Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Mafarkai

Abubuwan ban mamaki

Mafarkai a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (36), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Mayunwaci yakan yi mafarki yana ci, sa’an nan ya farka da yunwaIsh 29:8
    Ayoyin
    Ish 29:8kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci, amma sai ya farka, yunwan tana nan; kamar sa’ad da mai ƙishirwa yana mafarki cewa yana shan ruwa, amma sai ya farka yana suma, da ƙishinsa. Haka zai zama da sojoji na dukan al’ummai da suka yi yaƙi da Dutsen Sihiyona.
  • Mafarki yakan zo saboda damuwa mai yawaM Had 5:3
    Ayoyin
    M Had 5:3Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa, haka jawabin wawa yake sa’ad da yake yawan magana.
  • Doka game da mai mafarki da yake zuga a bi waɗansu alloliM Sh 13:1–5
    Ayoyin
    M Sh 13:1–5In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi, in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,” kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku. Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa. Dole a kashe wannan annabi ko mai mafarki, domin ya yi wa’azin tawaye ga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, ya fanshe ku daga ƙasar bauta; gama annabin nan ya yi ƙoƙari yă juye daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, ku bi. Dole ku fid da mugu daga cikinku.
  • Irmiya game da annabawan da suke ta cewa, “Na yi mafarki! Na yi mafarki!”Irm 23:25–28
    Ayoyin
    Irm 23:25–28“Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’ Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu? Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada. Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji.

