Bincika › Jigogi › Wanke ƙafafu da hannuwa
Abubuwan ban mamaki
Wanke ƙafafu da hannuwa a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (27), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
- Ibrahim ya ba baƙinsa ruwa su wanke ƙafafunsu su hutaFar 18:4
Ayoyin
Far 18:4Bari a kawo ruwa ku wanke ƙafafunku, ku huta a ƙarƙashin wannan itace.
- Lot: “Ku wanke ƙafafunku, ku kwana”Far 19:2
Ayoyin
Far 19:2Ya ce, “Ranku yă daɗe, ina roƙonku ku ratsa zuwa gidan bawanku. Ku wanke ƙafafunku, ku kwana, sa’an nan ku kama hanyarku da sassafe.” Suka ce, “A’a, za mu kwana a dandali.”
- Gidan Laban ya ba bawan Ibrahim da mutanensa ruwa domin ƙafafunsuFar 24:32
Ayoyin
Far 24:32Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu.
- Wakilin Yusuf ya ba ’yan’uwan ruwa su wanke ƙafafunsuFar 43:24
Ayoyin
Far 43:24Mai yin hidimar ya ɗauki mutane zuwa gidan Yusuf ya ba su ruwa su wanke ƙafafunsu, ya kuma tanada wa jakunansu abinci.
- A gidan tsohon a Gibeya sun wanke ƙafafunsu, suka ci suka shaMah 19:21
Ayoyin
Mah 19:21Saboda haka sai kai shi zuwa gidansa ya ciyar da jakunansa. Bayan sun wanke ƙafafunsu, sai aka ba su abinci da abin sha.
- Abigiyel: a shirye nake in wanke ƙafafun bayin maigidana1Sam 25:41
Ayoyin
1Sam 25:41Sai ta rusuna da fuskarta har ƙasa ta ce, “Ni baranyarka ce, na shirya in bauta maka in kuma wanke ƙafafun bayin shugabana.”
- Dawuda ga Uriya: “Gangara gidanka ka wanke ƙafafunka”2Sam 11:8
Ayoyin
2Sam 11:8Sa’an nan Dawuda ya ce wa Uriya, “Gangara gidanka ka wanke ƙafafunka.” Saboda haka Uriya ya bar fadar, sarki kuma ya aika masa da kyauta.
- Mefiboshet bai kula da ƙafafunsa ba lokacin da Dawuda ba ya nan2Sam 19:24
Ayoyin
2Sam 19:24Mefiboshet, jikan Shawulu, shi ma ya gangara don yă taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har ran da ya komo lafiya, Mefiboshet bai lura da ƙafafunsa, ko yă aske gemunsa, ko yă wanke tufafinsa ba.
- Waƙar Waƙoƙi: “Na wanke ƙafafuna, sai in sāke ɓata su?”WW 5:3
Ayoyin
WW 5:3Na tuɓe rigata, sai in sāke sa ta kuma? Na wanke ƙafafuna, sai in sāke ɓata su?
A cikin Linjila
- Yesu ga Siman: ba ka ba ni ruwa domin ƙafafuna baLuk 7:44
Ayoyin
Luk 7:44Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta.
- Wata mace ta jiƙa ƙafafunsa da hawayenta ta goge su da gashintaLuk 7:38
Ayoyin
Luk 7:38ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare.
- Maryamu ta shafa wa ƙafafun Yesu turaren nard ta goge su da gashintaYoh 12:3
Ayoyin
Yoh 12:3Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.
- A wurin cin abinci Yesu ya ɗaura tawul a ƙugunsa ya wanke ƙafafun almajiraiYoh 13:4–5
Ayoyin
Yoh 13:4–5saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa. Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura.
- Bitrus: “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba”Yoh 13:8
Ayoyin
Yoh 13:8Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.”
- Yesu: wanda ya yi wanka yana bukatar wanke ƙafafunsa kawaiYoh 13:10
Ayoyin
Yoh 13:10Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yă wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.”
- “ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna”Yoh 13:14
Ayoyin
Yoh 13:14Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna.
- Gwauruwar da aka san ta da wanke ƙafafun tsarkaka1Tim 5:10
Ayoyin
1Tim 5:10aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.
Wanke hannuwa
- Firistoci sukan wanke hannuwa da ƙafafu a daron tagulla kafin su yi hidimaFit 30:18–21, Fit 40:31
Ayoyin
Fit 30:18–21“Ka yi daro na tagulla, ka yi masa ƙafafun da za a ajiye shi da tagulla don wanki. Ka ajiye shi tsakanin Tentin Sujada da bagade, ka zuba ruwa a ciki. Haruna da ’ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu da ruwan da yake cikinsa. Duk lokacin da suka shiga Tentin Sujada, za su yi wanka, don kada su mutu. Duk lokacin da suka yi kusa da bagade don hidima ta miƙa hadayar da aka yi wa Ubangiji da wuta, za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu, don kada su mutu. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla domin Haruna da zuriyarsa daga tsara zuwa tsara.”
Fit 40:31a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu.
- Saboda kisan da ba a san mai kisan ba, dattawa sukan wanke hannuwansu a kan karsanaM Sh 21:1, M Sh 21:6
- Bilatus ya wanke hannuwansa a gaban taron: “ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan”Mat 27:24
Ayoyin
Mat 27:24Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”
- Farisiyawa ba sa ci ba tare da sun wanke hannuwansu ba, bisa ga al’adar dattawaMar 7:3–4
Ayoyin
Mar 7:3–4(Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce. Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.)
- Sun tambaya me ya sa almajiran Yesu suke ci ba tare da sun wanke hannuwansu baMat 15:2, Mar 7:5
- Wani Bafarisiye ya yi mamaki cewa Yesu bai wanke hannu kafin cin abinci baLuk 11:38
Ayoyin
Luk 11:38Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi.
- Randunan dutse shida a Kana suna ɗauke da ruwa domin al’adun tsarkakewaYoh 2:6
Ayoyin
Yoh 2:6Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.