Bincika › Jigogi › Dusar ƙanƙara
Abubuwan ban mamaki
Dusar ƙanƙara a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (17), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- A ranar da ake ƙanƙara Benahiya ya kashe zaki a cikin rami2Sam 23:20
Ayoyin
2Sam 23:20Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.
- Ƙanƙarar Lebanon takan bar gangarunsa ne?Irm 18:14
Ayoyin
Irm 18:14Dusar ƙanƙarar Lebanon ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon? Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa sun taɓa daina gudu?
- Rafuffukan da ƙanƙara mai narkewa ta duhunta suAyu 6:16
Ayoyin
Ayu 6:16kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara, yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,
- Allah yakan ce wa dusar ƙanƙara, “Fāɗo a kan duniya”Ayu 37:6
Ayoyin
Ayu 37:6Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
- Ka taɓa shiga ma’ajin ƙanƙara?Ayu 38:22
Ayoyin
Ayu 38:22“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara
- Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar uluZab 147:16
Ayoyin
Zab 147:16Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka.
- Ruwan sama da ƙanƙara sukan jiƙa ƙasa su sa ta tohoIsh 55:10
Ayoyin
Ish 55:10Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke saukowa daga sama, ba sa komowa ba tare da sun jiƙe duniya sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho, don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,
- Kamar ƙanƙara ta sauka a kan ZalmonZab 68:14
Ayoyin
Zab 68:14Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa, sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon.
Maganganu a Karin Magana
- Ɗan saƙo mai aminci kamar sanyin ƙanƙara ne a lokacin girbiK Mag 25:13
Ayoyin
K Mag 25:13Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika; ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi.
- Kamar ƙanƙara a lokacin rani, girma bai dace da wawa baK Mag 26:1
Ayoyin
K Mag 26:1Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba.
- Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro; iyalinta suna da tufafi masu kauriK Mag 31:21
Ayoyin
K Mag 31:21Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri.
Fari kamar ƙanƙara
- Hannun Musa, Miriyam da Gehazi: da kuturta, fari kamar ƙanƙaraFit 4:6, Ƙid 12:10, 2Sar 5:27
Ayoyin
Fit 4:6Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Sa hannunka cikin rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, sa’ad da ya fitar da shi, sai hannun ya a kuturce fari fat, kamar ƙanƙara.
Ƙid 12:10Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;
2Sar 5:27Kuturtar Na’aman zai manne maka da zuriyarka har abada.” Sai Gehazi ya fita daga gaban Elisha a kuturce, fari fat kamar dusar ƙanƙara.
- Ayuba: ko da na wanke jikina da sabuluAyu 9:30
Ayoyin
Ayu 9:30Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,
- Addu’ar Dawuda: ka wanke ni, zan kuwa fi ƙanƙara fariZab 51:7
Ayoyin
Zab 51:7Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab; ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.
- Mala’ikan a kabarin: tufafinsa farare kamar ƙanƙaraMat 28:3
Ayoyin
Mat 28:3Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.