Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Tsawon rai

Abubuwan ban mamaki

Tsawon rai a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (37), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Kafin rigyawa Ubangiji ya sa iyaka ga kwanakin mutumFar 6:3
    Ayoyin
    Far 6:3Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.”
  • Zabura: kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin in muna da ƙarfiZab 90:10
    Ayoyin
    Zab 90:10Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare.

Kafin rigyawa

  • Adamu ya rayu shekara 930Far 5:5
    Ayoyin
    Far 5:5Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.
  • Set ya rayu shekara 912Far 5:8
    Ayoyin
    Far 5:8Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
  • Enosh ya rayu shekara 905Far 5:11
    Ayoyin
    Far 5:11Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
  • Kenan ya rayu shekara 910Far 5:14
    Ayoyin
    Far 5:14Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.
  • Mahalalel ya rayu shekara 895Far 5:17
    Ayoyin
    Far 5:17Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.
  • Yared ya rayu shekara 962Far 5:20
    Ayoyin
    Far 5:20Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu.
  • Enok: shekara 365, sa’an nan ba a ƙara ganinsa baFar 5:23–24
    Ayoyin
    Far 5:23–24Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365. Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
  • Metusela ya rayu shekara 969Far 5:27
    Ayoyin
    Far 5:27Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
  • Lamek ya rayu shekara 777Far 5:31
    Ayoyin
    Far 5:31Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu.
  • Nuhu ya rayu shekara 350 bayan rigyawa, 950 duka-dukaFar 9:28–29
    Ayoyin
    Far 9:28–29Bayan ambaliyar, Nuhu ya yi shekaru 350. Gaba ɗaya dai, Nuhu ya yi shekara 950, sa’an nan ya mutu.

Bayan rigyawa

  • Shem: ya haifi ɗa yana da shekara 100, sa’an nan ya ƙara shekara 500Far 11:10–11
    Ayoyin
    Far 11:10–11Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad. Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
  • Arfakshad: ya haifi ɗa yana da shekara 35, sa’an nan ya ƙara shekara 403Far 11:12–13
    Ayoyin
    Far 11:12–13Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela. Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
  • Shela: ya haifi ɗa yana da shekara 30, sa’an nan ya ƙara shekara 403Far 11:14–15
    Ayoyin
    Far 11:14–15Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber. Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
  • Eber: ya haifi ɗa yana da shekara 34, sa’an nan ya ƙara shekara 430Far 11:16–17
    Ayoyin
    Far 11:16–17Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg. Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
  • Feleg: ya haifi ɗa yana da shekara 30, sa’an nan ya ƙara shekara 209Far 11:18–19
    Ayoyin
    Far 11:18–19Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu. Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
  • Nahor: ya haifi ɗa yana da shekara 29, sa’an nan ya ƙara shekara 119Far 11:24–25
    Ayoyin
    Far 11:24–25Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera. Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
  • Tera ya rayu shekara 205 ya kuma mutu a HaranFar 11:32
    Ayoyin
    Far 11:32Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.

Rayuwar da ta biyo baya

  • Saratu ta rayu har shekara 127Far 23:1
    Ayoyin
    Far 23:1Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya.
  • Ibrahim ya rayu shekara 175Far 25:7
    Ayoyin
    Far 25:7Duka-duka, Ibrahim ya yi shekara ɗari da saba’in da biyar.
  • Ishmayel shi ma ya yi tsawon raiFar 25:17
    Ayoyin
    Far 25:17Duka-duka Ishmayel ya yi shekara ɗari da talatin da bakwai; sai ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa.
  • Ishaku ya rayu shekara 180Far 35:28
    Ayoyin
    Far 35:28Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin,
  • Yaƙub ya rayu shekara 147, goma sha bakwai na ƙarshe a MasarFar 47:28
    Ayoyin
    Far 47:28Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai.
  • Yusuf ya mutu yana da shekara 110 aka shafe jikinsa da maganin adana gawa a MasarFar 50:26
    Ayoyin
    Far 50:26Yusuf kuwa ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Bayan an shafe shi da maganin hana ruɓa, sai aka sa shi a akwatin gawa a Masar.
  • Lawi ya rayu shekara 137, Kohat 133, Amram 137Fit 6:16, Fit 6:18, Fit 6:20
    Ayoyin
    Fit 6:16Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta, Gershon, Kohat da Merari. Lawi ya yi shekara 137.
    Fit 6:18’Ya’yan Kohat maza, su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Kohat ya yi shekara 133.
    Fit 6:20Amram ya auri ’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa. Amram ya yi shekara 137.
  • Haruna ya mutu a Dutsen Hor yana da shekara 123Ƙid 33:39
    Ayoyin
    Ƙid 33:39Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor.
  • Musa ya mutu yana da shekara 120, idanunsa ba su dushe baM Sh 34:7
    Ayoyin
    M Sh 34:7Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba.
  • Kaleb yana da shekara 85: har yanzu yana da ƙarfi kamar ranar da Musa ya aike shiYosh 14:10–11
    Ayoyin
    Yosh 14:10–11“Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar! Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā.
  • Yoshuwa ya mutu yana da shekara 110Yosh 24:29
    Ayoyin
    Yosh 24:29Bayan waɗannan abubuwa, Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekaru ɗari da goma.
  • Eli yana da shekara 98 ba ya iya gani1Sam 4:15
    Ayoyin
    1Sam 4:15wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani.
  • Barzillai, mai shekara tamanin, ya tanada wa Sarki Dawuda abinci2Sam 19:32
    Ayoyin
    2Sam 19:32To, Barzillai fa tsoho ne, mai shekara tamanin. Ya tanada wa sarki a lokaci da yake Mahanayim, gama shi attajiri ne.
  • Firist Yehohiyada ya mutu yana da shekara 1302Tar 24:15
    Ayoyin
    2Tar 24:15Yanzu Yehohiyada ya tsufa kuma cike da shekaru, ya kuwa mutu yana da shekara ɗari da talatin.
  • Ayuba ya ƙara rayuwa shekara 140 ya ga tsara huɗuAyu 42:16–17
    Ayoyin
    Ayu 42:16–17Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu. Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.
  • Anna, gwauruwa har shekara tamanin da huɗu, ba ta taɓa barin haikali baLuk 2:36–37
    Ayoyin
    Luk 2:36–37Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure, ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.