Mafarkan da Littafi Mai Tsarki ya ba da labarinsu

  • An gargaɗi Abimelek a mafarki game da SaratuFar 20:3
    Ayoyin
    Far 20:3Amma wata rana da dad dare Allah ya zo wa Abimelek a cikin mafarki ya ce masa, “Kai da matacce ɗaya kuke, saboda matar da ka ɗauka. Ita matar aure ce.”
  • Yaƙub ya yi mafarkin matakalar da ta kai samaFar 28:12
    Ayoyin
    Far 28:12Ya yi mafarki inda ya ga wata matakalar hawa, tsaye a ƙasa, kanta ta kai sama, mala’ikun Allah kuwa suna hawa, suna sauka a kanta.
  • Yaƙub ya yi mafarkin garkuna masu dabbare-dabbare, masu ɗigo-ɗigo da masu tabo-taboFar 31:10–13
    Ayoyin
    Far 31:10–13“A lokacin ɗaukar cikin garken, na taɓa yin mafarki inda na ga bunsuran da suke barbara da garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne. Sai mala’ikan Allah ya ce mini a mafarkin, ‘Yaƙub.’ Sai na amsa na ce, ‘Ga ni.’ Ya ce, ‘Ɗaga idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne, gama na ga dukan abin da Laban yake yin maka. Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa al’amudi mai, da kuma inda ka yi mini alkawari. Yanzu ka bar wannan ƙasa nan take, ka koma ƙasarka ta ainihi.’ ”
  • An gargaɗi Laban a mafarki kada ya cuci YaƙubFar 31:24
    Ayoyin
    Far 31:24Sai Allah ya bayyana ga Laban mutumin Aram a mafarki da dare, ya ce masa, “Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu, ko mai kyau ko marar kyau.”
  • Yusuf ya yi mafarkin dammuna suna rusuna wa dammensaFar 37:5–8
    Ayoyin
    Far 37:5–8Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi. Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.” Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.
  • Yusuf ya yi mafarkin rana, wata da taurari goma sha ɗaya suna rusunaFar 37:9–10
    Ayoyin
    Far 37:9–10Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.” Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?”
  • Mai shayarwa ya yi mafarkin kuringar inabi mai rassa ukuFar 40:9–13
    Ayoyin
    Far 40:9–13Sai shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusuf mafarkinsa. Ya ce masa, “A cikin mafarkina, na ga kuringa a gabana, kuma a kuringar, akwai rassa uku. Nan da nan kuringar ta yi toho, ta huda, ta kuma yi nonna har suka nuna, suka zama inabi. Kwaf Fir’auna kuwa yana a hannuna, na kuma ɗiba inabin na matse su cikin kwaf Fir’auna, na kuma sa kwaf ɗin a hannunsa.” Yusuf ya ce masa, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Rassan nan uku, kwana uku ne. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa.
  • Mai toya burodi ya yi mafarkin kwanduna uku na burodi a kansaFar 40:16–19
    Ayoyin
    Far 40:16–19Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga cewa Yusuf ya ba da fassara mai gamsarwa, sai ya ce, wa Yusuf, “Ni ma na yi mafarki. A kaina, akwai kwanduna uku na burodi. A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.” Yusuf ya ce, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Kwanduna uku, kwanaki uku ne. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’ ”
  • Fir’auna ya yi mafarkin shanu bakwai masu ƙiba da bakwai ramammuFar 41:1–4
    Ayoyin
    Far 41:1–4Bayan shekaru biyu cif, Fir’auna ya yi mafarki. A mafarkin, ya ga yana tsaye kusa da Nilu, sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul, suka fito daga kogin, suna kiwo a cikin kyauro. Bayansu, sai ga waɗansu shanu bakwai, munana, ramammu, suka fito daga Nilu, suka tsaya kusa da waɗancan masu ƙiban, a bakin kogin. Shanun nan da suke munana ramammu, suka cinye shanu bakwai nan masu ƙiba mulmul. Sai Fir’auna ya farka.
  • Sa’an nan zangarku bakwai masu ƙwari da bakwai marasa ƙwariFar 41:5–7
    Ayoyin
    Far 41:5–7Ya sāke yin barci, sai ya yi mafarki na biyu; ya ga kawuna bakwai na dawa, ƙosassu masu kyau, suka yi girma a kara guda. Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai na dawa, suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta sa suka yanƙwane. Siraran dawan suka haɗiye kawuna bakwai nan ƙosassu masu kyau. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne.
  • Wani mutumin Midiyan ya yi mafarkin wainar sha’ir ta kifar da tentiMah 7:13–14
    Ayoyin
    Mah 7:13–14Gideyon ya iso daidai wani yana faɗa wa wani aboki mafarkinsa, yana cewa, “Na yi mafarki, na ga dunƙule burodin sha’ir ya fāɗo a tsakiyar sansanin Midiyawa. Ya bugi tentin da ƙarfin da ya sa tenti ta kife a ƙasa.” Abokinsa ya ce, “Ai wannan ba wani abu ba ne fiye da takobin Gideyon ɗan Yowash, mutumin Isra’ila. Allah ya ba da Midiyawa da dukan sansani a hannuwansa.”
  • A Gibeyon Solomon ya roƙi hikima a mafarki1Sar 3:5–15
    Ayoyin
    1Sar 3:5–15A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.” Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana. “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?” Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba. Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna. In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.” Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne. Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki.
