Bincika › Jigogi › Sababbin sunaye
Abubuwan ban mamaki
Sababbin sunaye a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (16), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Suna mai kyau ya fi dukiya mai yawa darajaK Mag 22:1
Ayoyin
K Mag 22:1An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.
Misalai
- Abram ya zama IbrahimFar 17:5
Ayoyin
Far 17:5Ba za a ƙara kiranka Abram ba; sunanka zai zama Ibrahim, gama na mai da kai uban al’ummai masu yawa.
- Saira ta zama SaratuFar 17:15
Ayoyin
Far 17:15Allah ya kuma ce wa Ibrahim, “Game da Saira matarka kuwa, ba za ka ƙara kiranta Saira ba, sunanta zai zama Saratu.
- Yaƙub ya zama Isra’ilaFar 32:28
Ayoyin
Far 32:28Sai mutumin ya ce, “Sunanka ba zai ƙara zama Yaƙub ba, amma Isra’ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”
- Rahila ta ba ɗanta suna Ben-Oni; mahaifinsa ya kira shi BenyaminFar 35:18
Ayoyin
Far 35:18Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin.
- Fir’auna ya ba Yusuf suna Zafenat-FaneyaFar 41:45
Ayoyin
Far 41:45Fir’auna ya ba wa Yusuf suna Zafenat-Faneya, ya kuma ba shi Asenat ’yar Fotifera firist na On, ta zama matarsa. Yusuf kuwa ya zaga dukan ƙasar Masar.
- Musa ya ba Hosheya ɗan Nun suna YoshuwaƘid 13:16
Ayoyin
Ƙid 13:16Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)
- Na’omi: kada ku kira ni Na’omi, ku kira ni MaraRut 1:20
Ayoyin
Rut 1:20Ta ce musu, “Kada ku kira ni Na’omi. Ku kira ni Mara gama Maɗaukaki ya sa raina ya yi ɗaci sosai.
- An kuma ba Solomon suna Yedidiya2Sam 12:24–25
Ayoyin
2Sam 12:24–25Sai Dawuda ya yi wa matarsa Batsheba ta’aziyya, ya kuma tafi wurinta ya kwana da ita. Ta kuma haifi ɗa, suka ba shi suna Solomon. Ubangiji ya ƙaunace shi; kuma saboda Ubangiji ya ƙaunace shi, sai ya aika da saƙo ta wurin annabi Natan yă ba shi suna Yedidiya.
- Fir’auna Neko ya sāke wa Eliyakim suna Yehohiyakim2Sar 23:34
Ayoyin
2Sar 23:34Fir’auna Neko ya naɗa Eliyakim ɗan Yosiya sarki a maimakon mahaifinsa, ya kuma canja masa suna zuwa Yehohiyakim. Ya ɗauki Yehoyahaz ya kai Masar, a can ya mutu.
- Sarkin Babilon ya sāke wa Mattaniya suna Zedekiya2Sar 24:17
Ayoyin
2Sar 24:17Sarkin Babilon ya sa Mattaniya, ɗan’uwan mahaifin Yehohiyacin, ya zama sarki a madadinsa, ya canja masa suna zuwa Zedekiya.
- Daniyel, Hananiya, Mishayel, Azariya: Belteshazar, Shadrak, Meshak, AbednegoDan 1:7
Ayoyin
Dan 1:7Sai sarkin fada ya raɗa musu sababbin sunaye, ga Daniyel ya raɗa masa Belteshazar; ga Hananiya ya raɗa masa Shadrak; ga Mishayel ya raɗa masa Meshak; ga Azariya kuma ya raɗa masa Abednego.
- An kira Siman Kefas, wato, BitrusYoh 1:42
Ayoyin
Yoh 1:42Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan).
- An ba Yaƙub da Yohanna suna Buwarnajis, ’Ya’yan TsawaMar 3:17
Ayoyin
Mar 3:17Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);
- Yusuf daga Saifurus an kira shi Barnabas, Ɗan ƘarfafawaAyy M 4:36
Ayoyin
Ayy M 4:36Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa)
- Shawulu, wanda ake kira Bulus kumaAyy M 13:9
Ayoyin
Ayy M 13:9Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce,
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.