Bincika › Jigogi › Salkuna, tuluna da kwalabai
Abubuwan ban mamaki
Salkuna, tuluna da kwalabai a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (31), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Salkuna domin ruwa, ruwan inabi da madara
- Ibrahim ya ba Hagar burodi da salkar ruwaFar 21:14
Ayoyin
Far 21:14Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.
- Sa’ad da salkar ta ƙare, ta ga rijiya ta cika taFar 21:15, Far 21:19
- Yayel ta ba Sisera abin sha daga salkar madaraMah 4:19
Ayoyin
Mah 4:19Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi.
- Gibeyonawa sun nuna tsofaffin salkunan ruwan inabi, tsattsagaggu da aka ɗinkaYosh 9:4, Yosh 9:13
Ayoyin
Yosh 9:4sai suka shirya wata dabara ta ruɗu, suka shirya ɗan abinci don tafiya, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu da suka sha ɗinki.
Yosh 9:13Waɗannan salkuna kuma da muka cika ruwan inabi, sababbi ne amma duba yadda suka yayyage. Tufafinmu da takalmanmu duk sun yayyage don doguwar tafiya.”
- Hannatu ta kawo Sama’ila Shilo da bijimi, gari da salkar ruwan inabi1Sam 1:24
Ayoyin
1Sam 1:24Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo.
- Mutum uku masu zuwa Betel: awaki, burodi uku da salkar ruwan inabi1Sam 10:3
Ayoyin
1Sam 10:3“Sa’an nan za ka ci gaba daga nan sai ka kai wajen babban itace na Tabor. Waɗansu mutum uku za su sadu da kai a hanyarsu zuwa wurin yin wa Allah sujada a Betel. Ɗaya yana ɗauke da ’yan awaki uku, ɗaya yana ɗauke da burodi uku, ɗayan kuma yana ɗauke da salkar ruwan inabi.
- Yesse ya aiki Dawuda wurin Shawulu da burodi, salkar ruwan inabi da ɗan akuya1Sam 16:20
Ayoyin
1Sam 16:20Saboda haka Yesse ya ɗauki jaki tare da burodi da ruwan inabi da ɗan ƙarami bunsuru ya ba wa ɗansa Dawuda yă kai wa Shawulu.
- Abigiyel ta kawo wa Dawuda salkar ruwan inabi biyu da abinci mai yawa1Sam 25:18
Ayoyin
1Sam 25:18Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna.
- Ziba ya taryi Dawuda da jakuna ɗauke da kaya da salkar ruwan inabi2Sam 16:1
Ayoyin
2Sam 16:1Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.
- Yesu: ba wanda yake zuba sabon ruwan inabi cikin tsofaffin salkunaMat 9:17, Mar 2:22, Luk 5:37–38
Ayoyin
Mat 9:17Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yă zube salkunan kuma su lalace. A’a, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.”
Mar 2:22Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.”
Luk 5:37–38Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace. A’a, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna.
- Elihu: cikina yana shirin fashewa kamar sabuwar salkar ruwan inabiAyu 32:19
Ayoyin
Ayu 32:19a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba, kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa.
- Mai zabura: kamar salkar ruwan inabi a cikin hayaƙiZab 119:83
Ayoyin
Zab 119:83Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba.
- Mai zabura: “ka jera hawayena a littafinka”Zab 56:8
Ayoyin
Zab 56:8Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?
Tuluna da kwalabai
- Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗartaFar 24:15
Ayoyin
Far 24:15Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim.
- Mutanen Gideyon sun ɗauki cociyoyi a cikin tuluna suka farfashe suMah 7:16, Mah 7:19–20
Ayoyin
Mah 7:16Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.
Mah 7:19–20Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu. Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!”
- Sama’ila ya zuba kwalabar mai a kan Shawulu1Sam 10:1
Ayoyin
1Sam 10:1Sai Sama’ila ya ɗauki ’yar kwalabar mai, ya zuba man ɗin wa Shawulu a kansa, ya yi masa sumba yana cewa, “ Ubangiji ya keɓe ka shugaba bisa gādonsa.
- Dawuda ya ɗauki māshi da tulun ruwa daga kan Shawulu da yake barci1Sam 26:12
Ayoyin
1Sam 26:12Saboda haka Dawuda ya ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da Shawulu suka tafi. Ba wanda ya gan su, ba wanda ya san abin da ya faru, ba kuwa wanda ya farka, dukansu suna barci gama Ubangiji ya sa barci mai nauyi ya ɗauke su.
- Gwauruwar Zarefat tana da ɗan gari hannu guda a tulu da ɗan mai1Sar 17:12
Ayoyin
1Sar 17:12Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara ’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.”
- Wata gwauruwa ta zuba mai har tuluna suka ƙare2Sar 4:2–6
Ayoyin
2Sar 4:2–6Elisha ya amsa mata ya ce, “Me kike so in yi miki? Ki faɗa mini, me kike da shi a gidanki?” Sai ta ce, “Baiwarka ba ta da kome a can, sai ɗan tulun man zaitun.” Elisha ya ce, “Ki je wurin dukan maƙwabtanki, ki nemi tulunan da babu kome a ciki. Kada ki nemo kaɗan kawai. Sa’an nan ki shiga ciki, ki kulle ƙofar da ke da ’ya’yanki kuke ciki. Ku ɗuɗɗura man a dukan tulunan, sa’ad da kowanne ya cika, sai ki ajiye a gefe.” Ta tashi ta shiga tare da ’ya’yanta maza, suka kulle ƙofa. ’Ya’yanta suka kawo mata tuluna, ita kuma tana ɗurawa. Da dukan tulunan suka cika, sai ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tulu.” Amma ya amsa ya ce, “Ai, ba saura.” Sa’an nan man ya daina zuba.
- Elisha ya aiki wani matashin annabi da kwalabar mai zuwa Ramot Gileyad2Sar 9:1
Ayoyin
2Sar 9:1Sai Elisha ya kira wani daga cikin ƙungiyar annabawa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kwalabar mai ka je Ramot Gileyad.
- Irmiya ya sayi tulun yumɓu na maginin tukwane ya farfashe shi a gaban dattawaIrm 19:1, Irm 19:10
- A Kana tulunan dutse shida, kowanne gallon ashirin zuwa talatin, an cika su har bakiYoh 2:6–7
Ayoyin
Yoh 2:6–7Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin. Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.
- Wani mutum mai ɗauke da tulun ruwa zai ja-goranci almajiraiMar 14:13
Ayoyin
Mar 14:13Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.
- Matar Samariya ta bar tulun ruwanta ta tafi gariYoh 4:28
Ayoyin
Yoh 4:28Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane,
- Wata mace ta fasa kwalabar alabastar ta turaren nard ta zuba a kan YesuMar 14:3
Ayoyin
Mar 14:3Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.