Abubuwan ban mamaki
Beyar a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (7), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Dawuda ya kashe zaki da beyar da suka ɗauki ’yan raguna1Sam 17:34–37
Ayoyin
1Sam 17:34–37Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita. Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe. Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai. Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.”
- Beyar mata biyu sun yayyage yara arba’in da biyu da suka yi wa Elisha ba’a2Sar 2:23–24
Ayoyin
2Sar 2:23–24Daga nan sai Elisha ya tafi Betel. Yayinda yake tafiya a hanya, sai waɗansu matasa suka fito daga cikin gari, suka yi masa dariya suna cewa, “Ka haura, ya kai mai kai marar gashi! Ka haura, kai mai kai marar gashi!” Sai ya juya ya dube su, ya la’anta su da sunan Ubangiji. Sai beyar guda biyu suka fito daga jeji suka hallaka matasa arba’in da biyu daga cikinsu.
- Dawuda da mutanensa suna da zafi kamar beyar da aka ƙwace ’ya’yanta2Sam 17:8
Ayoyin
2Sam 17:8Ka san mahaifinka da mutanensa mayaƙa ne, suna cikin fushi kamar mugun beyar da aka ƙwace mata ’ya’ya. Ban da haka ma, mahaifinka gogagge ne a yaƙi; ba zai kwana da rundunar ba.
- Gara ka sadu da beyar da aka ƙwace ’ya’yanta da wawa cikin wautarsaK Mag 17:12
Ayoyin
K Mag 17:12Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.
- Mugun mai mulki kamar beyar mai kai hari neK Mag 28:15
Ayoyin
K Mag 28:15Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake.
- Gudu daga zaki, sai a sadu da beyarAmos 5:19
Ayoyin
Amos 5:19Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki sai suka fāɗa a hannun beyar, ko kuma kamar wanda ya shiga gida ya dāfa hannu a bango sai maciji ya sare shi.
- Dukanmu muna gurnani kamar beyarIsh 59:11
Ayoyin
Ish 59:11Muna gurnani kamar beyar; muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci amma ina; mun nemi fansa, amma yana can da nisa.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.