Bincika › Jigogi › Ƙidayar jama’a
Abubuwan ban mamaki
Ƙidayar jama’a a cikin Littafi Mai Tsarki
Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (21), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.
A cikin jeji
- An ƙidaya kowane namiji mai shekara ashirin ko fiye da zai iya yin yaƙiƘid 1:2–3
Ayoyin
Ƙid 1:2–3“Ka yi ƙidayan dukan al’umman Isra’ilawa bisa ga iyalansu da kabilarsu, ka rubuta kowa da sunansa bi da bi. Da kai da Haruna za ku lissafta dukan mazan Isra’ila bisa ga sashensu, waɗanda suka kai shekaru ashirin ko fiye, da za su iya shiga soja.
- Kowane mutumin da aka ƙidaya ya biya rabin shekel, mawadaci da matalauci daidaiFit 30:13–15, Fit 38:26
Ayoyin
Fit 30:13–15Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji. Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji. Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku.
Fit 38:26Duk mutumin da ya shiga ƙirge daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, ya ba da rabin shekel. Mazan da suka shiga ƙirge sun kai mutum 603,550.
- Ƙidaya ta farko: 603,550Ƙid 1:46
Ayoyin
Ƙid 1:46Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550.
- Ba a ƙidaya Lawiyawa tare da sauran kabilu baƘid 1:47–49
Ayoyin
Ƙid 1:47–49Ba a dai ƙidaya zuriyar Lawi tare da saura kabilan ba. Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Ka tabbatar ba ka ƙidaya mutanen Lawi ko kuma ka haɗe su tare a ƙidayan sauran Isra’ilawa ba.
- Mazan Lawiyawa daga mai wata ɗaya zuwa sama: 22,000Ƙid 3:39
Ayoyin
Ƙid 3:39Jimillar Lawiyawan da Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga umarnin Ubangiji bisa ga danginsu, haɗe da kowane jariri daga wata ɗaya ko fiye, 22,000 ne.
- Ƙidaya ta biyu, kusa da Urdun: 601,730Ƙid 26:2, Ƙid 26:51
- Ba wani daga cikin waɗanda aka fara ƙidaya da ya rage sai Kaleb da YoshuwaƘid 26:64–65
Ayoyin
Ƙid 26:64–65Ba ko ɗayansu da yake cikin waɗanda Musa da Haruna firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a Hamadar Sinai. Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.
Ƙidayar Dawuda
- Ƙidayar ta ɗauki wata tara da kwana ashirin2Sam 24:8
Ayoyin
2Sam 24:8Bayan suka ratsa dukan ƙasashen, a ƙarshe suka koma Urushalima, bayan wata tara da kwana ashirin.
- Sama’ila: 800,000 a Isra’ila da 500,000 a Yahuda2Sam 24:9
Ayoyin
2Sam 24:9Yowab ya ba wa sarki jimillar yawan mayaƙan. A Isra’ila akwai mutum dubu ɗari takwas da za su iya riƙe takobi. A Yahuda kuwa mutum dubu ɗari biyar.
- Tarihi: 1,100,000 a Isra’ila da 470,000 a Yahuda1Tar 21:5
Ayoyin
1Tar 21:5Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda.
- Yowab bai ƙidaya Lawi da Benyamin ba1Tar 21:6
Ayoyin
1Tar 21:6Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba.
- Bayan ƙidayar, lamirin Dawuda ya dame shi2Sam 24:10
Ayoyin
2Sam 24:10Bayan Dawuda ya ƙidaya mayaƙan, lamirinsa ya kāshe shi, sai ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka ka gafarta wa bawanka. Na yi wauta ƙwarai.”
- Ba a rubuta yawan a littafin tarihin Sarki Dawuda ba1Tar 27:24
Ayoyin
1Tar 27:24Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba.
Waɗansu ƙidayoyi
- Lawiyawa masu shekara talatin ko fiye: 38,0001Tar 23:3
Ayoyin
1Tar 23:3Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas.
- Solomon ya ƙidaya baƙi 153,600 a ƙasar2Tar 2:17
Ayoyin
2Tar 2:17Solomon ya ƙidaya dukan baƙin da suke cikin Isra’ila, bayan ƙidayan da mahaifinsa Dawuda ya yi; aka kuma tarar sun kai 153,600.
- Waɗanda suka dawo daga bauta sun kai 42,360Ezr 2:64
Ayoyin
Ezr 2:64Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,
- Augustus ya umarta a yi ƙidaya; Kwiriniyus ne gwamnan SuriyaLuk 2:1–2
Ayoyin
Luk 2:1–2A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.)
- Yusuf da Maryamu sun tafi Betlehem don a rubuta sunansuLuk 2:3–5
Ayoyin
Luk 2:3–5Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi. Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.
- Yahuda na Galili ya tashi a kwanakin ƙidayarAyy M 5:37
Ayoyin
Ayy M 5:37Bayansa, Yahuda mutumin Galili ya ɓullo a kwanakin ƙidaya, ya jagoranci mutane cikin tawaye. Shi ma aka kashe shi, dukan mabiyansa kuma aka watsar da su.
Tushe
Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.