Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Ranakun haihuwa

Abubuwan ban mamaki

Ranakun haihuwa a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (8), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

  • A ranar haihuwar Fir’auna ya yi wa hafsoshinsa bikiFar 40:20
    Ayoyin
    Far 40:20To, a rana ta uku ne, ranar tunawa da haihuwar Fir’auna, ya kuwa yi biki wa dukan hafsoshinsa. Ya fid da shugaban masu shayarwa da kuma shugaban masu tuya a gaban hafsoshinsa.
  • A ranar ya mayar da mai shayarwa ya kuma rataye mai toya burodiFar 40:21–22
    Ayoyin
    Far 40:21–22Ya mai da shugaban masu shayarwa a matsayinsa, saboda haka shugaban masu shayarwa ya sāke sa kwaf a hannun Fir’auna, amma ya rataye shugaban masu tuya, kamar dai yadda Yusuf ya faɗa musu a fassarar mafarkan da suka yi.
  • A ranar haihuwar Hiridus ya yi wa shugabannin Galili liyafaMar 6:21
    Ayoyin
    Mar 6:21A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili.
  • ’Yar Hiridiyas ta yi rawa ta roƙi kan YohannaMat 14:6–8
    Ayoyin
    Mat 14:6–8A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai, har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa. Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.”
  • Ayuba ya la’anci ranar haihuwarsaAyu 3:1–3
    Ayoyin
    Ayu 3:1–3Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi. Ayuba ya ce, “A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’
  • Irmiya: la’ananniya ce ranar da aka haife niIrm 20:14, Irm 20:18
    Ayoyin
    Irm 20:14La’ananniya ce ranar da aka haife ni! Kada ranar da mahaifiyata ta haife ni ta zama mai albarka!
    Irm 20:18Me ya sa na ma fito daga cikin ciki in ga wahala da baƙin ciki in kuma ƙare kwanakina da kunya?
  • Suna mai kyau ya fi turare, ranar mutuwa kuma ta fi ranar haihuwaM Had 7:1
    Ayoyin
    M Had 7:1Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.