Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Ƙattai

Abubuwan ban mamaki

Ƙattai a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (29), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanakiFar 6:4
    Ayoyin
    Far 6:4Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.
  • ’Yan leƙen asiri: mun zama kamar fāra a gaban zuriyar AnakƘid 13:32–33
    Ayoyin
    Ƙid 13:32–33Sai suka yaɗa labari marar kyau ga Isra’ilawa game da ƙasar da suka binciko. Suka ce, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zama a cikinta. Dukan mutanen da muka gani a wurin, ƙatti ne. Mun ga Nefilimawa a can (zuriyar Anak sun fito ne daga Nefilim). Sai muka ga kanmu kamar fāra ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”
  • Anakawa: mutane masu ƙarfi da tsayiM Sh 1:28, M Sh 9:2
    Ayoyin
    M Sh 1:28Ina za mu? ’Yan’uwanmu suka sa muka fid da zuciya. Suka ce, ‘Mutanen sun fi mu ƙarfi, sun kuma fi mu tsayi; biranen manya ne, da katanga har sama. Mun ma ga Anakawa a can.’ ”
    M Sh 9:2Mutane ne masu ƙarfi, kuma dogaye, zuriyar Anakawa! Ai, kun ji akan ce, “Wa zai iya tsayayya da Anakawa?”
  • Emawa, dogaye kamar Anakawa, sun zauna a MowabM Sh 2:10–11
    Ayoyin
    M Sh 2:10–11(Emawa, mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa, dā sun zauna a can. Kamar Anakawa, su ma an ɗauka su Refahiyawa ne, amma Mowab suna kiransu Emawa.
  • Ammonawa sun kira Refahiyawa na ƙasarsu ZamzummawaM Sh 2:20–21
    Ayoyin
    M Sh 2:20–21(Wannan ita ma a ɗauka ta a matsayin ƙasar Refahiyawa waɗanda dā sun zauna a can ne; amma Ammonawa suna ce da su Zamzummawa. Mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa. Ubangiji ya hallaka su daga gaban Ammonawa, waɗanda suka kore su, suka kuma zauna a wurinsu.
  • Kedorlayomer ya ci Refahiyawa, Zuziyawa da Emawa da yaƙiFar 14:5
    Ayoyin
    Far 14:5A shekara ta goma sha huɗu, Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi suka tafi suka cinye Refahiyawa a Ashterot Karnayim, Zuziyawa a Ham, Emawa a Shabe Kiriyatayim,

Og na Bashan

  • Og, sarkin Bashan, shi ne na ƙarshe cikin RefahiyawaM Sh 3:11, Yosh 12:4
    Ayoyin
    M Sh 3:11(Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)
    Yosh 12:4Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.
  • Gadonsa na ƙarfe tsawonsa kamu tara ne, fāɗinsa kamu huɗuM Sh 3:11
    Ayoyin
    M Sh 3:11(Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)
  • Isra’ila sun ci Og a Edireyi suka ƙwace garuruwansa sittinƘid 21:33–35, M Sh 3:1–4
    Ayoyin
    Ƙid 21:33–35Sai suka juya suka haura kan hanya ta zuwa Bashan, inda Og yake sarauta, ya kuwa fito tare da dukan sojojinsa suka yi yaƙi da Isra’ila a Edireyi. Ubangiji ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na ba da shi a gare ka, da dukan sojojinsa da kuma ƙasarsa. Ka yi da shi yadda ka yi da Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.” Ta haka suka kashe shi, tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa, ba wanda ya ragu. Suka kuma mamaye ƙasarsa.
    M Sh 3:1–4Biye da wannan muka juya muka haura ta hanyar wajen Bashan, inda Og, sarkin Bashan tare da dukan mayaƙansa suka fito don su sadu da mu a yaƙi, a Edireyi. Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ji tsoronsa, gama na riga na miƙa shi da dukan mayaƙansa da kuma ƙasarsa gare ka. Yi masa abin da ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon.” Saboda haka Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, sarkin Bashan da dukan mayaƙansa a hannuwanmu. Muka karkashe su, ba mu bar wani da rai ba. A wannan lokaci muka kwashe dukan biranensa. Babu ɗaya daga birane sittin da ba mu ɗauke daga gare su ba, dukan yankin Argob, masarautar Og a Bashan.
  • Ƙasarsa ta zama ta Ruben, Gad da rabin ManasseƘid 32:33, M Sh 29:7–8
    Ayoyin
    Ƙid 32:33Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.
    M Sh 29:7–8Sa’ad da kuka kai wannan wuri, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan, suka fito don su yi yaƙi da mu, amma muka ci su da yaƙi. Muka ƙwace ƙasarsu, muka ba da ita gādo ga mutanen Ruben, mutanen Gad, da kuma rabin mutanen Manasse.

