Bincika › Jigogi › Mabuɗai, hatimai, zobban hatimi
Abubuwan ban mamaki
Mabuɗai, hatimai, zobban hatimi a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (27), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
Mabuɗai da sakatai
- Ehud ya kulle ƙofofin ɗakin sama na Sarki Eglon a bayansaMah 3:23
Ayoyin
Mah 3:23Sa’an nan Ehud ya fita daga shirayin; ya rufe ƙofar ɗakin saman, ya kuma kulle su.
- Bayin sun jira, sa’an nan suka ɗauki mabuɗi suka buɗe ƙofofinMah 3:24–25
Ayoyin
Mah 3:24–25Bayan da ya tafi, bayin sarki suka zo suka tarar duk ƙofofin ɗakin sama suna kulle, suka ce, “Wataƙila yana bayan gari ne a ɗakin ciki.” Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ƙofar ba, sai suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe. Sai ga shugabansu a ƙasa matacce.
- Lawiyawa sukan tsare gidan Allah da dare su buɗe shi kowace safiya1Tar 9:27
Ayoyin
1Tar 9:27Sukan kwana a kewayen gidan Allah, domin dole su tsare shi; kuma su suke lura da mabuɗi don buɗewa a kowace safiya.
- An sāke gina ƙofofin Urushalima da ƙyamare, sakatai da ƙyaurayeNeh 3:3
Ayoyin
Neh 3:3’Ya’yan Hassenaya ne suka gina Ƙofar Kifi. Suka kafa ginshiƙan, suka kuma sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu.
Hatimai da zobban hatimi
- Yahuda ya bar hatiminsa, igiyarsa da sandansa wurin Tamar jinginaFar 38:18
Ayoyin
Far 38:18Ya ce, “Wace jingina zan ba ki?” Sai ta amsa, “Hatiminka da ka rataye a wuya da kuma sandan da yake a hannunka.” Ya ba da su gare ta, ya kuma kwana da ita, sai ta yi ciki.
- Tamar: “ko za ka gane da hatimin nan, da abin ɗamaran nan, da kuma sandan nan, ko na wane ne?”Far 38:25
Ayoyin
Far 38:25Yayinda ake fitar da ita, sai ta aika saƙo zuwa wurin surukinta, ta ce, “Mutumin da yake da waɗannan kayan ne ya yi mini ciki.” Ta kuma ƙara da cewa, “Duba ko za ka gane da hatimin nan, da abin ɗamaran nan, da kuma sandan nan, ko na wane ne?”
- Fir’auna ya sa zoben hatiminsa a yatsan YusufFar 41:42
Ayoyin
Far 41:42Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa.
- Yezebel ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab ta hatimce su da hatiminsa1Sar 21:8
Ayoyin
1Sar 21:8Sai ta rubuta wasiƙu a sunan Ahab, ta buga hatiminsa a kansu, sa’an nan ta aika su ga dattawa da manyan gari waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake.
- Zerzes ya ba Haman zoben hatiminsaEsta 3:10
Ayoyin
Esta 3:10Saboda haka sarki ya zare zoben hatimi daga yatsarsa, ya ba wa Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban Yahudawa.
- An rubuta umarnin Haman da sunan sarki aka hatimce shi da zobenEsta 3:12
Ayoyin
Esta 3:12Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.
- Zoben, da aka karɓe daga Haman, aka ba MordekaiEsta 8:2
Ayoyin
Esta 8:2Sarki ya cire zobensa na hatimi, wanda ya karɓo daga Haman ya ba Mordekai. Esta kuma ta naɗa shi a kan mallakar Haman.
- Dokar da aka hatimce da zoben hatimi na sarki ba a iya soke taEsta 8:8
Ayoyin
Esta 8:8Yanzu ku rubuta wata doka, a sunan sarki, a madadin Yahudawa, yadda kuka ga ya fi kyau ku kuma hatimce ta da zoben hatimin sarki, gama babu takardar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce da zobensa da za a iya sokewa.”
- Mordekai ya hatimce wasiƙun ya aika da su ta hannun ’yan aike a kan dawakaiEsta 8:10
Ayoyin
Esta 8:10Mordekai ya yi rubutu da sunan Sarki Zerzes, ya hatimce saƙonin da zoben hatimin sarki, ya kuma aika da su ta hannun masu ’yan aika a kan dawakai, waɗanda sukan hau dawakai masu gudu sosai, da aka yi kiwonsu musamman saboda sarki.
- An hatimce kogon zakoki da zoben sarki da zobban manyan mutanensaDan 6:17
Ayoyin
Dan 6:17Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel.
- Rubutacciyar yarjejeniya da aka hatimce da sunayen shugabanni, Lawiyawa da firistociNeh 9:38, Neh 10:1
- Irmiya ya sa hannu ya hatimce takarda: ɗaya a hatimce, ɗaya a buɗeIrm 32:10–11
Ayoyin
Irm 32:10–11Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna shekel a ma’auni. Na ɗauki takardar ciniki, takardar da aka rubuta sharuɗan a ciki, da kuma takardar da ba a liƙe ba,
- An sa takardun a tulun yumɓu don su daɗeIrm 32:14
Ayoyin
Irm 32:14‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka ɗauki waɗannan takardun ciniki, wanda aka liƙe da wanda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tulun yumɓu don kada su lalace.
- An tsare kabarin Yesu ta wurin hatimce dutsen da sa masu tsaroMat 27:66
Ayoyin
Mat 27:66Sai suka je suka tsare kabarin ta wurin buga masa hatimi, suka kuma sa masu gadi.
Zānen kamar na hatimi
- Duwatsun onis biyu da aka zāna kamar hatimi da sunayen ’ya’yan Isra’ila mazaFit 28:9, Fit 28:11, Fit 39:6
Ayoyin
Fit 28:9“Ka ɗauki duwatsu biyu masu daraja, ka rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kai
Fit 28:11A rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsu biyun, yadda mai yin aiki da dutse mai daraja yakan zāna hatimi. Sa’an nan a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya
Fit 39:6Suka shimfiɗa duwatsun onis, suka jera su cikin tsaiko na zinariya, suka kuma zāna sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.
- Duwatsu goma sha biyu na ƙyallen ƙirji, kowanne da aka zāna kamar hatimi da sunan kabilaFit 28:21, Fit 39:14
- Allon zinariya da aka zāna kamar hatimi: Mai tsarki ga UbangijiFit 28:36, Fit 39:30
- Magana a Waƙar Waƙoƙi: “Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka”WW 8:6
Ayoyin
WW 8:6Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka, kamar hatimi a hannunka; gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, kishinta yana kamar muguntar kabari, yana ƙuna kamar wuta mai ci, kamar gagarumar wuta.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.