Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Kacici-kacici

Abubuwan ban mamaki

Kacici-kacici a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (15), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Kacici-kacicin Samson

  • Samson ya sami ƙudan zuma da zuma a cikin zakin da ya kasheMah 14:5–9
    Ayoyin
    Mah 14:5–9Sai Samson ya gangara zuwa Timna tare da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Da suka yi kusa da gonar inabin Timna, nan da nan sai ga ɗan zaki ya taso ya nufe shi yana ruri. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa da ƙarfi, ya sa ya yaga zakin kashi biyu da hannu kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Sai dai bai gaya wa iyayensa abin da ya yi ba. Sa’an nan ya gangara ya yi magana da yarinyar, yana kuwa sonsa. Daga baya, da ya koma don yă aure ta, sai ya ratse don yă ga gawar zakin. Sai ga taron ƙudan zuma da zuma a ciki, wanda ya sa hannu ya ɗebo yana tafiya yana sha. Sa’ad da ya iso wurin iyayensa, ya ba su zuman, su ma suka sha. Sai dai bai gaya musu cewa ya ɗebo zuman daga gawar zaki ba.
  • Caca: riguna talatin na lilin da tufafi talatin na sakawaMah 14:12–13
    Ayoyin
    Mah 14:12–13Sai Samson ya ce, “Bari in yi muku kacici-kacici, in kun ba ni amsa cikin kwana bakwai na wannan biki, zan ba ku riguna lilin talatin da kuma tufafi talatin. In kuma ba ku iya ba ni amsar ba, dole ku ba ni rigunan lilin talatin da tufafi talatin.” Suka ce, “Ka gaya mana kacici-kacicin.”
  • “Daga mai ci, abinci ya fito”Mah 14:14
    Ayoyin
    Mah 14:14Sai ya ce, “Daga mai ci, abinci ya fito; daga mai ƙarfi, abu mai zaki ya fito.” Har kwana uku ba su iya ba da amsa ba.
  • Matarsa ta matsa masa kwana bakwai, sa’an nan ta gaya wa mutanentaMah 14:15–17
    Ayoyin
    Mah 14:15–17A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson “Ki rarrashi mijinki yă bayyana mana kacici-kacicin, ko kuwa mu ƙone ki da gidan mahaifinki duka da wuta. Kun kira mu domin ku yi mana fashi ne?” Sa’an nan matar Samson ta kwanta masa a jiki tana kuka tana cewa, “Kai maƙiyina ne, lalle ba ka ƙaunata, ka yi wa mutanena kacici-kacici, amma ba ka gaya mini amsar ba.” Ya amsa ya ce, “Ban ma bayyana wa mahaifina ko mahaifiyata ba, to, don me zan bayyana miki?” Ta yi ta kuka har kwana bakwai na bikin. Saboda haka a rana ta bakwai sai ya gaya mata, don ta dame shi. Ita kuwa ta bayyana kacici-kacicin wa mutanenta.
  • “Me ya fi zuma zaki? Me ya fi zaki ƙarfi?”Mah 14:18
    Ayoyin
    Mah 14:18Kafin rana ta fāɗi a rana ta bakwai mutane garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaki? Me ya fi zaki ƙarfi?” Samson ya ce musu, “Da ba don kun haɗa baki da matata ba, da ba za ku san amsar kacici-kacici ba.”

Waɗansu kacici-kacici

  • Sarauniyar Sheba ta gwada Solomon da tambayoyi masu wuya1Sar 10:1–3, 2Tar 9:1–2
    Ayoyin
    1Sar 10:1–3Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso Urushalima da tawaga mai yawa, tare da raƙuma masu ɗauke da kayan yaji, da zinariya masu yawa, da duwatsu masu daraja. Ta zo wurin Solomon ta kuwa yi magana da shi game da dukan abin da take da shi a ranta. Solomon ya amsa dukan tambayoyinta, ba abin da ya yi wa sarki wuyan bayyanawa mata.
    2Tar 9:1–2Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta. Solomon ya amsa dukan tambayoyinta; babu wani abin da ya yi masa wuya yă bayyana mata.
  • Allah yana magana da Musa a fili, ba da kacici-kacici baƘid 12:8
    Ayoyin
    Ƙid 12:8Da shi nake magana fuska da fuska, a fili kuma, ba a kacici-kacici ba; yakan ga siffar Ubangiji. To, me ya sa ba ku ji tsoro ku yi magana a kan bawana Musa ba?”
  • Wani mai zabura ya bayyana kacici-kacicinsa da garayaZab 49:4
    Ayoyin
    Zab 49:4Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
  • Karin Magana suna domin fahimtar kacici-kacicin masu hikimaK Mag 1:6
    Ayoyin
    K Mag 1:6don su fahimci karin magana da kuma misalai, kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
  • Daniyel yana iya bayyana kacici-kacici ya kuma warware matsaloli masu wuyaDan 5:12
    Ayoyin
    Dan 5:12Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.”
  • An gaya wa Ezekiyel ya yi kacici-kacici game da babban gaggafaEzk 17:2–3
    Ayoyin
    Ezk 17:2–3“Ɗan mutum, ka shirya kacici-kacici ka faɗa wa gidan Isra’ila misali. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa babbar gaggafa mai manyan fikafikai, dogayen gasusuwa da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ta zo Lebanon. Ta cire kan al’ul,
  • Maganganun Agur: abubuwa uku, abubuwa huɗuK Mag 30:15–16, K Mag 30:18–19, K Mag 30:24–28
    Ayoyin
    K Mag 30:15–16“Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’ Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’
    K Mag 30:18–19“Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu, yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.
    K Mag 30:24–28“Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana, duk da haka suna da hikima ƙwarai. Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani; remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu; fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma; ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.