  • Nebukadnezzar ya bukaci masu hikimarsa su faɗa masa mafarkin kansaDan 2:1–9
    Ayoyin
    Dan 2:1–9A shekara ta biyu ta mulkinsa, Nebukadnezzar ya yi mafarkai; hankalinsa ya tashi har ya kāsa barci. Sai sarki ya sa aka tattara masa masu sihiri da masu dabo da bokaye da masanan taurari domin su faɗi abin da ya yi mafarki a kai. Da suka shigo suka tsaya a gaban sarki, sai ya ce musu, “Na yi mafarkin da ya dame ni kuma ina so in san me yake nufi.” Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki da Arameyanci “Ran sarki yă daɗe! Ka faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma sai mu fassara.” Sai sarki ya amsa wa masanan taurarin ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa-gunduwa, a mai da gidajenku juji. Amma in har kuka faɗa mini mafarkina kuka kuma bayyana fassararsa, za ku sami lada mai girma. Saboda haka ku faɗa mini mafarkin da kuma fassararsa.” Sai suka sāke amsa masa suka ce, “Ran sarki yă daɗe, faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma za mu fassara shi.” Sai sarki ya amsa ya ce, “Na gane cewa kuna ƙoƙari ku ɓata lokaci ne kawai domin ku ga na manta da abin. In ba ku faɗa mini mafarkin ba, akwai hukunci guda ɗaya kurum dominku. Kun haɗa baki domin ku faɗa mini munanan al’amura domin ku ruɗe ni har lokaci yă wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.”
  • Mafarkinsa na babban mutum-mutumi na zinariya, azurfa, tagulla, ƙarfe, yumɓuDan 2:31–35
    Ayoyin
    Dan 2:31–35“Ya sarki, ka ga wata babbar siffa, mai girma, siffa ce mai haske, abar bantsoro tana tsaye a gabanka. An yi kan wannan siffa da zinariya zalla, ƙirjinta da kuma hannuwanta an yi su da azurfa, cikinta da kuma cinyarta da tagulla ne. An yi ƙafafun da ƙarfe, tafin ƙafafunta kuma an yi rabi da ƙarfe rabi kuma da yumɓu. A lokacin da kake dubawa, sai aka yanko wani dutse, amma ba da hannun mutum ba. Ya fāɗa a kan ƙafafun siffar na ƙarfen da aka haɗa da yumɓu aka kuma ragargaje su. Sai ƙarfen da yambun da tagulla da azurfan da kuma zinariyan suka ragargaje a lokaci ɗaya ya zama kamar ƙaiƙayi a masussuka a lokacin kaka. Sai iska ta kwashe su ta tafi, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma dutsen da ya fāɗo a siffar ya girke ya zama tsauni ya kuma cika dukan duniya.
  • Mafarkinsa na babban itacen da aka sareDan 4:10–17
    Ayoyin
    Dan 4:10–17Waɗannan su ne wahayin da na gani a lokacin da nake kwance a gadona, na duba, a gabana kuwa ga wani itace a kafe a tsakiyar duniya, yana da tsawo ƙwarai. Itacen ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, har tsayinsa ya taɓa sarari sama; ana iya ganinsa a ko’ina a duniya. Ganyayensa suna da kyau, yana da ’ya’ya jingim, abinci kuma domin kowa da kowa. A ƙarƙashinsa namun jeji suke samun wurin hutawa, kuma tsuntsayen sama suna zaune a bisa rassansa; daga cikinsa kowace halitta take cin abinci. “A cikin wahayin da gani sa’ad da nake kwance a kan gadona, Na duba, a gabana kuwa ga wani ɗan saƙo, mai tsarki, yana saukowa daga sama. Sai ya yi kira da babbar murya ya ce, ‘A sare itacen a kuma yayyanka rassansa; a karkaɗe ganyensa a kuma warwatsar da ’ya’yansa. Bari dabbobi su tashi daga ƙarƙashinsa da kuma tsuntsayen da suke a rassansa. Amma a bar kututturen da kuma saiwoyinsa, a daure shi da ƙarfe da kuma tagulla, a bar shi a cikin ƙasa, a cikin ciyayin filaye. “ ‘Bari yă jiƙu da raɓar, bari yă zauna cikin dabbobi tare da tsire-tsiren duniya. Bari a canja tunaninsa irin na mutane a ba shi tunani irin na dabbobi, har sau bakwai su wuce a kansa. “ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’
  • Daniyel ya rubuta mafarkin namomi huɗuDan 7:1–3
    Ayoyin
    Dan 7:1–3A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa. Daniyel ya ce, “A cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga kusurwoyi huɗu na sama suna gurɓata babban teku. Sai ga dabbobi huɗu, kowannensu ya yi dabam da sauran, suna fitowa daga teku.
  • An gaya wa Yusuf a mafarki ya ɗauki Maryamu matarsaMat 1:20–21
    Ayoyin
    Mat 1:20–21Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”
  • An gargaɗi Masanan nan a mafarki kada su koma wurin HiridusMat 2:12
    Ayoyin
    Mat 2:12Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
  • An gaya wa Yusuf a mafarki ya gudu zuwa Masar, sa’an nan ya dawoMat 2:13, Mat 2:19–22
    Ayoyin
    Mat 2:13Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”
    Mat 2:19–22Bayan Hiridus ya mutu, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar, ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Isra’ila, domin waɗanda suke neman ran yaron sun mutu.” Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Isra’ila. Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili,
  • Matar Bilatus ta sha wahala a mafarki saboda YesuMat 27:19
    Ayoyin
    Mat 27:19Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”

