cikin kwana bakwai na wannan biki, zan ba ku riguna lilin talatin da kuma tufafi talatin.
Mah 14:17Ta yi ta kuka har kwana bakwai na bikin. Saboda haka a rana ta bakwai sai ya gaya mata, don ta dame shi. Ita kuwa ta bayyana kacici-kacicin wa mutanenta.
- Zerzes ya yi biki na kwana bakwai a lambun fādaEsta 1:5
Ayoyin
Esta 1:5Sa’ad da waɗannan kwanaki suka wuce, sai sarki ya yi liyafa a cikin lambun da aka shinge na fadar sarki wadda ta ɗauki kwana bakwai wa dukan mutane daga ƙarami har zuwa babba, waɗanda suke zama a masarautar Shusha.
- Bulus ya zauna kwana bakwai a TayaAyy M 21:4
Ayoyin
Ayy M 21:4Da muka sami almajirai a can, sai muka zauna da su kwana bakwai. Ta wurin Ruhu, suka yi ƙoƙari su hana Bulus wucewa zuwa Urushalima.
Shekara bakwai
- Yaƙub ya yi aiki shekara bakwai saboda Rahila, sa’an nan ƙarin bakwaiFar 29:20, Far 29:27
- Shekara bakwai na yalwa, sa’an nan bakwai na yunwa a MasarFar 41:53–54
Ayoyin
Far 41:53–54Shekaru bakwai na yalwa a Masar suka zo ga ƙarshe, sai shekaru bakwai na yunwa suka soma shigowa, kamar yadda Yusuf ya faɗa. Aka yi yunwa ko’ina amma ban da ƙasar Masar. Don akwai abinci.
- Yunwa ta shekara bakwai a zamanin Elisha2Sar 8:1–2
Ayoyin
2Sar 8:1–2To, Elisha ya riga ya ce wa matan da ya tā da ɗanta daga matattu, “Ki kwashe iyalinki ku tafi duk inda za ku tafi na ɗan lokaci, domin Ubangiji ya sa a yi yunwa na shekara bakwai a ƙasar.” Sai macen ta yi kamar yadda mutumin Allah ya faɗa. Ita da iyalinta suka tafi ƙasar Filistiyawa suka zauna shekara bakwai.
- Solomon ya gina haikali a shekara bakwai1Sar 6:38
Ayoyin
1Sar 6:38A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.
- Shekaru bakwai sau bakwai har zuwa shekarar murnaFir 25:8
Ayoyin
Fir 25:8“ ‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara.
Sau bakwai da bakwai-bakwai
- Lamek: za a rama wa Kayinu sau bakwai, Lamek kuwa sau saba’in da bakwaiFar 4:24
Ayoyin
Far 4:24Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.”
- Bakwai-bakwai na kowace dabba mai tsabta a cikin jirgiFar 7:2
Ayoyin
Far 7:2Ka ɗauki bakwai na kowace iri tsabtaccen dabba tare da kai, namiji da ta mace, da kuma biyu na kowace dabba marar tsabta, namiji da ta mace,
- Ibrahim ya ba Abimelek ’yan tumaki mata bakwaiFar 21:28–30
Ayoyin
Far 21:28–30Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke, sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.”
- Yaƙub ya rusuna har ƙasa sau bakwai a gaban IsuwaFar 33:3
Ayoyin
Far 33:3Shi kansa ya sha gabansu, ya rusuna har ƙasa sau bakwai, kafin ya kai kusa da inda ɗan’uwansa Isuwa yake.
- Mafarkin Fir’auna: shanu bakwai da zangarku bakwaiFar 41:2–7
Ayoyin
Far 41:2–7sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul, suka fito daga kogin, suna kiwo a cikin kyauro. Bayansu, sai ga waɗansu shanu bakwai, munana, ramammu, suka fito daga Nilu, suka tsaya kusa da waɗancan masu ƙiban, a bakin kogin. Shanun nan da suke munana ramammu, suka cinye shanu bakwai nan masu ƙiba mulmul. Sai Fir’auna ya farka. Ya sāke yin barci, sai ya yi mafarki na biyu; ya ga kawuna bakwai na dawa, ƙosassu masu kyau, suka yi girma a kara guda. Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai na dawa, suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta sa suka yanƙwane. Siraran dawan suka haɗiye kawuna bakwai nan ƙosassu masu kyau. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne.
