Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Raƙuma

Abubuwan ban mamaki

Raƙuma a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (26), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Ba za a ci raƙumi baFir 11:4
    Ayoyin
    Fir 11:4“ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku.
  • Abram, Yaƙub da Ayuba sun ƙidaya raƙuma cikin dukiyarsuFar 12:16, Far 30:43, Ayu 1:3
    Ayoyin
    Far 12:16Ya mutunta Abram sosai saboda ita, Abram kuwa ya mallaki tumaki da shanu, da jakuna maza da mata, da bayi maza da mata, da kuma raƙuma.
    Far 30:43Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna.
    Ayu 1:3yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa.
  • Ayuba yana da raƙuma 3,000, daga baya 6,000Ayu 1:3, Ayu 42:12
    Ayoyin
    Ayu 1:3yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa.
    Ayu 42:12Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu.
  • Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuman Dawuda1Tar 27:30
    Ayoyin
    1Tar 27:30Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma. Yedehiya mutumin Meronot shi ne mai lura da jakuna.

A cikin labarai

  • Bawan Ibrahim ya ɗauki raƙuma goma don ya nemo wa Ishaku mataFar 24:10
    Ayoyin
    Far 24:10Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor.
  • Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya da yammaFar 24:11
    Ayoyin
    Far 24:11Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.
  • Rebeka ta ɗebo ruwa domin dukan raƙumansaFar 24:14, Far 24:19–20
    Ayoyin
    Far 24:14Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”
    Far 24:19–20Bayan ta ba shi ya sha, sai ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka ruwa su ma, har sai sun gama sha.” Sai ta yi sauri ta juye ruwan da yake tulunta cikin kwami, ta koma zuwa rijiyar da gudu don ta ƙara ɗebo ruwa, ta kuma ɗebo isashe saboda dukan raƙumansa.
  • Rebeka ta hau raƙumi ta je ta sadu da IshakuFar 24:61, Far 24:64
    Ayoyin
    Far 24:61Sa’an nan Rebeka da bayinta mata suka shirya suka hau raƙumansu suka koma tare da mutumin. Da haka bawan ya ɗauki Rebeka ya tafi.
    Far 24:64Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri,
  • Rahila ta ɓoye gumakan Laban cikin sirdin raƙuminta ta zauna a kansuFar 31:34
    Ayoyin
    Far 31:34Rahila fa ta kwashe gumakan gidan ta sa su cikin sirdin raƙumi, ta kuma zauna a kansu. Laban ya bincika cikin kowane abu a tentin amma bai sami kome ba.
  • Kyautar Yaƙub ga Isuwa ta haɗa da raƙuma masu shayarwa 30 da ’ya’yansuFar 32:15
    Ayoyin
    Far 32:15raƙuma mata talatin tare da ƙananansu, shanu arba’in da bijimai goma, jakuna mata ashirin da kuma jakuna maza goma.
  • Raƙuman mutanen Ishmayel suna ɗauke da kayan yaji zuwa MasarFar 37:25
    Ayoyin
    Far 37:25Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.
  • Raƙuman Midiyawa ba su ƙidayuwa kamar yashiMah 7:12
    Ayoyin
    Mah 7:12Midiyawa, Amalekawa da dukan sauran mutane gabashi suka yi sansani a kwari, kamar fāra. Raƙumansu kuma kamar yashi a bakin teku don sun wuce ƙirge.
  • Gideyon ya ɗauki kayan ado masu siffar jinjirin wata daga raƙuman sarakunanMah 8:21
    Ayoyin
    Mah 8:21Zeba da Zalmunna suka ce masa, “Zo, ka yi da kanka. ‘Yadda mutum yake haka ƙarfinsa.’ ” Ta haka Gideyon ya matso gaba ya kashe su, ya ɗauki kayan ado daga wuyar raƙumansu.
  • Amalekawa ɗari huɗu sun tsere wa Dawuda a kan raƙuma1Sam 30:17
    Ayoyin
    1Sam 30:17Dawuda ya yaƙe su tun daga fāɗuwar rana har yammar kashegari. Ba ko ɗaya da ya tsira sai samari ɗari huɗu waɗanda suka tsere a kan raƙuma.
  • Sarauniyar Sheba ta zo da raƙuma ɗauke da kayan yaji da zinariya1Sar 10:2
    Ayoyin
    1Sar 10:2Ta iso Urushalima da tawaga mai yawa, tare da raƙuma masu ɗauke da kayan yaji, da zinariya masu yawa, da duwatsu masu daraja. Ta zo wurin Solomon ta kuwa yi magana da shi game da dukan abin da take da shi a ranta.
  • Hazayel ya kawo wa Elisha kyautai labtun raƙuma arba’in2Sar 8:9
    Ayoyin
    2Sar 8:9Sai Hazayel ya tafi taryen Elisha, ya ɗauka kyauta na kowane irin kaya masu kyau na Damaskus tare da shi a raƙuma arba’in. Ya shiga ya tsaya a gaban Elisha ya ce, “Ɗanka Ben-Hadad na Aram ya aike ni in tambaye ka, ‘Zan warke daga ciwon nan?’ ”
  • Mahara Kaldiyawa sun kwashe raƙuman AyubaAyu 1:17
    Ayoyin
    Ayu 1:17Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa sun auka wa raƙumanka sun kwashe su duka, suka kuma karkashe masu yi maka aiki, ni kaɗai ne na tsira na zo in gaya maka!”
  • Yohanna yakan sa rigar gashin raƙumiMat 3:4, Mar 1:6
    Ayoyin
    Mat 3:4Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji.
    Mar 1:6Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, ya kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fāri ne da kuma zumar jeji.

Maganganun Yesu

  • Ya fi sauƙi raƙumi ya wuce ta kafar alluraMat 19:24
    Ayoyin
    Mat 19:24Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”
  • Kukan tace ƙwaro amma kuna haɗiye raƙumiMat 23:24
    Ayoyin
    Mat 23:24Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.