Wahayoyi da dare

  • Allah ya yi magana da Yaƙub da dare game da gangarawa zuwa MasarFar 46:2–4
    Ayoyin
    Far 46:2–4Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!” Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.” Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama zan mai da kai al’umma mai girma a can. Zan gangara zuwa Masar tare da kai, tabbatacce zan sāke dawo da kai. Kuma hannun Yusuf zai rufe idanunka.”
  • Elifaz ya ji raɗa cikin wahayoyi na dareAyu 4:12–16
    Ayoyin
    Ayu 4:12–16“Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji. Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan. Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa. Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi. Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya.
  • Bulus ya ga wani mutumin Makidoniya yana cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu”Ayy M 16:9
    Ayoyin
    Ayy M 16:9Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.”
  • A cikin hadari wani mala’ika ya gaya wa Bulus cewa dukan waɗanda suke cikin jirgi za su rayuAyy M 27:23–24
    Ayoyin
    Ayy M 27:23–24Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shari’a; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’

Masu fassara

  • Yusuf ya fassara mafarkan mai shayarwa da mai toya burodiFar 40:8, Far 40:12–13, Far 40:18–19
    Ayoyin
    Far 40:8Sai suka amsa, “Mu biyu, mun yi mafarki, amma babu wani da zai fassara mana su.” Sa’an nan Yusuf ya ce musu, “Fassara ba daga Allah take zuwa ba? Ku faɗa mini mafarkanku.”
    Far 40:12–13Yusuf ya ce masa, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Rassan nan uku, kwana uku ne. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa.
    Far 40:18–19Yusuf ya ce, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Kwanduna uku, kwanaki uku ne. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’ ”
  • Yusuf ya fassara mafarkan Fir’auna: shekara bakwai na yalwa, bakwai na yunwaFar 41:25–32
    Ayoyin
    Far 41:25–32Sai Yusuf ya ce wa Fir’auna, “Mafarkan Fir’auna, ɗaya ne. Allah ya bayyana wa Fir’auna abin da yake shirin yi. Shanu masu kyau nan, shekaru bakwai ne, kawunan dawa bakwai ƙosassun nan kuwa shekaru bakwai ne; mafarkan iri ɗaya ne. Shanun nan ramammu, munana, da suka zo daga baya, shekaru bakwai ne, haka ma kawuna dawan nan shanyayyu da iskar gabas ta yanƙwane. Shekaru ne bakwai na yunwa. “Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir’auna cewa Allah ya nuna wa Fir’auna abin da yake shirin yi. Shekaru bakwai na yalwar abinci suna zuwa a dukan ƙasar Masar, amma shekaru bakwai na yunwa za su biyo bayansu. Tsananin yunwar za tă sa a manta da dukan isashen abincin da aka samu a ƙasar Masar, yunwa kuwa za tă rufe dukan ƙasar. Ba za a tuna da isashen abincin da aka samu a ƙasar ba, domin yunwar da za tă biyo baya za tă zama da tsanani ƙwarai. Dalilin da aka ba wa Fir’auna mafarkan nan kashi biyu kuwa shi ne cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin. Allah zai aikata shi, ba da daɗewa ba.
  • Daniyel ya faɗa wa Nebukadnezzar mafarkinsa, sa’an nan ya bayyana shiDan 2:27–30, Dan 2:36, Dan 4:19–24
    Ayoyin
    Dan 2:27–30Daniyel ya amsa, “Babu wani mai hikima, ko mai sihiri, ko mai dabo ko mai duban da zai iya warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi, amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne, “A sa’ad da kake kwance, ya sarki, tunaninka ya ga al’amuran da suke zuwa, kuma shi mai bayyana al’amuran ya bayyana maka asiran abubuwan da za su faru. Amma ba a bayyana mini wannan asiri saboda ina da wata hikima fiye da sauran mutane ba, sai dai domin a sanar wa sarki da fassarar, ka kuma san tunanin da ya shiga zuciyarka.
    Dan 2:36“Wannan shi ne mafarkin, yanzu kuma za mu fassara ta wa sarki.
    Dan 4:19–24Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan! Itacen da ka gani; wanda ya yi girma da ƙarfe, da tsayinsa ya taɓa sararin sama, wanda ana ganinsa ko’ina a duniya, wanda ganyayensa masu kyau ne yana da ’ya’yan itace da yawa, wanda yake ba da abinci ga duka, yana ba da wurin hutu ga namun jeji, kuma rassansa suna ɗauke da sheƙar tsuntsayen sama. Ya sarki kai ne itacen nan! Ka yi girma da ƙarfi; girmanka kuma ta kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko’ina a duniya. “Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’ “Ga fassarar, ya sarki, wannan ita ce doka wadda Mafi Ɗaukaka ya bayar a kan ranka yă daɗe, sarkina.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.