- Firist yakan yayyafa jini da mai sau bakwaiFir 4:6, Fir 14:16
- Bala’am ya nemi bagadai bakwai, bijimai bakwai, raguna bakwaiƘid 23:1
Ayoyin
Ƙid 23:1Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”
- Firistoci bakwai, ƙahoni bakwai, kewaye Yeriko sau bakwaiYosh 6:4, Yosh 6:15–16
Ayoyin
Yosh 6:4Ka sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni raguna su kasance a gaban akwatin alkawari. A rana ta bakwai sai ku zaga birnin sau bakwai, firistocin suna busa ƙahoni.
Yosh 6:15–16A rana ta bakwai, suka tashi da sassafe suka zaga birnin sau bakwai yadda suka saba. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai. A zagawa ta bakwai, da firistoci suka busa ƙahoni, sai Yoshuwa ya ba sojojin umarni ya ce, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin!
- Kitso bakwai na SamsonMah 16:13, Mah 16:19
Ayoyin
Mah 16:13Sa’an nan Delila ta ce, “Har yanzu, ka mai da shashasha, kana mai da ni wawiya kana kuma yin mini ƙarya. Ka gaya mini yadda za a daure ka mana.” Ya ce mata, “In kin yi kitson gashin kaina guda bakwai kika ɗaura su da zare kika buga su da akwasha, zan rasa ƙarfi in zama kamar kowa.” Saboda haka yayinda yake barci, sai Delila ta yi kitson gashin kansa guda bakwai ta ɗinka su da zare,
Mah 16:19Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.
- Bawan Iliya ya duba wajen teku sau bakwai1Sar 18:43–44
Ayoyin
1Sar 18:43–44Ya ce wa bawansa, “Tafi ka dubi wajen teku.” Sai bawan ya haura ya duba. Ya ce, “Ba kome a can.” Sau bakwai Iliya ya ce, “Koma.” Sau na bakwai, bawan ya ce, “Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku.” Sai Iliya ya ce, “Je ka faɗa wa Ahab, ‘Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama yă tare ka.’ ”
- Ɗan matar Shunam ya yi atishawa sau bakwai2Sar 4:35
Ayoyin
2Sar 4:35Elisha ya tashi, ya yi ta kai komo a cikin ɗakin. Sa’an nan ya sāke koma kan gadon yă miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa sau bakwai, ya kuma buɗe idanunsa.
- Na’aman ya yi wanka a Urdun sau bakwai2Sar 5:10, 2Sar 5:14
- Nebukadnezzar ya sa a ƙara zafin tanderu sau bakwaiDan 3:19
Ayoyin
Dan 3:19Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā.
- Bābānni bakwai da hakimai bakwai a fādar ZerzesEsta 1:10, Esta 1:14
Ayoyin
Esta 1:10A rana ta bakwai, sa’ad da Sarki Zerzes, ya yi tilis da ruwan inabi, sai ya umarci bābānni bakwai waɗanda suke yin masa hidima, wato, Mehuman, Bizta, Harbona, Bigta, Abagta, Zetar da Karkas,
Esta 1:14suke kuma mafi kusa da sarki. Waɗannan masu hikima kuwa su ne, Karshena, Shetar, Admata, Tarshish, Meres, Marsena da kuma Memukan. Su hakimai bakwai ne na Farisa da Mediya waɗanda suke da dama ta musamman ta kaiwa ga sarki, suke kuma da matsayi mafi girma a masarautar.
- Ka yafe ba sau bakwai kawai ba, amma fiye da haka nesaMat 18:21–22
Ayoyin
Mat 18:21–22Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?” Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.
- Burodi bakwai, da kwanduna bakwai cike da gutsattsari da suka rageMat 15:34–37
Ayoyin
Mat 15:34–37Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.” Ya sa taron su zazzauna a ƙasa. Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane. Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai.
- An zaɓi mutane bakwai su yi hidima ga masu bi na UrushalimaAyy M 6:3
Ayoyin
Ayy M 6:3’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki
- ’Ya’ya maza bakwai na SikebaAyy M 19:14
Ayoyin
Ayy M 19:14’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.