Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Hasumiyoyi

Abubuwan ban mamaki

Hasumiyoyi a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (30), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • A Babel: birni mai hasumiyar da ta kai sammaiFar 11:4
    Ayoyin
    Far 11:4Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”
  • Ubangiji ya sauko don ya ga birnin da hasumiyarFar 11:5
    Ayoyin
    Far 11:5Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.
  • Sun daina gina birnin, aka kuma kira shi BabelFar 11:8–9
    Ayoyin
    Far 11:8–9Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin. Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.
  • Yaƙub ya kafa tentinsa a bayan Hasumiyar EderFar 35:21
    Ayoyin
    Far 35:21Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder.

Hasumiyoyi a yaƙi

  • Gideyon ya yi wa hasumiyar Fenuwel barazana, sa’an nan ya rushe taMah 8:9, Mah 8:17
    Ayoyin
    Mah 8:9Saboda haka sai ya ce wa mutanen Fenuwel, “Sa’ad da na dawo da nasara zan rushe wannan hasumiya.”
    Mah 8:17Ya rushe hasumiyar Fenuwel ya kuma karkashe mutanen garin.
  • Kusan mutum dubu suka mutu sa’ad da Abimelek ya ƙone hasumiyar ShekemMah 9:46, Mah 9:49
    Ayoyin
    Mah 9:46Da jin haka, sai ’yan ƙasa a hasumiyar Shekem suka shiga wurin mafaka a hankalin El-Berit.
    Mah 9:49Saboda haka mutanen suka sassare rassan itatuwa suka bi Abimelek. Suka tattara su a jikin mafakar suka kuma cinna mata wuta a kan mutanen da suke a ciki. Ta haka dukan mutanen da suke cikin hasumiyar Shekem, wajen maza da mata dubu ɗaya suka mutu.
  • A Tebez mutane sun kulle kansu a cikin hasumiya mai ƙarfiMah 9:50–52
    Ayoyin
    Mah 9:50–52Biye da wannan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta ya kuma cinye ta da yaƙi. A cikin birnin, akwai wata hasumiya mai ƙarfi, inda dukan maza da mata, dukan mutanen birnin, suka ɓuya. Suka kulle kansu, suka kuma hau rufin hasumiyar. Abimelek ya je wajen hasumiya ya kuma auka mata. Amma da ya yi kusa da ƙofar hasumiyar don yă cinna mata wuta,
  • Daga rufinta wata mace ta jefa dutsen niƙa a kan AbimelekMah 9:53
    Ayoyin
    Mah 9:53sai wata mata ta saki ɗan dutsen niƙa a kan Abimelek ta fasa ƙoƙon kansa.
  • Mai tsaro a kan hasumiya a Yezireyel ya ga sojojin Yehu suna zuwa2Sar 9:17
    Ayoyin
    2Sar 9:17Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezireyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yoram ya umarta, “Nemi mahayin doki a aike shi yă tarye su, yă kuma tambaye su, ‘Lafiya?’ ”
  • “Daga hasumiya zuwa birni mai katanga”2Sar 17:9, 2Sar 18:8
    Ayoyin
    2Sar 17:9Isra’ilawa a ɓoye sun aikata abubuwan da ba daidai ba ga Ubangiji Allahnsu. Tun daga hasumiyoyi har zuwa birane masu katanga, sun gina wa kansu wuraren sujada na tudu a dukan garuruwansu.
    2Sar 18:8Daga hasumiya zuwa birni mai katanga, ya ci Filistiyawa da yaƙi, har zuwa Gaza da kewaye.

