Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Gishiri

Abubuwan ban mamaki

Gishiri a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (21), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Matar Lot ta waiwaya ta zama ginshiƙin gishiriFar 19:26
    Ayoyin
    Far 19:26Amma matar Lot ta waiwaya baya, ta kuma zama ginshiƙin gishiri.
  • Ana cin abinci marar ɗanɗano ba tare da gishiri ba?Ayu 6:6
    Ayoyin
    Ayu 6:6Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba, ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?
  • Elisha ya zuba gishiri cikin maɓuɓɓugar Yeriko2Sar 2:20–21
    Ayoyin
    2Sar 2:20–21Sai ya ce, “Ku kawo mini sabuwar ƙwarya, ku kuma sa gishiri a ciki.” Sai suka kawo masa. Sai ya tafi maɓulɓular ruwan yana watsa gishirin a ciki, yana cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da ruwan nan. Ba zai ƙara jawo mutuwa, ko yă hana ƙasar ba da amfani ba.’ ”
  • Abimelek ya rushe Shekem ya kuma barbaɗe ta da gishiriMah 9:45
    Ayoyin
    Mah 9:45Dukan yinin, Abimelek ya matsa yaƙi da birnin sai da ya cinye ta ya kuma kashe mutanenta. Sa’an nan ya hallaka birnin ya barbaza gishiri a kanta.
  • Akan goge jarirai da gishiriEzk 16:4
    Ayoyin
    Ezk 16:4A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki.
  • Sarkin Farisa ya ba da gishiri ba iyaka domin haikaliEzr 6:9, Ezr 7:22
    Ayoyin
    Ezr 6:9A tanada musu duk abin da suke bukata. A ba su ’yan bijimai, da raguna, da ’yan tumaki domin miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na sama, haka kuma dole a tanada wa firistoci alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da mai, kullum ba fasawa yadda firistoci suke yi a Urushalima
    Ezr 7:22har zuwa talenti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari na ruwan inabi, da garwa ɗari na man zaitun, da kuma gishiri ba iyaka.

A cikin sujada

  • Akan sa gishiri a kowace hadaya ta gariFir 2:13
    Ayoyin
    Fir 2:13A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.
  • Firistoci sukan barbaɗa gishiri a kan hadayun ƙonawaEzk 43:24
    Ayoyin
    Ezk 43:24Za ka miƙa su a gaban Ubangiji, firistoci kuma za su barbaɗe gishiri a kansu su kuma miƙa su kamar hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
  • Alkawarin gishiriƘid 18:19, 2Tar 13:5
    Ayoyin
    Ƙid 18:19Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.”
    2Tar 13:5Ba ku san cewa Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda da zuriyarsa har abada ta wurin alkawarin gishiri ba?

Wurare

  • Tekun Gishiri, iyakar gabas ta Isra’ilaFar 14:3, Ƙid 34:12, Yosh 15:2
    Ayoyin
    Far 14:3Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri).
    Ƙid 34:12Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ”
    Yosh 15:2Iyakarsu a kudanci ta tashi tun daga kurewar kudu na Tekun Gishiri,
  • Birnin Gishiri a jejin YahudaYosh 15:62
    Ayoyin
    Yosh 15:62Nibshan, Birnin gishiri da En Gedi, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.
  • Yaƙe-yaƙe da Edom a Kwarin Gishiri2Sam 8:13, 2Sar 14:7
    Ayoyin
    2Sam 8:13Dawuda kuwa ya ƙara zama shahararre bayan ya dawo daga kai wa ƙasar Aram hari, daga nan sai ya je ya karkashe mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.
    2Sar 14:7Shi ne kuma wanda ya ci mutanen Edom dubu goma a yaƙi, a Kwarin Gishiri, ya kuma ci Sela da yaƙi, ya ba ta suna Yokteyel, sunan da ake kiranta har wa yau.

Maganganu

  • Gishirin da ya rasa ɗanɗanonsa ba shi da amfaniMat 5:13, Luk 14:34
    Ayoyin
    Mat 5:13“Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
    Luk 14:34“Gishiri fa yana da kyau, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa?
  • Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma zauna lafiyaMar 9:50
    Ayoyin
    Mar 9:50“Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”
  • Bari maganarku ta zama da ladabi da daɗin jiKol 4:6
    Ayoyin
    Kol 4:6Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.