Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Ruwan sama da fari

Abubuwan ban mamaki

Ruwan sama da fari a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (21), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • Kafin wani tsiro ya toho, babu ruwan sama a duniyaFar 2:5
    Ayoyin
    Far 2:5babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar,
  • Ruwan sama na kaka da na bazaraM Sh 11:14
    Ayoyin
    M Sh 11:14sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.
  • Taron Ezra sun zauna suna rawar jiki cikin ruwan sama na wata na taraEzr 10:9, Ezr 10:13
    Ayoyin
    Ezr 10:9A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi.
    Ezr 10:13Amma akwai mutane da yawa, kuma lokacin damina ne; saboda haka ba za mu iya tsayawa a waje ba. Ban da haka ma, aikin nan ba na kwana ɗaya ko biyu ba ne, domin ba ƙaramin laifi muka yi ba.
  • Iskar arewa takan kawo ruwan samaK Mag 25:23
    Ayoyin
    K Mag 25:23Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.
  • In gizagizai sun cika, sukan zubar da ruwan samaM Had 11:3
    Ayoyin
    M Had 11:3In gizagizai sun cika da ruwa, sukan zub da ruwan sama bisa duniya. Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa, inda ya fāɗi a nan zai kwanta.
  • Yakan sa ruwan sama ya sauko a kan masu gaskiya da marasa gaskiyaMat 5:45
    Ayoyin
    Mat 5:45don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.
  • Ruwan sama ya sauko, rigyawa kuma ta bugi gidanMat 7:25
    Ayoyin
    Mat 7:25Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.

Rigyawa

  • Ƙofofin ruwa na sammai sun buɗe; ruwan sama ya sauka kwana arba’in dare da ranaFar 7:11–12
    Ayoyin
    Far 7:11–12A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in.
  • Sa’an nan ƙofofin ruwa suka rufe, aka kuma tsai da ruwan samaFar 8:2
    Ayoyin
    Far 8:2Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari.
  • Bakan gizo: ba za a ƙara yin rigyawa da za ta hallaka duniya baFar 9:11–15
    Ayoyin
    Far 9:11–15Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba.” Allah ya kuma ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na yi tsakanina da ku, da kowace halitta tare da ku; alkawari na dukan zamanai masu zuwa. Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya. Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan, zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba.

Hadari

  • Ƙanƙara da tsawa sun bugi Masar, amma ba Goshen baFit 9:23–26
    Ayoyin
    Fit 9:23–26Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar; ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma. Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace. Wuri guda kaɗai da ba a yi ruwan ƙanƙara ba, shi ne yankin Goshen, inda Isra’ilawa suke.
  • Sama’ila ya roƙi tsawa da ruwan sama lokacin girbin alkama1Sam 12:17–18
    Ayoyin
    1Sam 12:17–18Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki. Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.

Fari

  • Iliya: ba raɓa ko ruwan sama sai da maganata1Sar 17:1
    Ayoyin
    1Sar 17:1To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”
  • A shekara ta uku ta farin, aka yi alkawarin ruwan sama1Sar 18:1
    Ayoyin
    1Sar 18:1Bayan dogon lokaci, a cikin shekara ta uku, maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Tafi, ka gabatar da kanka ga Ahab, zan kuwa aika da ruwan sama a ƙasar.”
  • Girgije ƙarami kamar hannu, sa’an nan ruwan sama mai yawa1Sar 18:44–45
    Ayoyin
    1Sar 18:44–45Sau na bakwai, bawan ya ce, “Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku.” Sai Iliya ya ce, “Je ka faɗa wa Ahab, ‘Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama yă tare ka.’ ” Ana cikin haka, sarari ya ƙara duhunta da girgije, iska ta taso, sai ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauko, Ahab kuwa ya hau zuwa Yezireyel.
  • An rufe sama shekara uku da rabiLuk 4:25, Yaƙ 5:17–18
    Ayoyin
    Luk 4:25Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar.
    Yaƙ 5:17–18Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi. Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.
  • Ruwan sama a kan wani gari, ba a kan wani baAmos 4:7
    Ayoyin
    Amos 4:7“Na kuma hana muku ruwan sama tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi. Na sa aka yi ruwan sama a wani gari, sai na hana a yi a wani gari. Wata gona ta sami ruwan sama; wata gona kuma ta bushe.
  • Ƙasa ta tsattsage; manoma sun rufe kawunansuIrm 14:4
    Ayoyin
    Irm 14:4Ƙasa ta tsattsage saboda babu ruwan sama a ƙasar; manoma sun sha kunya suka kuma rufe kawunansu.
  • Solomon ya yi addu’a domin ruwan sama sa’ad da aka rufe sammai1Sar 8:35–36
    Ayoyin
    1Sar 8:35–36“Sa’ad da sammai sun kulle, babu kuma ruwan sama domin mutane sun yi maka zunubi, sa’ad da suka yi addu’a suna fuskantar wannan wuri, suka kuma furta sunanka, suka juye daga zunubinsu domin ka hore su, ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.