Bible Explorer

Bincika › Jigogi › Lamba arba’in

Abubuwan ban mamaki

Lamba arba’in a cikin Littafi Mai Tsarki

Nassosin Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa (31), layi bayan layi, daga Nave’s Topical Bible.

Kwana arba’in

  • Ruwan sama ya sauka a duniya kwana arba’in dare da ranaFar 7:4, Far 7:12, Far 7:17
    Ayoyin
    Far 7:4Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.”
    Far 7:12Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in.
    Far 7:17Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya.
  • Bayan kwana arba’in Nuhu ya buɗe tagar jirginFar 8:6
    Ayoyin
    Far 8:6Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,
  • Shafe jikin Yaƙub da maganin adana gawa ya ɗauki kwana arba’inFar 50:3
    Ayoyin
    Far 50:3Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi makoki dominsa kwana saba’in.
  • Musa ya zauna a kan dutse kwana arba’in dare da ranaFit 24:18, Fit 34:28, M Sh 9:9
    Ayoyin
    Fit 24:18Sa’an nan Musa ya shiga girgijen ya hau kan dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba’in da dare arba’in.
    Fit 34:28Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.
    M Sh 9:9Sa’ad da na hau kan dutse don in karɓi allunan dutse, allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutse yini arba’in da dare arba’in; ban ci abinci ba, ban sha ruwa ba.
  • ’Yan leƙen asiri sun dawo bayan kwana arba’inƘid 13:25
    Ayoyin
    Ƙid 13:25A ƙarshen kwana arba’in sai suka komo daga bincikensu.
  • Goliyat ya fito kwana arba’in, safe da yamma1Sam 17:16
    Ayoyin
    1Sam 17:16Kwana arba’in cif, Bafilistin nan ya yi ta fitowa kowane safe da kuma kowace yamma.
  • Iliya ya yi tafiya kwana arba’in dare da rana zuwa Horeb1Sar 19:8
    Ayoyin
    1Sar 19:8Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah.
  • Yunana: saura kwana arba’in a kuma birkice NinebeYun 3:4
    Ayoyin
    Yun 3:4A rana ta fari, Yunana ya kama tafiya yana ratsa birnin. Sai ya yi shela cewa, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Ninebe?”
  • Yesu ya yi azumi kwana arba’in dare da ranaMat 4:2
    Ayoyin
    Mat 4:2Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa.
  • Bayan tashinsa, Yesu ya bayyana har kwana arba’inAyy M 1:3
    Ayoyin
    Ayy M 1:3Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.

Shekara arba’in

  • Isra’ila sun ci manna shekara arba’in a jejiFit 16:35
    Ayoyin
    Fit 16:35Isra’ilawa suka yi shekaru arba’in suna cin Manna, har sai da suka shiga cikin ƙasar da take da mutane, suka ci Manna har zuwa kan iyakar ƙasar Kan’ana.
  • Shekara arba’in na yawo, shekara ɗaya domin kowace rana ta leƙen asiriƘid 14:34
    Ayoyin
    Ƙid 14:34Shekaru arba’in, shekara ɗaya a madadi kwana ɗaya cikin kwanakin arba’in da kuka ɗauka kuka leƙi asirin ƙasa, za ku sha wahala saboda zunubanku, ku kuma san abin da ake nufi da sa ni in yi gāba da ku.’
  • Ishaku ya auri Rebeka yana da shekara arba’inFar 25:20
    Ayoyin
    Far 25:20Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rebeka ’yar Betuwel, mutumin Aram, daga Faddan Aram, ’yar’uwar Laban mutumin Aram.
  • Musa yana da shekara arba’in sa’ad da ya ziyarci mutanensa; shekara arba’in daga baya, ƙaramin itaceAyy M 7:23, Ayy M 7:30
    Ayoyin
    Ayy M 7:23“Da Musa ya cika shekara arba’in da haihuwa, sai ya yanke shawara yă ziyarci ’yan’uwansa Isra’ilawa.
    Ayy M 7:30“Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai.
  • A zamanin alƙalai da dama ƙasar ta huta shekara arba’inMah 3:11, Mah 5:31, Mah 8:28
    Ayoyin
    Mah 3:11Saboda haka ƙasar ta zauna da lafiya shekara arba’in har sai da Otniyel ɗan Kenaz ya rasu.
    Mah 5:31“Ta haka bari dukan abokan gābanka su hallaka, ya Ubangiji! Amma bari waɗanda suke ƙaunarka su zama kamar rana sa’ad da ta fito da ƙarfinta.” Sa’an nan ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba’in.
    Mah 8:28Da haka Isra’ilawa suka mallaki Midiyawa ba su kuma sāke tā da kai ba. A zamanin Gideyon ƙasar ta sami zaman lafiya har shekara arba’in.
  • Filistiyawa sun mallaki Isra’ila shekara arba’inMah 13:1
    Ayoyin
    Mah 13:1Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda haka ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba’in.
  • Eli ya shugabanci Isra’ila shekara arba’in1Sam 4:18
    Ayoyin
    1Sam 4:18Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.
  • Shekara arba’in a ƙarƙashin Shawulu, in ji BulusAyy M 13:21
    Ayoyin
    Ayy M 13:21Sa’an nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawulu ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arba’in.
  • Dawuda ya yi mulki shekara arba’in: bakwai a Hebron, talatin da uku a Urushalima2Sam 5:4, 1Sar 2:11
    Ayoyin
    2Sam 5:4Dawuda yana da shekara talatin ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara arba’in.
    1Sar 2:11Ya yi sarauta shekaru arba’in a bisa Isra’ila. Wato, shekaru bakwai a Hebron da kuma talatin da uku a Urushalima.
  • Solomon ya yi mulki shekara arba’in1Sar 11:42
    Ayoyin
    1Sar 11:42Solomon ya yi mulki a Urushalima, a bisa dukan Isra’ila, shekaru arba’in.
  • Yowash ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in2Sar 12:1
    Ayoyin
    2Sar 12:1A shekara ta bakwai ta Yehu, Yowash ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima na tsawon shekaru arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; daga Beyersheba.

Bulala arba’in

  • Doka ba ta yarda a yi bulala fiye da arba’in baM Sh 25:3
    Ayoyin
    M Sh 25:3amma kada yă yi masa bulala fiye da arba’in. In ya yi masa fiye da haka, za a ƙasƙantar da ɗan’uwanku, zai kuma zama rainanne a idonku.
  • Sau biyar Bulus ya sha bulala arba’in ɗaya babu2Kor 11:24
    Ayoyin
    2Kor 11:24Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.

Tushe

Daga Nave’s Topical Bible (Orville J. Nave, 1896; na kowa): an zaɓi jigogi, an taƙaita layuka an kuma sa su cikin kalmomin zamani, an bar layukan fassarar ma’ana; an duba kowace aya.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.