Sarakunan da suka gina hasumiyoyi

  • Asa: birane da katanga da hasumiyoyi, ƙofofi da sakatai2Tar 14:7
    Ayoyin
    2Tar 14:7Ya ce wa Yahuda, “Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe.” Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara.
  • Uzziya ya gina hasumiyoyi a ƙofofin Urushalima da kuma a hamada2Tar 26:9–10
    Ayoyin
    2Tar 26:9–10Uzziya ya gina hasumiyoyi a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, a Ƙofar Kwari da kuma a kusurwar katanga, ya kuma yi musu katanga. Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma.
  • Na’urorin Uzziya sun harba kibiyoyi suka jefa duwatsu daga hasumiyoyi2Tar 26:15
    Ayoyin
    2Tar 26:15A Urushalima ya yi na’urori da gwanaye suka sarrafa don amfani a hasumiyoyi da kuma a kusurwar kāriya don harbin kibiyoyi da jefan manyan duwatsu. Sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako sosai har ya zama mai iko.
  • Yotam ya gina katanga da gine-gine masu tsawo a cikin kurmi2Tar 27:4
    Ayoyin
    2Tar 27:4Ya gina garuruwa a tuddan Yahuda, ya giggina katanga da gine-gine masu tsawo a wuraren da suke a kurmi.
  • Hezekiya ya sāke gina katangar da ta rushe ya kuma gina hasumiyoyi a kanta2Tar 32:5
    Ayoyin
    2Tar 32:5Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.

Hasumiyoyin Urushalima

  • Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar HananelNeh 3:1, Neh 12:39
    Ayoyin
    Neh 3:1Eliyashib babban firist da ’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel.
    Neh 12:39bisa Ƙofar Efraim, Ƙofar Yeshana, Ƙofar Kifi, Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiya ɗari, har zuwa Ƙofar Tumaki. A Ƙofar Matsara suka tsaya.
  • Hasumiyar Wurin GashiNeh 3:11, Neh 12:38
    Ayoyin
    Neh 3:11Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-Mowab ya yi gyare-gyaren wani sashe da kuma Hasumiyar Wurin Gashi.
    Neh 12:38Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi,
  • Doguwar hasumiyar da ta fito, kusa da katangar OfelNeh 3:25–27
    Ayoyin
    Neh 3:25–27sai Falal ɗan Uzai ya yi aiki ɗaura da kusurwa da kuma doguwar hasumiya daga fadar da take bisa kusa da shirayin masu tsaro. Biye da shi, Fedahiya ɗan Farosh da masu hidimar haikali da suke zama a tudun Ofel ne suka yi gyare-gyaren har zuwa wani wuri ɗaura da Ƙofar Ruwa wajen gabas da kuma doguwar hasumiya. Biye da su, mutanen Tekowa suka yi gyaran wani sashe, daga babbar doguwar hasumiya zuwa katangar Ofel.
  • Mutum goma sha takwas sun mutu sa’ad da hasumiyar Silowam ta fāɗiLuk 13:4
    Ayoyin
    Luk 13:4Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya a Silowam ya fāɗi a kansu, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne?

Gonakin inabi da maganganu

  • Mai gonar inabi yakan gina hasumiyar tsaro ya kuma haƙa wurin matse inabiIsh 5:2, Mat 21:33
    Ayoyin
    Ish 5:2Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya.
    Mat 21:33“Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.
  • Yesu: ka lissafta kuɗin kafin ka gina hasumiyaLuk 14:28–30
    Ayoyin
    Luk 14:28–30“In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin. Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa ba’a, yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’
  • Mai tsaro: kowace rana nakan tsaya a hasumiyar tsaroIsh 21:8
    Ayoyin
    Ish 21:8Mai tsaron kuma ya yi ihu, “Kowace rana, ranka yă daɗe, nakan tsaya a hasumiyar tsaro; kowane dare nakan tsaya a wurin aikina.
  • Waƙar Waƙoƙi: wuyanki ya yi kamar hasumiyar DawudaWW 4:4, WW 7:4
    Ayoyin
    WW 4:4Wuyanki ya yi kamar hasumiyar Dawuda, da aka gina da daraja; a kansa an rataye garkuwoyi dubu, dukansu garkuwoyin jarumawa ne.
    WW 7:4Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.