Hebron da Anakawa

  • Dā ana kiran Hebron Kiriyat Arba, sunan Arba, mafi girma cikin AnakawaYosh 14:15, Yosh 15:13
    Ayoyin
    Yosh 14:15(Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi.
    Yosh 15:13Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne wuri a Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron, bisa ga umarnin Ubangiji. (Arba shi ne mahaifin Anak.)
  • Kaleb ya kori ’ya’yan Anak maza uku: Sheshai, Ahiman, TalmaiYosh 15:14, Mah 1:20
    Ayoyin
    Yosh 15:14Daga can sai Kaleb ya kori ’ya’yan Anak, maza su uku daga Hebron, wato, Sheshai, Ahiman da Talmai.
    Mah 1:20Yadda Musa ya yi alkawari, sai aka ba Kaleb Hebron, wanda ya kori daga cikinta ’ya’ya maza uku na Anak.
  • Yoshuwa ya kawar da Anakawa; waɗansu sun ragu a Gaza, Gat da AshdodYosh 11:21–22
    Ayoyin
    Yosh 11:21–22A lokacin nan Yoshuwa ya je ya hallaka Anakawa daga ƙasar tudu. Daga Hebron, Debir da Anab. Daga dukan ƙasar tuddai na Yahuda, da kuma dukan ƙasar tudu ta Isra’ila, Yoshuwa ya hallaka su duka da garuruwansu. Ba a bar waɗansu Anakawa a harabar Isra’ila ba; sai dai a Gaza, Gat da Ashdod ne aka samu waɗanda suka ragu da rai.

Goliyat da danginsa

  • Tsayin Goliyat daga Gat kamu shida da taƙi ne1Sam 17:4
    Ayoyin
    1Sam 17:4Wani jarumin da ake kira Goliyat wanda ya fito daga Gat, ya fita daga sansanin Filistiyawa. Tsawonsa ya fi ƙafa tara.
  • Nauyin sulkensa shekel dubu biyar ne1Sam 17:5
    Ayoyin
    1Sam 17:5Ya sa hular kwanon da aka yi da tagulla, da rigar ƙarfe mai sulke, nauyin rigar ya kai shekel dubu biyar.
  • Nauyin kan māshinsa shekel ɗari shida ne1Sam 17:7
    Ayoyin
    1Sam 17:7Ƙotar kibiyarsa kuwa kamar sandar saƙar igiya take, ƙarfen kibiyar kuma nauyinsa ya kai shekel ɗari shida. Mai riƙe masa garkuwa yana tafe a gabansa.
  • Kwana arba’in yakan fito kowace safiya da yamma1Sam 17:16
    Ayoyin
    1Sam 17:16Kwana arba’in cif, Bafilistin nan ya yi ta fitowa kowane safe da kuma kowace yamma.
  • Dawuda ya kashe shi da majajjawa da dutse1Sam 17:49–50
    Ayoyin
    1Sam 17:49–50Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki. Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.
  • Daga baya an ajiye takobin Goliyat naɗe a bayan Efod1Sam 21:9
    Ayoyin
    1Sam 21:9Sai firist ya ce, “Takobin Goliyat Bafilistin nan wanda ka kashe a Kwarin Ela yana nan. An naɗe shi da ƙyallen aka ajiye a bayan Efod, in kana so, sai ka ɗauka. Ba wani takobi kuma sai wancan.” Dawuda ya ce, “Ba ni shi, ai, ba wani kamar sa.”
  • Nauyin māshin tagulla na Ishbi-Benob shekel ɗari uku ne; Abishai ya kashe shi2Sam 21:16–17
    Ayoyin
    2Sam 21:16–17Ishbi-Benob kuwa, wani daga zuriyar Rafa, wanda nauyin kan māshinsa na tagulla ya yi shekel ɗari uku, wanda yake kuma da sabon māshi, ya ce zai kashe Dawuda. Amma Abishai ɗan Zeruhiya ya kawo wa Dawuda gudummawa; ya bugi Bafilistin, ya kashe shi. Sa’an nan mutanen Dawuda suka rantse masa suka ce, “Ba za ka ƙara fita tare da mu wurin yaƙi ba, don kada fitilar Isra’ila tă mutu.”
  • Elhanan ya kashe Lahmi, ɗan’uwan Goliyat1Tar 20:5
    Ayoyin
    1Tar 20:5Yaƙi kuma ya sāke tashi tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, Elhanan ɗan Yayir ya kashe Lahmi ɗan’uwan Goliyat mutumin Gat, wanda yake riƙe da māshi mai sandan masaƙa.
  • Wani mutum a Gat yana da yatsotsi shida a kowane hannu, shida a kowace ƙafa2Sam 21:20–21, 1Tar 20:6–7
    Ayoyin
    2Sam 21:20–21Har wa yau a wani yaƙin da aka yi a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu, da kuma yatsotsi shida a kowane ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriya Rafa ne. Da ya yi wa Isra’ila reni, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwa Dawuda, ya kashe shi.
    1Tar 20:6–7Aka sāke yin wani yaƙin kuma, wanda ya faru a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu da kuma yatsotsi shida a kowace ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriyar Rafa ce. Sa’ad da ya yi wa Isra’ila ba’a, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda ya kashe shi.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.