Abubuwan ban mamaki
Rijiyoyi a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (20), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Hagar ta ga rijiya ta ba yaron ruwa ya shaFar 21:19
Ayoyin
Far 21:19Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha.
- Ibrahim ya ba da ’yan tumaki bakwai shaida cewa shi ya haƙa rijiyar a BeyershebaFar 21:25–31
Ayoyin
Far 21:25–31Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace. Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.” Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya. Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke, sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.” Saboda haka aka kira wurin Beyersheba, domin a nan ne su biyun suka yi rantsuwa.
- Filistiyawa sun toshe rijiyoyin Ibrahim; Ishaku ya sāke buɗe suFar 26:15, Far 26:18
Ayoyin
Far 26:15Saboda haka dukan rijiyoyin da bayin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin da mahaifinsa Ibrahim yake da rai, Filistiyawa sun toshe su, suka kuma ciccike su da ƙasa.
Far 26:18Ishaku ya sāke tona rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa suka tattoshe bayan mutuwar Ibrahim, ya kuma sa musu sunayen da mahaifinsa ya ba su.
- Gardama game da rijiyoyi: Esek, Sitna, sa’an nan RehobotFar 26:20–22
Ayoyin
Far 26:20–22Amma makiyayan Gerar suka yi faɗa da na Ishaku suka ce, “Ruwan namu ne!” Saboda haka Ishaku ya ba wa rijiyar suna Esek, domin sun yi faɗa da shi. Sai suka haƙa wata rijiya, amma suka yi faɗa a kanta ita ma, saboda haka ya ce da ita Sitna. Sai Ishaku ya matsa daga can ya sāke haƙa wata rijiyar, babu wani kuma da yi faɗa a kanta. Sai ya ba ta suna Rehobot, yana cewa, “Yanzu Ubangiji ya ba mu wuri, za mu kuwa yi ta haihuwa a ƙasar.”
- Bayin Ishaku sun sami ruwa: Shiba, BeyershebaFar 26:32–33
Ayoyin
Far 26:32–33A wannan rana bayin Ishaku suka zo suka faɗa masa game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, “Mun sami ruwa!” Sai ya kira ta Shiba, don haka har wa yau ana kira garin Beyersheba.
- Rijiyar da ake kira Beyer-Lahai-RoyiFar 16:14
Ayoyin
Far 16:14Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered.
- Rebeka ta zo maɓuɓɓuga da tuluntaFar 24:16
Ayoyin
Far 24:16Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.
- Babban dutse ya rufe bakin rijiyar a HaranFar 29:2–3
Ayoyin
Far 29:2–3A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne. Sa’ad da dukan garkuna suka taru a can, sai makiyayan su gungurar da dutsen daga bakin rijiyar su shayar da tumaki. Sa’an nan su mai da dutsen a wurinsa a bakin rijiya.
- Yaƙub ya mirgine dutsen ya ba garken Rahila ruwaFar 29:10
Ayoyin
Far 29:10Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.
- Musa ya zauna kusa da rijiya a Midiyan ya taimaki ’yan’uwa mata bakwaiFit 2:15–17
Ayoyin
Fit 2:15–17Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya. To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu. Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.
- Isra’ila sun rera waƙa ga rijiya: “Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya!”Ƙid 21:16–18
Ayoyin
Ƙid 21:16–18Daga can, suka gangara zuwa Beyer, wato, rijiyar da Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane duka, zan kuwa ba su ruwa.” Sai Isra’ilawa suka rera wannan waƙa, “Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya! Rera waƙa game da ita, game da rijiyar da ’ya’yan sarki suka haƙa, rijiyar da manyan mutane masu sandunan sarauta suka nuna da sandunansu.” Sa’an nan suka tashi daga hamadar, suka tafi Mattana,
- Ƙasar alkawari tana da rijiyoyin da ba su haƙa baM Sh 6:11
Ayoyin
M Sh 6:11gidaje cike da kowane irin abubuwa masu kyau, da ba ku kuka tanadar ba, rijiyoyin da ba ku kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun da ba ku kuka shuka ba, sa’ad da kuwa kuka ci, kuka kuma ƙoshi,
- ’Yan leƙen asirin Dawuda sun ɓuya a cikin rijiya a Bahurim2Sam 17:18–19
Ayoyin
2Sam 17:18–19Amma wani saurayi ya gan su, ya gaya wa Absalom. Sai dukansu biyu suka tashi da sauri suka shiga gidan wani mutum a Bahurim. Yana da rijiya a cikin gida, sai suka shiga cikinta. Matarsa mutumin kuwa ta kawo tabarma ta shimfiɗa a bakin rijiyar, sai ta kawo hatsi ta baza a kanta. Ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.
- Jarumawa uku sun kawo wa Dawuda ruwa daga rijiyar Betlehem2Sam 23:15–16
Ayoyin
2Sam 23:15–16Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!” Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.
- Uzziya ya haƙa randuna da yawa domin dabbobinsa2Tar 26:10
Ayoyin
2Tar 26:10Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma.
- An jefa Yusuf cikin rami marar ruwaFar 37:24
Ayoyin
Far 37:24suka kuma ɗauke shi suka jefa a cikin rijiya. To, rijiyar wofi ce, babu ruwa a ciki.
- Irmiya ya nutse a cikin laka na rami marar ruwaIrm 38:6
Ayoyin
Irm 38:6Saboda haka suka kama Irmiya suka sa a rijiyar da ba ruwa a ciki ta Malkiya, ɗan sarki, wadda take a sansanin matsara. Suka saukar da Irmiya cikin rijiyar da ba ruwa da igiya; babu ruwa a cikinta, sai laka, Irmiya ya nutse cikin laka.
- Yesu ya zauna kusa da rijiyar Yaƙub wajen sa’a ta shidaYoh 4:6
Ayoyin
Yoh 4:6Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne.
- Matar: ba ka da guga, rijiyar kuma da zurfiYoh 4:11
Ayoyin
Yoh 4:11Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai?
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.